*14*

506 31 14
                                    

"Lily ni kike ma rashin kunya kina wani hura hanci da zazzarewa ido don na ce ki raka ni?"

"Haba Umma ni wallahi ki barni ,Haba bini-bini ki ce wani in biki Denmark ,to ni wallahi Maama zan bi Da'kasoye,gwara in je 'kauye in ga me a gurin." Lily ta fa'da tana kuma murguda baki.

"Lallai ni yar nan  Sumayya bayan mijin da kika kwace min har 'ya'yan ma sai kin rabani da su? Tsakanina da ke wallahi Allah ya isa."

"Yauwa Umma ni ki daina ce min Lily din nan sai ka ce wata flower an fa ce min..."

Ai kan ta gama fitsarar tata bakin nata ya rufu da wata maka da Umman ta kai wa bakin tsiwar. Ta ko takarkare karfin da Allah ya bata ta kwantsama ihu sai a kunnen Babanta.

"Haba Haba ba wai mun gama magana akan yadda kike dukan Leela ba? yarinya kankanuwa kin bi kin sa ta a gaba ,ta ce ba za ta bi ki ba ko ana dole ne? Ki wuce in yi dropping dinki a airport ina da abin yi."

"Haka dai kuma ka cigaba ,kana sangarta yarinya da sunan so, ice tun yana 'danye ai ake tan'kwara shi,ke kuma wallahi kin yi da yar halak,za ki ga wanda zai 'kara zuwa da ke unguwa." Ta karasa zance tana sauke rankwashi a kan Leela  kafin ta dangwarar da travelling bag din da ta hada kayan Jalilan a ciki.

Wannan furucin sai ya sosa zuciyar Jalila don ita Allah ya yi ta da son fita unguwa barin ma dai da Umman tata ko ba komai za ta ci dadi a hanya amma dai bata jin za ta iya yafe zuwa Dakasoye,tana da plan a kai tun ba yau ba, tana so ta je ta ga Hansai da mutanenta,gashi da Najma za a yi tafiyar ba za ta bari ta bata labari ba. Tunanin yadda Umman tasu ke son su ya kwantar mata da hankali, ta san za ta sauko,tana blackmailing dinta da hawaye da kalamai shi kenan. in kana so ka taba  Shafaatu  to ka taba 'ya'yanta,don ita tana matukar kaunarsu kawai dai takan boye ne saboda bata so su lalace,wannan halin nata da ma wasu halayen na matuwar burge Dr Aminu shi ya sa kullum yake adduar matarshi mafi soyuwa a gareshi ta dawo, ya san har yanzu kishi ke dawainiya da ita shi ya sa take ta wasu abubuwan da da bai san ta da su ba,ko tafiye tafiyen da take tsira ma duk don ta san ba ya son ta yi nisa da shi ne,ba wai don karan kanta tana enjoying ba,yanzu ma wai 'kawarta da ke can Denmark din zata je dubowa wai ta yi zazzabi daga nan kuma ta biya ta kaiwa 'kanwarta da ke karatu a can ziyara bayan ko wata biyu bata rufa ba da zuwa can din.

"Ha'a har kun shirya kenan,yanzu nake kokarin kiran Drivern office dinmu ya zo ya taimaka ya kai ku wani uzuri ya taso min." Dr Aminu  Ya fada da murmushin da ya zunguri zuciyar Shafaatu tana jin dama ita kadai yake yiwa murmushin.

"To ba matsala ,Allah ya yi jagora,dama so nake mu je da wuri ko zamu sami damar juyowa yau bana son mu  kwana a gidan mu har rai hudu." Sumayya ta bashi amsa itama da murmushin tana gyara goyon Maimun da tunda taji muryar babanta ta fara zillo a bayanta. Shafa kumatun Maimun din Dr ya yi suka kamar hanya shi da Ogar tashi wadda kadan ya rage ta fashe tana ta wani kumbara sai ka ce kwabin fanke.

"Leela ba za ki ci komai ba zamu tafi ?Na san ki da kyankyamin abincin hanya kar mu je fa tabahuwa ta isheki." Sumayya ta tambaya tana mai dauke travelling bag din da aka yasar a kasa har ta yi niyyar tafiya da ita kuma ta tuna ba kwana za su yi ba ta ajiye.

"Kai Mama ni fa zumudi ya 'ki bari na in yi komai,so na ke kawai in gan ni a Da'kasoye." Leelan ta fada tana buga tsalle.

Ita dai Najma bata ce komai ba bayan zuba musu ido da ta yi,tunda Mahir ya ce ba zai bi su ba ta rasa walwalarta,ba don kawai karatu na da amfani ba da sai ta ce dama Mahir din ba ya zuwa makaranta. Bini Bini ya ce Lesson. Ta ja tsaki daidai da honk din mota. Ko ba a fada ba ta san Drivern ne ya iso.

***
Wurin azahar suka isa garin,all thanks to Ussy driver ,da ke dan Shafta ne gashi ya sami yan shafta su Jalila.

Tunda suka shiga garin mood din 'yan matan biyu ya canza, tun bayan da wasu yara 'kazamai a cewar Leela suka shafa motarsu suna ihun jirgi ranta ya soma baci, ruwan robar da tun da aka fara tafiya shi take sha ta rufe ta ajiye tana jin baza ta iya saka komai ba kuma a cikinta, dama haka take , abinci in dai ba a gidansu aka dafa ba bata ci.

Najma da MahirWhere stories live. Discover now