*6*

390 24 3
                                    

Alhaji Yunusa

Ana idar da Sallahr idi ya sako rusheshan tumbinshi mai kama da randar iyali da ya zauna daram cikin Babbar rigarshi a gaba, 'ya'yanshi guda goma a bayanshi suna biye da shi.

Sauri yake ya je ya bawa cikinshi hakkinshi, musamman ma dai yau da Suwaiba za ta yi wannan tuwon nata mai laushi da da'di. Tunanin Tuwon da ya yi na sa wa yawunshi ya tsinke.Duk da a 'kasan zuciyarshi yana jin kamar zai yi missing din fried rice din Sumayya, sau 'daya ta ta'ba yi waccan sallahr kuma zai yi 'karya in har ya ce ya ta'ba cin mai da'dinta, ya numfasa kafin ya kore tunaninta, ya riga ya saketa ba ya san wani abu da zai kuma ha'dashi da ita,dukda zuciyarshi na san bijire mai.

Da sallama ya shiga gidan kamshin abinci na dukan hancinshi, yana jin ko ba a gama miya ba zai iya cin tuwon haka gaya, ajiyar zuciya ya yi kafin ya soma ranga'dawa matar tashi kira.

"Suwai, Suwai kina ina ne mun dawo fa. "

Dinning area ya nufa, warmers ne jere a 'kasa kan tabarma, kallonsu da ya yi na saukar mai da wata nutsuwa ta musamman, akwai wata 'kauna mai 'karfi tsakaninshi da abinci wannan na 'daya daga cikin abubuwan da suke 'karawa cikinshi girma.

Zama ya yi akan tabarmar ya 'dan baje saboda ya samarwa hamsha'kin tumbinshi wurin zama, yana mamakin yadda cikin yake 'kara ha'baka, ya 'dan shafa cikin ta saman Babbar rigar da ta sha aiki, yana tuno lokacin da 'danshi Sani yake bashi labarin wai sun yi fa'da da abokinshi, kuma ya 'dau alwashin ba zai gayyaceshi suna ba in har Babanshi ya haihu.

"Sannu da zuwa Alhaji, sai na ga kun yi sauri, ban da'de ba da shigowa ba nima hala ba ku tsaya jin hu'duba ba. " Daga asibitin bayan sun ga Sumayya gida ta dawo don ta 'karasa girki yayinda su Alhajin suka wuce masallaci.

"Mami sai da na ce mu tsaya suka 'ki, wai su yunwa su ke ji. "  Wani yaro da bai fi shekara goma ba ya fa'da yana zama kusa da Alhaji Yunusa.

"Ba an hana ka sa baki ba in manya na magana ba, ka cigaba Yaya Sani babu kyau dai. "

"Abbu Allah ka yi wa Sabi'u magana, ya bi ya raina ni, da na ce a tsaya ba 'ki kuka yi ba ko 'karya na yi? " wanda aka kira Sani ya fada cikin hargowa kamar zai tashi sama.

"Ni ya isa don Allah, ba a isa a zauna ba sai kun yi fa'da kamar kuna ganin hanjin juna, a kanku aka fara haihuwar 'ya'ya maza ne? Kai kuma Sani ina kayanka? ka shigowa mutane parlor daga kai sai boxers ko kunya baka ji a gaban 'kannenka. "

"Mami bana son in 'bata kayana ne, anjima zan fita da su. " Sani ya 'bata amsa yana zumburo baki.

"Wai don Allah Suwai sai yunwar ta ci ni ta kasheni tukunna kan ki sallameni ne? " Yunusa ya fa'da yana 'dauko malmalar tuwon da ko kusa bata da ala'ka da kalar fatarshi.

Tana zuba miya a wani bowl babba ya kar'be,to za a iya cewa kalarsu ta zo 'daya don bowl din da ka'dan ya fi gawayi haske.

Sani ne ya yun'kuro ya zura hannu a bowl din, ya ci sa'a kuwa ya 'dauko 'katuwar cinya, bai yi wata-wata ba ya kama yaga da hakoransa kamar abinda ya zo yi duniya kenan.

"Sani ka fita idona in rufe, ya muka yi da kai jiya akan tsame? Don butar gidanku a kwanon Abbu din za ka yi tsame tsabar rashin hankali? " Babba a cikin 'ya'yan ne yayi maganar ranshi a 'bace.

"Ka ga Auwalu, ba dai a abincina ya 'dauka ba? To na yafe fid Dunya wal Akhira, naman nan gashi nan sai kun ci kun ture, me kuma na damun kanka Ha'a!!!. Yunusa ya tsawatar mai,bayan nan ya kai wa malmalar tuwon da ta kusa 'karewa hari, ya gutsiro wata 'katuwar loma da ban san inda zai saka ba, don kuwa a fuskarshi in ka cire hancinshi da goshinshi , komai 'karami ne.

"Alhaji ka daina irin haka, in yaro ya yi ba daidai ba ka bari a ringa gyara masa, wannan ba soyayya bace ba, za ka sa ya raina yayanshi ne kawai. " Suwaiba ta fada cikin nuna sarewa da al'amarin, da alama ta da'de tana ya'ki da shi.

Najma da MahirWhere stories live. Discover now