Takowa yai ya dawo kusa da ita.
“Indai saboda ni za ki yi, to karki aikata, taya zaki auri wani wanda ba Sadia ba, saboda Sadiq? Ki kwanta tare da shi ki tashi tare da shi ki masa kalamai masu dadi sa oda Sadiq? Idan har na aminta kika aikata wannan abun na zama ragon namiji”
“Babu zancen zama jarumi ko rago a nan Sadiq, ba gazawarka ba ce, ba zai yiyu na fasa aikata abunda nai niya ba, domin naje da kaina n fadawa Abbn Sadam cewar ina son Sadam kuma na fadawa Umma cewar bana son ka, as long as zaka rike min alkawarina zan nemo kudin kuma zan dawo gareka Sadiq zamu yi rayuwa ta farinciki. Taimako daya na ke son kai kace ka janye zancen aurena da kanka ta yadda Abbah zai fi yarda da ni yai min yadda na ke so, idan kuma ba haka ba guduwa zan yi har sai kai da Abbah kun amince da auren Sadam”
Murmushi yai irin murmushin nan da ake cewa ya fi kuka ciwo, ya kalli agogon hannunsa sannan ya kalleta still yana murmushi.
“Na kagara na farka daga wannan dogon bachin da nake, komai daya faru a yau mafarki ba gaske ba...”
Ya fada sannan ya juya ya nufi motarsa ya shiga ya fisgeta kamar zai tashi sama har kura na tashi gurin. Zinneera bata aikin komai sai na hawaye, kukan ya tsaya mata amman kwalla ya kasa barin idonta. Haka ta nufi gida kwalla na mata zuba tana gogewa har bata iya ganin abunda ke gabanta sosai.
Tun daga nesa kyakkyawan saurayin dake tsaye jikin wata kotuwar mota dake kusa da gidansu Zinneera, sanye da farar shadda da hular da ita kanta ta isa ta amsa sunansa, yake mikowa Zinneera tattausan murmushi yana kallonta a natse. Tana daf da karaso kusa da inda yake ya saka hannunsa aljihu ya dauko handkerchief ya mika mata. Kallo daya tai masa tai ma handkerchief din ta dauke kai zata shiga gida, sai yai hanzarin kiran sunanta.
“Zinneera...!”
Tsaya tai kamin ta juyo ta kalleshi.
“A ina ka san sunana?”
Ta tambaya tana takowa zuwa inda yake.
“Sai kin fara share hawayenki tukunna”
Ya sake mika mata handkerchief din, sai ta karba ta share hawayen.
“Ammy ta fada min”
“Wacece Ammy? Me kake yi a nan? Waye kai”
“Sunana Suhail Muhammad amman ce min Dattijo, mahaifiyata na kawo tana nna cikin gidan”
Tsayawa tai tunani wa za a kawo cikin wannan babbar mota haka?
“Hajiya Karima?”
Ya gyada nata kai sai ta jefar da handkerchief din gabansa ta juya a fusace ta shige cikin gidan. Murmushi yai ya duka ya dauki handkerchief ya bude motarsa ya shiga ya zauna still murmushi a fuskarsa, ta cikin farin gilashin motar ya hango rubutu dake jikin ginin gidan. _Suna cewa bana tunani irin na mutane_ yar dariya yai haka kawai zuciyarsa ta raya masa cewar Zinneera ce tai wannan rubutun. Fita yai daga motar ya nufi gurin da handkerchief dinsa a hannu yana kallon rubutun kamin ya saka handkerchief din ya goge rubutun.
Duddubawa ya shigayi har ya samo gawaye yai nasa rubutun a daidai inda ya goge nata, sannan ya koma jikin motar ya jingina wannan karon fuskarsa a hade kamar ba shine ya gama murmushi yanzu ba.
*** *** **
A saman tabarma ta samu Hajiya Karima zaune Umma na daga tsaye bayan ta aje mata kofin ruwa.Wani bakin haushinta Zinneera take ji da ace ta bata kudin da duk yanzu haka be faru ba.
“Meya kawo ki gidanmu? Me kika zo yi? Wai ke baki da zuciya n...... ”
Bata rufe baki ba Umma ta wanke mata fuska da wani kyakkyawan mari.
YOU ARE READING
ZABIN RAI
General FictionChoice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking story.