*3*

488 44 3
                                    

Kuka? To ta yi kuka akan me? Akan abubuwan da suka faru kamar a mafarki? Mafarkin ma mummuna, to inba mafarki ba na farko ta ya za a ce Yayarta wadda ta zame mata Uwa da Uba ta rasu? Rasuwarma ta ba zata, ba yanzu wai ta fita siyo kayan shayi ba?

"Ikon Allah" Ta fada tana kara rungume Najma, don jinta take kamar Yayarta da ta rasa.

Abu na biyu da ta kasa yarda da shi shi ne wai mijinta ya sake ta, sakin ma na wulakanci, ga kazafin zina, ga sheganta mata 'ya da ya yi, ko da yake ba auran Soyayya suka yi ba na hadi ne wanda har yau ta kasa gane me yasa Babanta ya mata haka.

Tunowa da ta yi da Babanta ya sa ta sakin wani murmushi mai ciwo, tun tasowarta bata san wani abu soyayyar mahaifi ba, soyayyar yayarta kadai ta sani, don tun tana shekara uku mahaifiyarsu ta rasu.

Sunan Babansu Alhaji Labaran Bala, cikakken manomi ne domin ko a kauyen da yake da zama gonarshi ta fi ta kowa girma. Bayan noman da yake, yakan yi kasuwancin amfanin gonar daga gari zuwa gari.

Matanshi biyu;ta farko ita ce Hansai, yaransu shida da ita maza biyar;Ayuba ,Yawale, Munzali, Murtala da Habu sai mace daya Zuwaira. Auran Soyayya suka yi da ita, lokacin yana da kimanin shekaru ashirin yayinda ita kuma take sha biyar.

Hansai macece mai kwadayi da san abin duniya, ga rashin tawakkali, dake a kauye aka taso, ba kowa ke da shaawar neman ilimi ba,sai dai a je talla ba dare ba rana da sunan neman na kayan daki. Hansai na daga cikinsu don ko sallahr kirki ba ta iya ba.

Ta biyun ita ce Kausar, za a iya ce mata balarabiya ko Shuwa don daga Sudan take, a gurin yawon kasuwancinsa ya hadu da ita a tasha, lokacin ko Hausa ba ta iya ba, shima don ya dan iya larabci ne kadan kadan ya samu ya san ko ita wace, tunda ya ganta rakube ita kadai ya ji yana so ya shiga rayuwarta,ba wani bata lokaci ta fada mai ya'ki a ka yi a garinsu garin gudun hijira ta tsinci kanta a Nigeria. Ba wani bata lokaci ya ce zai taimaketa, tunda ta fara magana ya ji ya ga mata yana so, ita ma da ya ke bata da kowa,ga kuruciya da rashin iyaye, ba musu ta amince zata aureshi, dukda karancin shekarunta,bata fi shekara sha bakwai ba, shi ko ya tasamma arba'in.

Ko da suka je garinsu, Labaran ya sami Hansai da maganar, ya ga tashin hankali da bala'i don ko tsalle ta yi ta dire ta ce ba da ita ba, kishi ba nata bane balle a ce da balarabiya, lokacin tana goyon Habu danta namiji na karshe. Da ya ke shima Labaran namijin duniya ne, sai ya lallabeta da dadin baki irin nasu na maza, ya ringa janyo ayoyi da hadisai yana kara gamsar da ita. Da kyar ta amince duk da koda bata amince ba din,ya dau aniyar auran Kausar.

Cikin ikon Allah ya auri Kausar inda Maigarinsu ne ya yi mata waliyyci yayinda Kawunsa ya wakilceshi.
Wannan ne mafarin rayuwar su Bilkisu da Sumayya, 'ya'yan Kausar da ta haifa bayan auransu da Labaran.

Bilkisu ce Babba kamarsu daya da Mamanta, fara ce sol don har ta so ta fi Kausar haske. Tun bayan sunanta Kausar ta fara ganin canje canje daga wurin Labaran, ya daina cin abincinta, magana ma baya mata sai dai in rashin mutunci zai sauke mata, wani lokacin ma ya hada da duka, tun Bilkisu ba ta fahimtar komai har ta fara, ga cin zalin Bilkisu da su Ayuba ke yi, ba dama ta fita tsakar gida za su kamata su jibgeta, in ta yi magana Hansai ko Labaran su far mata. Duk wannan aikin Hansai ne don dama ta amince da auranne don ta ga an fi karfinta, amma da taimakon kawarta Lami suka kai Lamarin gurin wani boka(wa'iyazubillah),shi ne ya kunna wutar gaba a tsakanin Labaran da Kausar.

