*4*

381 38 0
                                    


Haka rayuwa ta cigaba, da dadi babu dadi haka Sumayya take zaune da Hansai ga kadaici da ya bi ya dameta, Yaya ta yi aure ta barta, dama ba wani shirin kirki suke da Zuwaira ba, ba abinda yake hadasu sai raini da tsangwama, saukin abinma Babanta yakan barta ta je gidan Bilkisu duk weekend, in ta je kuwa kamar karta dawo domin ko tsakaninta da Yayarta har ma mijinta babu komai sai alkhairi da kulawa, in ta je haka za yi ta nan nan da ita, Ya hanya? Ba dai wata damuwa ko? me za ki ci? Gaskiya sai kin mana sati...

Wannan abin ne ya kara karfafa dankon zumunci a tsakanin 'yan uwan guda biyu,cikin ikon Allah bayan shekara daya da auren Bilkisu ta haifo 'danta kyakkyawa mai kama da ita sai dai bakin babansa ya dauko, ranar suna ya ci suna Mahir.

Sumayya ta dauki son duniya ta daura mai, da ke Babansu ya barta ta zauna da Yaya saboda taya aiki,tare da Salma kanwar Ahmad suke, dama sa'anni ne, sai suka zama kamar kawaye. Tun Sumayya bata iya mai wanka ba har ta zo ta iya, ta goya shi, a takaice dai a daki daya suke kwana.

Mahir na da shekara tara a duniya aka yi wa Salma kanwar Ahmad aure, da ke mijinta, Barr Anwar ba a Kano yake ba, Abuja aka kaita, tare da Sumayya aka yi komai na bikin, da ke lokaci ya ja, Labaran ya kara tsufa, rashin mutuncin nashi ya dan ragu, za a ce yanzu yakan zauna su dan yi hira da 'yar tashi, Zuwaira kuwa sai abinda ya yi gaba, Hansai ta sa mata wani tunani na daban a zuciyarta, ita dai burinta ta auri mai kudi, kuma wanda zai mata duk abinda ta ce ba musu. Turkashi!!!.

Bayan wata.uku da kai amarya ne,gaba daya iyalan Arc Ahmad na zaune a falo, Mahir na manne da 'Kawarshi(Yadda yake kiran Sumayya),tana koya mai homework. Ita kadai ke iya sa shi a gaba ya yi homework, shi in ta tashi ne a barshi ya je gidansu Jameel da Jameela su yi wasa.

Wataran in Yaya ta nuna 'bacin ranta akai sai Babanshi ya ce a kyaleshi,kadaici ke damunshi. Tunda aka haifi Mahir shiru Bilkisu ba ta kara haihuwa ba, tun tana damuwa har ta daina, Ahmad yakan bata hakuri tare da nuna mata ba fa yawan 'ya'yan ake bukata ba, albarkarsu ake so.

" 'Kawata ki ce Yaya ta haifo min 'kanwa kin ga an sake haifowa Jameel kanwa ba ki ganta ba fara da ita kamar Yaya ya ce wai Jalila za a sa mata. " Mahir ya fada yana rufe littafinshi.

"Banda abinka Mahir haihuwa ai ta Allah ce, in ya nufa sai ka ga an haifo ma 'yan uku ma. " Sumayya ta bashi amsa tana saka littafin nashi a jaka.

Ya 'dan yatsina fuska sannan ya ce;
"Ni mata nake so duka a sa musu Najma, Nawwara da Nawal. "

Kafin ta bashi amsa aka kirata a waya.

"Amarya ba kya laifi" Ta fada da tsokana.

"Sumaii!!! kin kyauta wallahi, kika ce za ki kwana sai ji na yi ana kin bi flight din 6 ,haka amana ta ce. "

"Haba Amaryar Barrister kaina bisa wuyana, kar ki sa a daureni yau dinnan, ya gida? "

"Lafiya lau, Ina Mahir da Yaya Ahmad da Yaya?duk na yi missing dinku barinma Mahir, ki shafa min kanshi don Allah, ki rokar min Ya Ahmad ya bar shi ya zo ya min weekend. "

"To ai banda abinki ko an barshi in dai Mahir ne ba zuwa zai yi ba, balle na ji ya ce an yi haihuwa a gidansu abokinshi, ki ga ko ai ya samu abin yi. "

"Ahh lallai to na hakura, nima dai in na haifi tawa ya ringa zuwa. "

"Yayy Salma don't tell me kin kusa haifa mana baby, wow can't wait. "

"Kai Sumaii har kin ba kunya ki gaishe da mun da su. " Tana fadin haka ta kashe wayar.

