“Taya taya?”
“Naje gidanka da zimmar n fadawa mahaifiyarka cewar kana asibiti sai na tararda gidan a hargice kofar kuma a bude, ta nan na ci karo da wannan littafin”
“Ba nawa ba ne”
Ya fada yana kokarin boye mata, bayan ya gama jin abun har cikin jininsa.
“Kai ne sunanka ne da na yarinyar daka kira lokacin dana kadeka”
Zaunawa tai saman kujerar tana kallon tashin hankalin dake cikin idonshi.
“Rayuwarka abar tausayi ce Sadiq kuma tabbas kana ciki hadari...”
Ajiyar zuciya ya sauke ya rasa inda zai saka kansa yaji sanyi, Zinneera ta tona masa asiri ita kuma wannan ta san komai, hakan na nufin mahaifiyarsa da yan'uwansa na kusa da jin komai, indai har hakan ne zai faru ba zai zauna garin ba, tomin ba zai yarda ayi ta yi da shi ba. Can a cikin duniyar tunaninsa ya cinkayo Ummi tana watso masa wasu kalamai da suka soma kwantar masa da hankali.
“Abunda ka aikata abu ne mai kyau Sadiq, domin ceton mahaifiyarka kai yi gashi kuma tana raye, ni kuma na rasa tawa Mahaifiyar duk kuwa da irin tarin dukiyar da muke da ita... Na san daraja uba tun daga lokacin dana rasa tawa sai nake ganin kima ko wace mace mai amsa sunan uwa...
Zuciyata cike da tausayin abubuwa biyu daka rasa, masoyiyarka wacce ta zabi wani saboda kai, da kuma kwanciyar hankali da natsuwa daka rasa na abunda ka aikata. Haka wani lokacin abubuwa suke zo mana ba yadda muka tsammace su ba, amman tabbas ka cancanci farinciki Sadiq”Komawa yai ya kwanta ya fada duniyar nazari. Can kuma ya dago ya kalleta.
“Za ki iya min wani abu?”
Ta gyada masa kai.
“Za ki iya aje min wannan sirri a cikinki?”
Dan murmushi tai kadan ta soma wasa da yatsun hannunta.
“Idan har ba zan aje maka wannan sirrin ba, ban da dalilin zubar da hawayena a kanka ba”
“Wane tabbaci nake da na cewar ba za ki fadawa kowa ba”
Tai shiru har na tsawon lokacin sannan ta ce.
“Saboda abunda zan aikata, ba zan kowa ya san sirrina ba mussaman mahaifina”
“Ban fahimta ba”
Tashi tai tsaye tana kallonsa.
“Yanzu dai ya kamata ka huku tukuna, sannan wani abun ya biyo baya...”
Kayan tea data shigo da su ta shiga hada masa, sannan ta shiga toilet din dakin ta dauko wata ruba ta tara masa ya wanke bakinsa sannan ya sha tea, bayan ya gama ya sauko yana takawa daker ya shigo toilet din yai alwala ya fito yai sallah daga zaune, sannan taje ta kira nurse ta duba shi ta bashi magani tare da wasu allurai. Bayan nurse din ta fita ne ya sauko ya dauki wayar daya jefar, abun ka da nokia ba tai komai ba sai dai marfin ne ya tsage battery kuma ya fita, sai da ya maida battery sannan ya kunna wayar. Sakon mtn ne ya fara shigo masa kamin na Zinneera ya biyo baya.
_Wallahi ban Fada ba Sadiq ka yarda da ni, ban fadawa kowa abunda ka aikata ba, kawai na ce bashi ake binka_
Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama karanta sakon, yai farinciki Sadam ya saketa amman a yadda sakin ya zo masa ne be yi masa dadi ba, zai tabbatar da gaskiyar maganar cewar bata fadawa kowa ba ne idan har ya ganta face to face. Number ta yai dialing me kamar daman can jiran kiran take nan da nan ta daga.
“Kina ina yanzu”
“Ina gidanmu”
Ta amsa tana ta kokarin danne kukan dake son hanata magana.
YOU ARE READING
ZABIN RAI
General FictionChoice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking story.