Life is short

2K 265 32
                                    

Da gangan ya haske Malika dake tsaye jikin gate din gidansa, kamin ya fito daga motar cikin bacin rai ya karasa inda gate din. Makulli yasa ya bude karamar kofar sannan ya shiga ta can ciki ya bude gate din gaba daya. Sai kuma ya koma cikin motar ya shiga da ita gida.

“Me ya kawo ki?”

Shine abunda ya fito daga bakinsa daga fitowa cikin motar.

“Na san kana da bukata ta”

“Ni na fada miki ina da bukatarki?”

“Na san ni mana, jiya shekaran jiya duk ba mu kasance tare ba”

“Arhar taki ta yi yawa Malika, ya kamata ace kina da tsadar da sai idan an kiraki ko lallaba ki zaki so ba wai ki kawo kanki ba, nifa bana son mata marar aji”

“Ina da aji Sadam, kuma ina tsada, amman a gurin wasu mazan ban da kai, bana iya daukar lokaci ban rabi jikinka ba, idan har kai baka bukata ni ina da bukatarka”

Murmushi yake a yanzu.

“Da gaske? Ashe rashin ajin naki na yayi nisa sosai, bana da bukatarki a yau fita pls”

“Sadam kana cikin bacin rai sai, zan iya kawar maka da shi a yau”

Rufe motar yai ya fara takowa zuwa inda take cikin yanayin dake nuna yana cikin tsanani bacin rai. Kanta ya rika ya turata wajen gate din da karfi ya rufe gate dinsa, sai da yaja wani dogon tsaki sannan ya nufi main house din. Saman kujera ya fara zama ba dan kuma yana son zaman ba sai dan be san abunda zai yi for now. Tafin hannunsa yake kallo tunanin yadda zai tafiyar da abun ya ke, ta ina zai fara koya ma kansa son Aleeya, ta yadda zai cire Zinneera a ransa but after every minutes fuskar Zinneera yake gani sunanta zuciyarsa ke ta kira.
  Kokarin tashi yai ya nufi dakinsa, da tunanin da yake jin yayi ma kansa girma, he find it difficult ya fitar da Zinneera a ransa, amman ta ya zai yi soyayya da Aleeya idan be cire Zinneera a ransa, this is unfair ace ya auri Aleeya da soyayyar Zinneera a ran shi, gaban madubi yaje ya tsaya yana kallon kansa. Be san sai yaushe ba, be san iya tsawon lokacin da za'a dauka ba, be san iya abunda zai hadu da shi ba, iyakar abunda ya sani dole ya cire soyayyar mutumen budurwar abokinshi kamar yadda yake wajibi ya ya koyama kansa son Aleeya.

Wani dogon nunfashi yaja ya sauke sannan a lokacin ya zauna bakin gado yana cire zaren takalmin dake kafarsa, wani abu yake ji mai tsananin nauyi da zafi ta tsaya masa a kirji. A take gumi ya fara karyo masa, zuciyarsa bata tana karbar wani abu mai muhimmanci kamar yanzu ba, be taba jin abu ya tsaya masa a rai irin yanzu ba. Kwantawa yai saman gadon yana kallon silin dakin. Ji yake ina ma ace kudi na iya canja kaddarar dake tsakanin Sadiq da Zinneera, ina ma Sadiq zai tausaya masa yace ya bar masa ita.

“Da ace na zo kamin wannan lokacin, wata kila da yanzu da ni take soyayya ba da Sadiq ba”

A fili yai magabar, yana ta tambayar kansa dalilin rashin dawowarsa da wuri.

“Saboda na hadu da Aleeya ne ko? Saboda ita ne, kaddarar so na a gurin Zinneera ne, kaddarar aure kuma a gurin Aleeya”

Ya dan yi murmushin takaici tare da jan wani dogon numfashi ya sauke, Aleeya is pretty and Daddy yana son na aureta ta tana da tarbiya and idan na aureta Daddy zai jidadi ya kamata nai yi wannan ko dan Daddy. Haka yai spending night yana kokorin neman dalilin da zai saka shi son Aleeya, a tunaninsa a dare daya zai iya cire son Zinneera a ransa ya dauki son Aleeya ya saka. Amman har garin Allah ya waye zuciyarsa sunan Zinneera take kira kamar yadda ita din dai idanuwansa ke gani. A kan idonsa kai kiran sallah asuba sai a sannan ya da bar gadon ya nufi bandaki.

  A masallaci yai azkar sai da rana ta fara fitowa sannan ya dawo cikin gidan yai wanka ya shirya cikin kananan kaya ya feshe jikinsa da turare ya dauki makulli ya nufi gurin Mommy. Horn daya yai be sake yi ba, har sai da mai gadin ya fito dan kansa ya bude karamin gate din yaga motar Sadam sannan ya dawo da sauri ya bude masa gate din gaba daya, daman dazu taji lokacin da kai horn din sai dai jin ba a kara yi ba yasa yai tunanin ko ba nan gidan ba ne.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now