“Amman Safiya wannan kawai be isa ya saka kui wa Zinneera aure a yanzu ba, kurciyace kowa da irin tasa, bana son ayi mata auren da zai zama bana kwanciyar hankali ba, aje a dawo ko kuma tai ta samun matsaloli a can, yi mata aure a yanzu ma tarwatsa mata karatu ne, shekarar nan ta fara karatu fa, dan me kuma za ace a katse mata karatun a yanzu, gaskiya ni bana goyon bayan wannan abun”
Daddy ya fada cike da damuwa bayan Umma ta fada masa cewar auren da gaske ne, da kuma dalilin auren.
“Ni kaina daga baya na yi tunanin haka, domin bana son abunda zai taba Zinneera, amman abubuwan da take ne suna damuna sosai, domin ba mutum mace mai hankali kamar kowa, ni ina ganin kamar iska ne akanta, yarinyar nan kamar ba ita kadai take ba”
“Babu wani aljani, kurciya ce kawai idan kun gaji da ita ku bani ni na kara, daman ta fi son zama can ai”
“Haba Yaya wane irin kurciya shekara goma sha shida? Ba kurciya ba ne wannan akwai dai wani abu”
“Aa ba wani abu, karku saka mata komai...”
Umma tayi shiru ba dan ta gamsu ba komai din ba,sai dan bata son jayayya da dan'uwanta, duk firar da suke,Nabeel be saka baki ba, Aliyu ma tuni yai bachi, suna haka Aleeya ta shigo dauke da ledodin daya ce suke su kwaso a mota.
“Ina Zinneera?”
Daddy ya tambaya.
“Gata nan shigowa, zata dauko ragowar ne”
“Okay”
Bayan ya amsa da okay ya gyara zamansa ya kalli Umma ya ce.
“Ni ina ganin zan yi magana da Abubakar ya barta ta cigaba da karatunta, zuwa nan da shekara biyu sai ayi mata auren...”
“Shekara biyu? Lokacin ai ta kara haukacewa”
Umma ta fada tana yar dariya.
“Safiya idan baku son yarinyar nan dan Allah ku ba ni ita”
“Ni har abunda na ke ganin yafi ayi mata karatu aji ko wani abun a jikinta”
Kamin Daddy ya kara cewa wani abu Zinneera ta shigo gidan da lododi a hannunta ranta duk a bace, tana aje aje lododin ta nufi dakinsu ta kwanta. Bayan kamar minti biyu da haka Sadam ya shigo gidan cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara.
“Daddy bana jindadin jikina, ina son zuwa gida”
A tsaye yai maganar wanda hakan ke nuna alamar ba ta tsawwala ya bar gidan.
“Bari na tashi mu wuce daman dan kawai na kawo ka ne ku gaisa kuma ku san juna”
Daddy ya fada yana mikewa tsaye, hannu yasa aljihu ya ciro kudi mai dan dama ya mikawa Umma, sannan ya bawa Nabeel da Aleeya da Larai. Har baki kofar gida Umma ta rako yayanta yana ta nanata mata zancen auren Zinneera akan kar ayi mata .
“Kin ga daga dawowa ta shige daki Wallahi bata son auren nan, dan Allah ku daga mata kafa ku bata dama komai zai zama daidai”
“To Allah yasa mahaifinta ya yarda, ita kuma Allah ya shirya ta”
“Amin hakan nake son jin daga gareki, ga nata aje mata ”
Ya mika mata kudin dake hannunsa. Ko da kai gurin motar har Sadam ya tashi motar. Sai da suka wuce sannan Umma dawo cikin gida rike da hannun Larai dake cike da farinciki saboda kudin da Daddy ya bata, dama haka yake musu a duk lokacin da ya zo shiyasa suke son zuwansa.
A inda take zaune ta sake zama tana kwalama Zinneera kira.“Zinneera...!”
“Na'am”
Ta amsa daga can cikin dakin sannan ta fito ta zo kusa da ita ta zauna.
YOU ARE READING
ZABIN RAI
Ficción GeneralChoice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking story.