"Wait wait wasa na ke miki papaya ne a ciki"
Ta bata fuska ta turo baki.
"Amman shine ka bani tsoro"
Ya mika hannu ya janyo ta ta fado kirjinsa.
"Sorry Babyna ba zan sake ba"
"Wani zai iya ganinmu fa"
Ta fada tana kokarin zame jikinta.
"Ba wanda zai ganmu"
Ya kara rumgumeta sosai yana sauke ajiyar zuciya.
"Ina son ki sosai Zinneera"
"Ina son ki Aleeya ina son ki Habiba ina son ki Ramatu, mace nawa ka fadawa haka"
Ya saketa yana dariya.
"Kin fara ko?"
"Ee ai gaskiya ce haka kuke kuje gurin wannan ku ce suna son ta kuje gurin wannan ku ce kuna son ta, ko ranar nan ma da ka kirani ai Aleeya ka ce min"
Ya sake yin dariya, sai ita tai dariya.
"Kaga ni ko? Dariya tana maka kyau shiyasa yan matan nan suke lake maka"
"Ni kam kinga na san a makarantar da kika fara yanzu, da Unguwar nan, na san akwai maza da yawa masu sonki, amman hakan be taba damu na ba, saboda na san ni kadai ne a zuciyarki, da zan hadu da mata dari kullum su ce suna so na, ba zai taba damuna ba, domin ni ke kadaice a gabana"
"Kai ma ai kasan wasa nake yi ko? But seriously am jealous, Sadiq kana da kyau sosai mata da yawa zasu yi crushing kanka, ni ba zan juri ganinka da wata mace ba, ko yar'uwarka ce"
"Eyyye Babyna an fara wayo har da su kishi haka"
Sai ta rufe fuskarta, sai kuma ta bude idon.
"Au da can bani da wayo?"
"Aa da baki da shi da ai ba zaki rika fada da Nabeel kullum ba"
Ya karasa yana mata gwalo, ta bata fuska har da rumgume hannayenta.
"Sorry"
Ya fada yana kama kunnesa alamar yana bata hakuri.
"Yi hakuri wasa nake miki, kawai na yi marmarin wannan fushin na ki ne, kin san ni komai na ki burgeni ya ke, fushinki dariyarki duk kyau suke miki, wani lokaci idan ina gida ko office na kan dauki wayata nai ta kallon hotunanki, ina jin nishadin haka, wani lokacin na kan tuna wani abu daya faru wanda ya kan saki dariya ko fushi sai na rika aina yanayinki, hakan yana kara min kaunarki. Har mahaifiyata ta sani, idan nai dariya sai ta ce Zinneera ko"
Ya karasa yana murmushi.
"Na san nafi ko wace mace a duniyar nan dacen masoyi, hakika ban yi kuken Zabin rai a matsayinka na wanda zan aura ba, wani lokacin na kan yi unkurin auna irin son da nake maka, amman sai na rasa silekin da zai dauki nauyin son balle har na iya irin kwatankwacin son da na ke maka, Umma tana yawan ce mun na yi dacen samun abokin rayuwa irinka, Abbana yana yabon kyakkawan halinka, sai dai ni kuma ina jin kamar akwai wata rana da son ka zai min illa, zai rufe idon na kasa gani a lokacin da ganin yake da muhimmanci, ya maida ni kurma a lokacin da jin ke da muhimmanci"
"Ko da mafarki, wani abu be taba tsikarata na ji akwai wata rana da zan yi zullumi ko dardar da son ki ba"
"ba zullumi na ke da dardar ba, har abada Zabin raina shine zabi bani da haufi akan zabarka a matsayin abokin rayuwa na san bazan yi nadama, a duk lokacin da nake tsara irin rayuwar zamantakewar auren da za mu yi sai na ji wani abu ya tsaya min, ban san ko minene ba, ban san mi wannan abun yake nufi ba"
YOU ARE READING
ZABIN RAI
General FictionChoice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking story.