Tun haihuwar ta ba ta kara ba, Hansai ta kuma haihuwar mace Zuwaira amma ita shiru, tun abin na damunta har ya daina, dama fatanta ta sami wadanda za su yi mata addua in ta bar duniya don tana ji a jikinta ta kusa mutuwa, takan yi aman jini, ko ta ringa jin zafi a kirjinta, ba sai an fada ba, ciwon zuciya ne ya kamata.

Cikin ikon Allah Bilkisu na da shekara bakwai, Kausar ta sami cikin Sumayya, ba ta gayawa kowa ba don dama bata da kowan, don ma dai an dan sami sauki daga gun Labaran shekaru biyu baya ya fara kulata amma a yan kwanakin nan an koma gidan jiya.

Lokacin da ta haifi Sumayya ne aka tabbatar da tana da hawan jini da ciwon zuciya, don ta sami arzikin zuwa asibiti dake Labaran ya sayi gida a birni sun tashi. Lokacin da ya gane tana da cikin ba karamar murna ya yi ba, har ya bata mamaki sosai, ta ji dadi saidai fa lokacin da ya yi arba da Sumayya ne aka koma gidan jiya,ba don komai ba sai don kalar fatarta,a cewarshi don me za ta dau kalar fatarsa? (Karfin hali) baka ce irin sosai don inba kamanninta mutum ya gani ba da Kausar,to zai iya rantsewa ba ita ta haifeta ba.

Bayan shekaru uku da haihuwar Sumayya Allah ya yi wa Kausar rasuwa, Bilkisu ce kadai abin ya shafa, lokacin tana 10 years, Labaran yakan yi kuka ya mata addua in asirin ya sakeshi yayinda wataran kuma sai ya ce gwara da ta rasu ya huta da wahala. Ta bangaren Hansai kuwa duniya tai dadi burinta ya cika, sai kuma ta fara cuzgunawa su Bilkisu, su za su yi shara, wanke wanke da duk wasu ayyuka na gidan, in sun gama kuma ta bi su da duka ba tsoron Allah.

Haka rayuwar ya da kanwar ta cigaba, ba wanda Sumayya ta sani sai Yaya (sunan da take kiran Bilkisu da shi),in yunwa ta ke ji Yaya, in barci za ta yi sai kusa da Yaya, in makaranta za ta je to da kuka za ta tafi in ta dawo kuwa sai ta bawa Yaya labarin duk abinda ya faru.

Dake Labaran mai kudi ne kowa shakkar gaya masa gaskiya yake, da kyar Kawunshi ya tsawatar mashi ya sa Sumayya a makaranta, Bilkisu dama tana zuwa don ba karya duk bakar zuciyarka sai ka so ta,ga kyau,na fuska da zuciya ga fara'a da kirki, tana da tausayi da taimako gurin taimakon ne Allah ya hadata da wani mutum Ahmad da ya yar da Wallet dinshi, ta dawo daga makaranta lokacin tana JSS3 ta tsinta, ba bata lokaci da taje gida ta ari wayar Ayuba ta kira numbershi, don ta tsinci complimentary card dinshi a wallet din.

Tun da ya karbi wallet din ya fada tarkon sonta, taimakon nata ya burgeshi, bai yi kasa a guiwa ba ya tunkari Labaran da maganar, abin nema ya samu don dama ya gaji da dawainiya da su, a cewarshi uwarsu ta mutu ta barshi da wahala.

Tana gama SS3 aka yi bikinsu, Hansai ta so ta hana ganin cewar ga 'yar ta Zuwaira shiru ba magana, amma da ya ke ba mai ja da ikon Allah, sai a ka yi lafiya aka gama lafiya.

Assalamu Alaikum, ya kuka ga rayuwar Marigayiya Yaya😥 da Sumayya? Zan cigaba insha Allah in na sami tym, vote and comment zasu kara min kaimi



Najma da MahirWhere stories live. Discover now