*10*

369 36 0
                                    

"Sai yau ko?" Ta tambaya tana turo baki.

"Naj Naj rigima, sai ki bari ai mu gaisa kafin ki fara aikin naki ai, sarkin 'korafi.

"To Ya Mir ka san yadda na yi missing 'dinka ne? 2 days fa ko le'kowa ba ka yi ba, gashi baka da waya balle in ari ta Mami in kiraka, kuma ka hanani zuwa gidanku ni ka'dai, na ce Yaya Salisu ya rakani jiya ya 'ki 'karshe ma da na nace musu suka ce wai ta tabbata ni 'Mayya' ce.

"Wai miye Mayya? "

"Naj Naj me nake ji  a bakinki kar in sake jin kin yi irin wannan maganar."

"Ya Mir, wallahi su Yaya Sani ne kullum in naje gurinsu wasa sai su yi ta korata suna ce min wai Mayya,tun ina hakura har na daina, na jiya ne dai ya fi bani haushi" Ta bashi amsa tana mitsittsike ido.

"I'm sorry, kema taurin kai ne ke damunki, na ce ki bar wasa da su, I'm enough, duk weekend kina zuwa gurin Maama, kina ha'duwa da su Jalila, gashi wataran itama Jalilan takan zo ku yi wasa, ki 'kyalesu don Allah bana so ki ri'ka 'bata ranki akan wannan minor issue 'din. "

"Wace Jalila? da 'kyar na bata ha'kuri ta yarda za ta cigaba da zuwa, ka san last week da tazo tsorata Yaya Sani ta yi, Allah ne ka'dai ya san me ta masa, shi ne ya je ya kai 'kara gun Ya Auwalu ba kunya ba tsoron Allah suka yi mata rubuti suka zaneta. Gashi Kai kuma ka zama busy yanzu, ba ka dawowa daga school sai 4, kuma lokacin nake tafiya islamiya. "

"Ke dai bari SSS3 'dinnan ne ba saurara mana ake ba, kwatakwata mutum bashi da time 'din kanshi, lessons upon lessons, two days 'dinnan ma CBT muke ta yi kin san JAMB ta gabato, Allah ya sa dai a samu abinda ake so kawai. "

"Amin Ya Mir, ya su Anisa? " Ta tambaya duk da ta san baya son ko ka'dan a yi masa maganar Anisa da Mahaifiyarta, su suka yi sanadiyyar rabashi da mahaifinshi, haka kawai yanzu gaisuwa ce ke ha'dasu sai kuma duk month ending zai tura mishi ku'di a account dinshi, da za a sha'ke Ahmad bai san a wane aji 'dan nashi yake ba, babu abinda ke gabanshi illa Anisa, komai Anisa, a 'yan shekarunta 'kasashen duniya ka'dan ne bata je ba, ta yi wata wayewa ta ban mamaki, ga doloncin tsiya don bata da wayo ko ka'dan duk abinda take yi Zuwaira ce take sakata.

"Farar mace alkyabbar mata,farar mace lantarkin gida. " Mahir ya fa'da yana yi mata jinjina duk a 'ko'karinshi na kawar da zancen su Anisa.

Ta saka hijabinta ta rufe fuskarta wanda ya yi sanadiyyar bayyanuwar shatin bulala hannunta na dama.

"An daketa kenan" Ya ayyana a ranshi, kafin ya tambayeta muryarta ta katseshi.

"Ya Mir ina jin kirarin nan fa nake gane abinda kake so, yau ma ba ka ci abincin ba?"  Ta tambayeshi da murmushi, don a duniya in ya mata kirarin nan takan mance da duk wata damuwa tata.

"A'a yau na ci gurasa fa, kawai dai wani abin ne daban. "

"Yanzu kai gurasa ka'dai ce zata isheka? Bari in je in dafama ko indomie ce. " Ta mi'ke da niyyar tafiya ya ri'ko hijabinta, wannan ya kuma bayyana masa wani shatin bulalar a hannun nata na dama.

"No please, bana jin yunwa ko ina ji ma kin ga ban siyo ba, ko za ki dafa min babu ne? " ya tambaya tare da ri'ko hanunta yana duba shatin bulalar.

"Yanzu Ya Mir, wannan abar dai banza indomie ba zan iya 'dauka a gida in dafa ma ba sai ka siyo ka kawo, ni sai in ga kamar baka 'daukeni 'kanwa ba. " Ta bashi amsa tana janye hannunta, bata shirya canza islamiya ba, tsohuwar islamiyarta ta bari ma saboda an daketa ne, ta tsaya jiran Mahir ya dawo ta dafa mai indomie kafin ta tafi shine ta makara aka daketa, aiko an sha bala'i a makarantar don bata ta'ba zaton Mahir na da zafin zuciya ba sai washegarin ranar, da kyar aka 'kwaci prefect 'din da ya daketa a hannunshi, kuma ya yi kashedi akan kar wanda ya 'kara dukanta a makarantar, da ta koma makarantar washegari aka ri'ka nunata da hannu ana gulmarta,  yayanta ya yi kaza da kaza, duk sai ta takura, ba shiri ta sa Abbu ya canza mata wata islamiyyar, kuma yanzu dukan da aka mata ma ko ya fi 'kuda naci bata fa'da mai.

Najma da MahirWhere stories live. Discover now