Be san yadda akai ya isa asibiti ba, all what he know ya kama hanyar asibitin kuma ya hau titi @360 domin hankalinsa ya tashi sosai. Private hospital ce a take suka shiga bata taimakon gaggawa nan take numfashinta ya dawo da karfi ta bude ido tana hakki. Ta yi minti biyar tana maida numfashin sannan ta ankoro da inda take, da sauri ta tashi zaune tana kallon nurse biyu da wata likita.
“Alhamdulillah Sannu”
Likitar ta fada tana kokarin kwanta da ita.
“Kina bukatar hutu a yanzu”
“Waya kawo ni nan?”
“Wani mutum ne yana nan waje”
Ta sake unkurowa a karo na biyu zata sauko daga saman gadon wannan karon nurse dince ke kokarin riketa.
“Baki ji abunda likita tace ba kina bukatar hutu”
“Ba wani hutu ni Umma ta zanje na gani tana asibiti”
“Kema a asibitin kike kina da bukatar hutu mana”
Likitar ta fada a tsawace, sai Zinneera ta kalleta
“To ina ruwanki ijikina ne ko na ki?”
“Ke saketa”
Likitar ta fada a fusace, aiko Zinneera ta sauko ta nufo kofar fita ko hijabinta bata tsaya sakawa ba. Sadam na tsaye yaga ta fito tsayawa yai kallonta da mamaki har ta karaso kusa da shi.
“Muje ka kaini gurin Umma”
“Zinneera baki da lafiya fa”
Ya fada yana tada kansa ya kalli likitar wacce ta fito daga dakin.
“Ta ki ta kwanta, kuma tana bukatar drip da bachi ko na awa biyu ne if possible”
Sai ya maida dubansa gurin Zinneera wacce kamaninta suka nuna alamar bata da lafiya da natsuwa a lokaci daya.
“Sis ki bari a daura miki ruwan ko na minti talatin ne sai mu tafi ki duba Umma, yanzu ma bachi take dan sun mata allurar bachi Daddy ya fada min sai na da awa biyar zata farka”
“Da gaske?”
“Daddy ya fada min kuma kin san ba zai yi karya ba, gashi nan zuwa ma tare da Nabeel, kin ga idan an saka miki drip din kamin su zo ya kare ko likita?”
Ya karasa yana kannewa Likitar ido daya ba tare Zinneera ta gani ba.
“Yes zai kare nan da minti talati, hakan zai kara miki kuzari ki daina ganin wannan dizziness din”
Likitar ta fada tana dafata. Zinneera ta juyo ta kalleta.
“Kin tabbatar ba zai wuce minti talatin ba?”
“Eh idan ma ya wuce ai za a iya cire miki ko doctor?”
“Yes”
Ta dan dade tana kallon Sadam kamar ba ta yarda ba, sai kuma ya juya ya koma cikin dakin ta hau gadon da kanta ta kwanta. Sadam ma shigowa dakin yai a lokacin da likitar ta biyo bayan, he thought sai anyi rigima da ita kamin a samu saka mata drip din to his surprise sai ta mika hannunta aka saka mata allurar, wata allurar likitar ta dauko tai mata a cikin ruwan kusan kala hudu a ta biyar din ne bachi yai gaba da ita domin a cikin alluran akwai na bachi. Bayan doctor da nurses din sun fita Sadam ya jingina jikin kofar yana kallon Zinneera, kallonta na kara masa kwarjini da nishadi, haka din ma da yake tsaye yana hangota a kwance natsuwa ce ke shigarsa, ji yake kamar ace matarsa ce yaje ya daga kanta ya dora a cinyarsa ha jimke hannunta har sai ta farka ta ganta kusa da shi. How he wish yana da yancin da zai kwanta bayanta yai hugging dinta har ta farka, he just wish yana da damar da zai nuna mata yana tare da ita in every situation.
YOU ARE READING
ZABIN RAI
Ficción GeneralChoice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking story.