A tare suke karyawa da Suraiya Siyama already ta wuce scul. Kadan kadan yake cin soyayyen dankalin tana kallon tv duk da kasancewar hankalinsa baya gurin. Suraiya na son ta tambaye ko ya samu Zinneera a can kuma tana jin tsoro sai dai ganinsa yai da safe ya bata mamaki sosai.
Wayarsa ya ciro ya kira Zinneera bugu daya ta daga kamar mai jira, sai kuma tai shiru bata ce komai ba, shi ma be ce mata ba yana ta sauraren yadda take sauke numfashi.“Ba za ka yi magana ba?”
“Kin yi breakfast?”
“Eh”
“Okay”
Daga haka ya kashe wayar yana kallon Mommy wacce ta fito part din Daddy dauke da kayan da ya ci abincin da su, sai da ta isa kitchen ta aje kayan sannan ta dawo dinning ta zauna tana hade hannayen rigar bachin dake jikinta.
“Favorite mun yi magana da Daddy ka gobe za muje Kaduna ni da kai mu dauko Zinneera zata fi samun kulawa a nan fiye da ko'ina”
Da sauri Sadam ya kalleta baki bude sai kuma ya runtse idonsa gam ya murja su ya bude ya kalleta.
“Mommy da gaske? Ke kike cewa haka?”
Farin cikin da ta gani shimfide a fuskar danta saboda wannan maganar da tai masa sai yasa ta ji kunya da kuma tausayin danta, taya uwa kamar ita zata hana danta abunda yake so, kuma he choose ya hakura saboda ita.
“Yes Fav”
“Oh really Mommy”
Cewar Suraiya baki har kunne. Mommy ta yi dan murmushi irin na su na manya sannan ta sauke ajiyar ba tare da ta ce komai ba.
“Idai har Daddy ne ya saka ki dole Mommy ki fada min”
“No ni na yi masa maganar da kaina, shima mamaki na yake”
Ta fada with smile on her face.
“Mommy ki na son ta yanzu kenan?”
Mommy ta dan yi shiru na wani lokaci kamar b zata ce komai ba, sai kuma ta soma magana a hankali.
“Ina ganin ko Umma ba ta fi mu nunawa Zinneera soyayya a gidan nan ba, mun so ta sosai musamman Daddy ku, a lokacin ma ba musan cewa za ka zo a ganta ka so ta ba, idan Umma ko Abbanta sukai mata wani abu, a nan take zuwa, ni nake dai nake mata horo ta hanyar sakata sharar gida ko wanke wanke, Daddy ku ma ko tsawa baya mata komai tai sai dai yai dariya yace kurciya na tare da ita. A lokacin da ka zo ka nuna ita kake so, sai naji nafi kowa sonta a duniyar nan, ko a gurin aurenta kadai mun nuna mata gata, tun da ba abunda iyayenta suka siye, kuma ko ba kai ta aura ba dole nai mata haka balle kuma ta ce dana take so. Amman abunda tai ya bani mamaki kuma ya bani tsoro sosai, har yanzu ina jin cewar indai Sadiq yana nan zai iya cutar da kai ko da bata hanyar Zinneera ba, ba wai bana son Zinneera bane dole ne wajizi na so abunda da na yake so ko dan farin cikinsa, na sani tun farko be kamata na ce a zubar da cikin ba, amman ina tsoron kar cikin yasa ta samu wata dama ta cutar da kai, sai dai a yadda ka fada min cewar mahaifiyarta ma bata son cikin yasa ni jin babu dadi Umma be kamata tace a zubar da cikinka ba ai right? Amman kuma idan na duba naga cewar ni ce na fara yin hakan sai na ji babu dadi, da nice mahaifiyar Zinneera ba zan iya gudunta ba, ba zan iya son a zubar da cikin ba, bana jin akwai wani abu da Suraiya ko Siyama zata aikata a gidan da zai saka na kyamace ta, as young as Zinneera ace kowa ya gujeta abun tausayi ne, and yes you're right mahaifiya tana da muhimmiyar rawar da zata taka a rayuwar yarta, indai har Zinneera ta gyara halinta ta zama macen kwarai muna mata barka da zuwa a matsayin sukarmu”
Mommy ta fada idonta cike da kwalla. Sadam ya bar kujerar da yake zaune yaje kusa da mommy ya rumgumeta ta baya.
“Daddy yai mana komai tunda har ya iya zabo mana ke a matsayin uwa, kina fahimtar komai yadda ya kamata i love you so much”
YOU ARE READING
ZABIN RAI
General FictionChoice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking story.