*12*

311 16 0
                                        

Sai da ya yanke farce sannan ya shiga wanka, yana ji Zuwaira nata bambami akan jiya ya musu taliya a harha'de, taliyar da ko dandanawa bai yi ba, dama ya san da haka shi ya sa ya yi wa kanshi qiyamul layli ya dafa indomie, shi ko ko a jikinshi wai an tsikari kakkausa, tsuntsun da ya ja ruwa ai shi ruwa zai daka, wani ya ce ta ce ya yi mata girki?

Da ya fito ne ya kalli agogo ya ga 'karfe goma na safe, ya koma toilet ya shanya towel din da ya goge lallausan gashinshi da shi. Cikin mintuna sha biyar ya shirya cikin riga sky blue da wando jeans shi ma blue.Signature turarenshi wato Oud ya fesa, shi ma'abocin arabian perfumes ne dama. Dukda yau juma'a, bai sa manyan kaya ba, shi ba ma'abocinsu bane, ya fi son English wear.

Dakin mahaifinshi ya wuce domin ya gaisheshi. Yana zaune a gefen gadonshi yana amfani da laptop 'dinshi, ko ba a fada ba ya san aikin kasuwancinshi yake yi. Shima yana da sha'awar kasuwanci shi ya sa ya cike Business Administration da zai yi registration 'din Jamb.

"Ina kwana Dad. " Ya ambata yana mai risinawa.

"Lafiya kalau Mahir, sai ina kuma? " Dad din ya tambaya ba tareda ya yi sparing dinshi glance ba.

"Eh dama ina so in je Farm centre ne in siyo wayar da ka ce. "

"Ohh toh toh, sai ka yi a hankali na ji an ce akwai 'bata gari a wurin, in ka dawo ka biyo ta nan akwai maganar da nake so mu yi. "

"Okay, amma in abin ba urgent bane zan iya bari sai da yamma? Saboda sallahr juma'a. "

"Take your time, babu wani abu in ka dawo sai ka zo. "

****
"Mami don Allah ba ki gani ba? "

"Wai Najma so kike da girmana in miki 'karya? Sau goma kenan kina min wannan tamabayar na ce ni banga wani Hijab blue ba, dole sai kun yi anko da shi Mahir 'din ne? "

"Mami ba ki gane wanda nake nufi ba, wannan mai hannun fa da Maama ta yi mana ni da Jalila. "

"Sai kuma ki yi, zo ki dake ni sai in gaya miki inda ya ke. "

"Shi kenan to ara min naki. " Ta fa'da cikin tsokana, ita kanta bata san yaushe ta fara wannan halin na tsokana ba, 'kila dai Jalila ce ta koya mata...Zama da madaukin kanwa.

"Je ki dauka to. " Da ya ke bata san gatse ba, sai ta nufi wardrobe 'din Mamin, aka ci sa'a kuwa ta ga sky blue 'din Hijab 'din, bata yi wata wata ba, ta janyoshi, sai dai fa ba shi ka'dai ta yi nasarar janyowa ba, harda wasu guda goma sun biyo shi.

"Najma kuma, ke 'din nan wallahi sai a hankali, yanzu Hijab nawa za ki sa? Da yake ba ki san gatse ba ko?. "

"Laaa to ai nawa ne ma, wata kin ga nawa ya fi kyau shi ne kika 'dauke, Hahan Allah ya yi dai sai mun yi ankon nan. "

Bata kwashe sauran Hijabs din ba ta nufi 'dakinta da kayanta ne kawai a ciki amma bata kwana, bedside drawer 'dinta ta je ta 'dau jakar Qur'an 'dinta mai pieces, Mahir ne ya fanso mata a cewarshi baya so tana 'daukar izu sittin, wanda ke da suratul Kahf ta 'dauka ta nufi Veranda din da suke zama tana biya haddar da za ta bashi.

Tana zaune har sha biyu da rabi ta yi bai zo ba, ta leka gate 'dinsu ya fi sau ashirin amma bata ga ko kyallin shi ba, a na ashirin da daya ne ta ga ya taho, ya yi kyau sosai, colour din sai ta dan haska shi, tunda ya hangota yake mata murmushi har ya karaso.

