"Bani phone number din naki sai ki debo min ruwa." Ya yamutsa fuska lokacin da yaga ta zumburo mai baki alamun ba za ta ba. Baya san rashin kunyar yarinyar.
"Wai kai ba ka da kafane? Mom dina tace in daina zuwa aikenka. " Ya rike kanshi da ke sarawa yana jaddada doloncinta a ranshi.
"Zaki je ki debo min ruwan ko sai na fasa miki transfer din airtime din? Ban san yaushe kika raina ni haka ba Anisa."
Sai da ya yi threatening dinta da airtime din ta tafi, ita har ga Allah ta manta ta rokeshi ya sa mata kati, a shekarunta na 8 da rabi, babu YouTube channel din da bata sani ba, yanzu ma haka wani series take kallo sub dinta ya 'kare shi ne ta ce ya sa mata kati.
"Ungo" ta fada cikin tsiwa tana nuna hancinshi da kofin saura kadan ruwan ya zube a jinkinshi.
"Bai bi takanta ba saboda ciwon kan da yake ji ya fi karfinshi, ya karbi ruwan yana ballo maganin da ya karba a wurin maigadinsu da ya dawo daga gidansu Najma.
Rufe idonshi ya yi yana tunanin mai ya haddasa mai ciwon kan, maybe tunanin da yake ta yi ne ko kuma gajiya don a 'kafa ya tako ya dawo gida tun daga Kabuga inda gidansu Najma ya ke zuwa unguwarsu Dorayi 'karama kuma duk takun da ya yi daidai yake da tunano kalmar satar da aka jefeshi da ita.
"Mom ta ce in biyar ta yi ka daura mata ruwan Tuwo. " muryar Anisa ta katse mai tunanin da yake.
"Haka ta iya, kullum yawo ni zan daura ruwan abincin da karshe ba zan ci ba. " Ya
ayyana a ranshi yana mi'kewa, barci zai yi dukda ya san ba a son barcin yamma sai dai bayajin ciwon kan zai barshi. Allah ya so shi ya yi La'asar.Da sallama ya shiga 'dakin nasa yana mai cin karo da cup 'din da ya sha cornflakes da shi da safe, wannan ya bawa cikinshi damar murdawa alamun yunwa. kila wannan ma ya taimaka wurin karamai ciwon kan.
Ya furzar da iska kafin ya nufi dan 'karamin fridge din da ke dakinshi. Sai dai abinda ya gani a ciki ne ya yi sanafiyyar subucewar wani bahagon tsaki daga bakinshi.
"Ta shanye kenan" Ya fada a fili da tsananin bacin rai. Shi bai san mai ya tarewa rayukan gidanba da suke neman rayuwarshi haka, yo neman rayuwarshi mana tunda sun hana shi abinci, dan maltina din da yake siyowa ya ajiye a fridge din ma Anisa bata barshi ba, ya tabbata ita ta shanye mai. Gata dai zubin dolaye amma bakin halinta ya fi 'karfinta, gashi ita ta hada makircin da ya sa Dad dinshi ya hana shi kulle kofar dakinshi idan baya nan, wai shi baya san wani munafurci a gidanshi mai yake boyewa da za a ce kamarshi sai ya wani rufe kofa.
Bai san me ya faru ba, ya dai tsinci kanshi da nufar wani akwati, akwatin da Najma ta mai iyaka da shi sai dai yana ji a lokacin zai karya alkawarin da ya daukar mata in ya so sai ya fada mata.
Tunaninta da ya yi ya sa zuciyarshi ta hasko mai fuskarta da hawaye lokacin da ya baro gidansu, ya so ya je ya rarrasheta sai dai kuma yana jin in ya zauna a gidan yana kallon brothers dinta komai zai iya faruwa."I'm coming to you Naj Naj, na san yanzu kina islamiya but bayan Magrib zan zo." Ya fada kamar tana jin shi yana mai zuge zip din akwatin.
"Kin ga abinda yake faruwa da ni ko? Me ya sa kika tafi kika barni in this cruel world? Ina missing dinki sosai Yaya, kowa baya so na, kin ga wannan da wannan ne kadai suke so na." Ya fada cikin wani yanayi yana nuna Sumayya da Najma a jikin hoton.
Ranar sallah aka dauki hoton, ranar da yayar ta rasu, kuma ranar da aka haifi Najma. Yayar ce ta rike Najman sai Sumayya a gefenta da murmushi duka a fuskarsu, shi ya dau hoton da wayar Yaya, kuma da kyar aka rarrasheshi ya ajiye Najman dake hannunshi ya karbi wayar. Bayan rasuwarta ne ya kai aka wanke mai hotunan, kala hamsin aka wanke mai, sai dai tun bayan lokacin da Najma ta gane yana daukan hotunan yana basu labari sai ta kwashesu da nufin konawa ta barshi da guda uku kawai.

YOU ARE READING
Najma da Mahir
Romance"Ga wannan sunanshi 'Dan aike' domin ko in ya je dawowa ya ke, an hadashi ne da majinar damisa mai mura,jelar'beran da bai taba satar daddawa ba,da kuma hakorin muzuru mai kimanin kwana cassa'in, ya yarda ke tun bai san miye yarda ba,a coffee za ki...