*13*

561 22 3
                                    

Tunda ta yi sallahr asuba ba ta koma ba, all thanks to Allah yanzu Ya Mir ya yi waya, sau uku tana kiranshi bayan ta idar da sallah dama Mami ta hakura ta sallama mata wayarta, tun da da ba kiran kowa take ba, bata barin wayar ta huta ta yi ta game kenan har sai charge ya 'kare, yanzu kuma da aka sami abokin hira shi kenan.

"Hello Yayana 'dan ba'ki ka san me? . "

"Hu'du"

"Au ba za ka ma amsa ba?me kuma hu'du? "

"This is the fourth time da kike kirana, yanzu kuma me za ki gaya min? Na san ba zai wuce yau za ki je ki ga Maama ba? "

"To ba ma haka bane, ce maka zan yi na siyo ma Amir bindigar wasa, kuma zan je in ga Baby Maimun, and my crazy friend Jalila, duk na rubuta abinda zan gaya mata, kuma na san za ta bani shawarar yadda zan yi dealing with Ya Sani ka san ita ce daidai shi. "

"To Aku kuturu, sai kuma me? Saboda I hate to admit it but 'Yar fara kin hana ni barci, ki barni in yi enjoying weekend dina mana. "

"Aww Allah ko, haka ma ka ce? Ba za ka zo mu hadu ba, please na san Maama ta yi missing dinka fah, pretty please. "

"Na ji, anjima zan zo. Jameel ne zai zo daukarki? "

"I guess so, ni wane ni in ce Ya Auwal ya kai ni, ka san shi da son girma, ni kuma in dai bai baka hakuri ba na daina gaisheshi, shi ne fa muke ta wasan buya bana bari mu hadu da shi. "

"Ya miki kyau, in ya kama ki ya tara miki jini babu ruwana. "

"sai anjima since you no more care. "

*****

"Jalila!!! " Najma ta yi tsalle ta dire lokacin da ta yi arba da Jalilan.

"'Kawas be classy mana big girl da ke kina tsalle?"

"See you, I'm still young dama ke ai kin fiya son girma, Ya Jameel good morning shi ne ba ka ce tare za ku zo ba? "

"Morning, ita ta nace sai ta biyoni, and na rasa me take so, na son in so take ta gan ki ai gidanmu za ki zo, na san akwai wata a kasa. "

Hada ido suka yi Jalila ta daga wa Najma gira, irin akwai labari dinnan.

"Bari in shiga mu gaisa da Mami, sarkin azarbabi har kin fito waje. "

Sai da Jalila ta bari ya shige tukunna ta jawo Najma.

"Ke, ina wannan 'dan rainin hankalin yayan naki? "

"Ke Jalila ki rufa min asiri, Ya Sanin ne 'dan rainin hankali? "

"To da me? Wani ba'ki da shi duk annakiya ta makale me a fata, da ga gani baya wanka ya fita, ni ina kika ce ya ajiye kejin kajinshi?"

"Suna bayan gida,ai kajin nan nashi yana ji da su"

"Ai na san yana ji da su shi ya sa na tambaye ki, zo mu je mu ga yadda suke 'kwai. "

"Kai ni dai ba ruwana, kema kin san yanzu Ya Jameel zai fito in ya ga bama nan da matsala. "

"ke dallacan Najman nan sai a hankali, in kika nuna kina tsoronshi shi ne zai nemi ya raina miki wayo, me zai mana? Ya wuce ya dakemu? Kuma muna zuwa gida in gayama Baba ya rama mana, zo mu je ni, shi ya sa ma fa na zo. "

Kafin 'kiftawar ido suka nufi bayan gidan su a dole za su ga yadda kaza ta ke 'kwai.

Da ke Najma ba laifi tana da tsoro, sai 'kawar tata sarkin karambani ta bu'de kejin, kan ta ce 'Ali' kaji hudu sun yi waje, da ta juya da niyyar kamo su sauran hudun suma suka ranta a na kare. Turkashi!!!.

"Sani ba ka gane min su Najma ba? Yanzu fa na shiga mu gaisa da Mami na fito kuma ban gansu ba. "

"Gaskiya ban gansu ba, fitowata kenan dama Abbu ya aiko ni...kai Hey Adewale ka bude gate wai za a fita da mota. " Sani ya yi maganar yana mika alamun dai daga barci ya tashi.

Najma da MahirWhere stories live. Discover now