Yaya Ahmad wai Salma na gaisheku.

"Auu shi ne bata kirani ba ko, to bana amsawa, wai fushi nan take da ni don na ko zuwa gidanta, haka ake yi? Kawai sai in dauki kafa har abuja na je gidan kanwata, Kai ba zai yiwu ba."

"Ni fa Sumayya na zaci surukina ne ya kiraki, ba san mai ya sa ba, na 'kagu in ga kin yi aure,in ga 'ya'yanki, kin san duniyar nan ba madawwama ba ce." Yaya ta fada cikin tsokana don ta san Sumayya da kunya.

"Haba Yaya don Allah... "

Wayarta ce ta sake kara ,tana kallon mai kiran gabanta ya fadi.

"Salamu Alaikum Baba" Ta amsa cikin tsoro.

"Sumayyatu, Yayarki na kusa? "Labaran ya tambaya cike da gadara.

"Eh Baba ga ta nan"

"To bata wayar mu yi magana"

Ta mika ma Yaya wayar tana tunanin wace magana za su yi.

"Ke Bilki me amfanin wayarki ne? Ana ta kira tun dazu ba ki dauka? " Labaran ya tambayeta a zafafe kamar zai aiko mata da duka ta wayar.

"A yi min afuwa Baba, tana chaji ne a daki. "

"To shi kenan, ki turo Sumayyatu da duk kayanta gobe, ki gayyaci mutanen da kike ganin za ki gayyata ,insha Allahu gobe za a daura aurenta da Alh Yunusa abokina. "

"Wace Sumayyan wai, wane Yunusa kuma? " Yaya ta tamabaya da dunbin mamaki.

"Shashashar wofi, kin raina mahaifiyarki Bilki ba dai ni ba,don butar gidanku Sumayya nawa kika sani? Ko Yunusa mijin Suwaiba baban su Sabi'u ne baki sani ba? "

"Allah ya huci zuciyarka Baba, amma na ga mutumin nan fa kusan sa'anka ne, 'yayanshi bakwai ina Sumayya za ta kai shi? "

"Gidan Babarki za ta kaishi, da wannan ba'kin nata ma ba taimakonta zai yi ba, Ja'irar banza ina magana kina ja da ni, to in tunanin hana auren nan kike to wallahi kin yi kadan, matsawar ina numfashi sai an yi. "

Daga nan ya katse wayar ya bar Yaya fuska shabe-shabe da hawaye, a ina aka taba haka,ko dai maganar da ta yi ta auran Sumayya ta fada da bakin mala'iku ne?

Kamar yadda Labaran ya fada kuwa haka aka daura auren Sumayya da Yunusa washegari, Ta yi kuka ta gode Allah, daga baya ta hakura don aikin gama ya gama, Yaya ce mai kara kwantar mata da hankali,ta bata shawarar zama da kishiyarta lafiya, ita ta siya mata kayan daki don in ta Labaran ne, katifa kawai ya siya sai wani tsohon pillow da ya sa Ayuba ya nemo masa ya bata. Yaya ta kuma yi mata alkawarin kawo mata kayan kitchen da sauran kayan bukata.

To ta yaya mutuwa za ta mata haka? Ina zata je bayan watanta huhu da aure Babansu ya rasu? Ta je gida aiki ko Hansai su kashe ta?

"Wai da gaske Yaya rasuwa kika yi? "

"Kowane mai rai mamacine, ki yi hakuri baiwar Allah, 'ya'yanki na bukatarki, addu'a za ki mata, insha Allah aljanna ce makomarta. "Wani likita ne ya yi maganar, haka kawai sai ta ji hankalinta ya 'dan kwanta da kalamanshi, ta ji za ta iya yayyafawa zuciyarta ruwan sanyi.

"Sunana Dr Aminu Shariff Daura,ni na dubaki bayan kin haihu, kuma na ji duk abinda ya faru da ke, karki dorawa kanki damuwar rashin mijinki, ko rejecting 'yarki da yayi, ni da abokina Ahmad mun isheta, 'da ai na kowa ne. "

Najma da MahirWhere stories live. Discover now