"Alkyabbar mata kin yi kyau sosai. "

"Har na kaika? Kayan sun ma kyau, ko in ce ka yi ma kayan kyau, amma fa yau Juma'a babbar rana, mai ya sa ba ka sa manyan kaya ba. " Ta tambaya bayan sun jera sun nufi Veranda din da ta yi musu shimfida.

"Kema kin san basa gabana, haka fa muke shan daru da Yaya akan wannan, amma Dad ke 'kara zugani ba za ki taba gani ya dinka min manyan kaya ba, kullum English wear yake siyo min.

Da ta fuskanci yanayin ya 'dan canza, sai ta yi maza ta ciro papers daga cikin hijab 'dinta ta mi'ka masa, ya karba yana mai dubawa, zanen riga ne irin wedding gowns 'dinnan, ta yi kyau sosai, sai kuma na biyun sanen moon ne da star, a kasa an sa #Najma #Mahir.

"Wannan wedding gown 'dinki kika zana? " ya tambaya da dariya a muryar shi don ya san in akwai abinda take jin kunyarshi to ya biyo bayan maganar aure.

"Kai Ya Mir, Allah bana so. " Ta fada tana cikuikuyeshi ita a dole kunya.

"Wai yaushe za ki girma ne? Na ce ki rika maintaining space a tsakaninmu ba kya ji. "

"Sowwie" Ta fada tana pouting, pink lipstick din da ta shafa yana kara nuna kanshi. Dama ita gwanar gwalli ce, in dai kwalliya ce to in aka zo gunta an gama.

"Wannan kuma Zara da wata ne, kamar ni da kai kenan, #Najma kuma na yi forming dinshi ne using 'Naj' from my name and 'Ma' from your name. #Mahir ma haka, last 'Ma' din sunana da 'Hir' din sunanka, how do you see it?"

"Wow I'm even speechless, that's very creative of you, if you use your talent wisely gaskiya zaki zama abar alfahari. Yanzu dai kar suruntun ya yi yawa dauko Quran din mu yi sauri bana so a fara huduba ba mu isa mosque ba."

***
Murmushi ne ya kuma subuce mai lokacin da yake viewing pics din Najma a sabuwar wayarshi, duk sun yi kyau duk da dai wasu shirme ne irun nata.

Da ya nuna nata wayar 'kirar infinix hauka ne bata yi ba, yadda ta rika Wow Wow kamar motar kwana-kwana. Ba shiri ta karbi numbershi, ko ba kamai za su rika magana sosai ba wai sai ya zo hidansu ba, bayan nan ta sha selfie, wasu ya yi joining amma most of the pics nata ne ita kadai.

Sai da ya gama danne dannenshi tukunna ya nufi dakin Dad dinshi.

Da sallama ya shiga, as usual Dad din na zaune a favorite spot dinshi yana danne danne a laptop.

Bayan kamar minti goma ne ya tambayeshi da:

"Ya, ka siyo wayar? "

"Eh ga shi Dad a sa min albarka. " Ya fada yana mika mai, sai da ya dan ji kunya da Dad din ya yi murmushi bayan ya ga pic din Najma da ya sa a wallpaper dinshi.

"Ohh wannan 'yar rigimar ta guje ni ko? "

"Aiko dai Dad kullum in ta ce zata zo brothers dinta ba sa yarda su kawota ni kuma bana so in daukota haka nan in taho da ita. "

"Eh to haka"

"Amma dama gobe take zuwa nan gidan Maama tunda bamu da nisa insha Allah zan daukota ku gaisa. "

"Hakan ma ya yi, yauwa yaushe za ka yi Jamb? "

"Eh to kamar dai a May aka ce. "

"Wane course ka cike? "

"Business Admin"

"Great, WAEC fa? "

"Ba za ta wuce September ba gaskiya? "

"Okay, in na canka daidai ba za a kai Babbar Sallah ba dai za ka yi grads? "

"Eh insha Allah "

"To madallah zaka iya tafiya."

"Nagode Dad Allah ya kara lafiya. "

Ya fita yana mai jin sanyi a ranshi, at least mahaifin nashi ya nuna ya san da zamanshi.

Najma da MahirWhere stories live. Discover now