At Hospital

1.5K 229 17
                                    

Doc Tahir Na daf da fice daga falom ya laluba aljihunsa ya juya da sauri yana fadin.

“Tsaya keys din motar na kan dorowarka”

Dakin ya koma da zimmar daukar keys dinsa.

“Sadiq,... A a hadari? Aa kar ya mutu... Sadiq ba yanzu ba.... Innalillahi...”

Abunda Zinneera ke fada kenan tana kwalla, ganin Doc Tahir ya shigo yasa tai saurin rufe bakinta tana kallonsa kamar daman can ta manta da inda take sai a yanzu ne ta tuna. Kallonta kawai yai sam be yarda ya nuna mata wata alama da zata gane cewar yaji maganarta ba, sai ya karasa gurin bedside drawer din ya dauki keys din ya juyo ya sake kallonta a karo na biyu sannan ya fice.

Yana fita tai saurin dukawa ta dauki wayar ta ta kasheta gaba daya ta zauna bakin gadon har lokacin tana kwalla. Ji tai kamar tai tsalle taje taga halin da yake ciki amman babu dama, waya kade shi? Garin ya aka kade shi? Yana da rai ko ya karya ko kuma ya mutu... Tayi zurfi gurin wannan tunanin da har bata iya jin shigowar Sadam ba sai da ya dafata, sai ta kalleshi a razane tana wani irin daukar numfashi. Shi dan kallon mamaki yai mata ganin yadda ta dawo cikin hayyacinta kamar wacce aka jefowa nunfashi daga sama, babbar rigarsa ya cire ya zauna kusa da ita yana murmushi tare da kai hannu ya rika hannunta.

“Sorry na razana ki... Na razana ki a lokacin da be kamata kiji tsoro ba a rana irin wannan mai muhimmanci da daraja a garemu...”

Sam hankalinta baya gurinsa babu kalaminsa ɗaya daya shiga kunnenta, har sai da ya kai yatsansa ya shafi gefen fuskarta a hankali yaja shi har zuwa gurin wuyanta, lumshe ido tai ta sauke numfashi a hankali hawaye na cigaba da mata zuba, zuciya kuma tana azalzalarta da halin da Sadiq yake ciki. Hannayensa biyu yasa ya juyo da fuskarta saitin tasa har suna iya shakar numfashin juna, ya kai bakinsa saitin cheek dinta inda hawayen suke mata zuba ya sumbace ta sannan ya hade front head dinsu guri hancinta na gugar nasa yana ta kallon fatar idonta yayinda nata idanuwan suke a lumshe.... Sun fi minti biyar a haka sannan yaja ta zuwa kirjinsa ya rumgumeta tsantsan. 
Fashe tai da kuka sosai ta kankame shi sosai tana jin kamar Sadiq yake rungume da ita. Mayafin kanta ya janye ya soma shafa bayanta a hankali alamar rarrashi.

“Ranar yau tafi ko wace rana a gurina daraja da martaba a gurina, na dade ina jiran zuwan wannan ranar, ranar da zan yi raya sunnar manzo na, na taba halalina, sai kuma ta zo min a yanayin da yafi ko wane saka ni farinciki wato aurenki Zinneera...ban san sau nawa zan fada miki ba, ban san yadda zan kwatanta miki ba ki gamsu ba, iyakar abunda zan iya zan nuna miki kauna kyautatawa soyayya gata da zaki tabbatar da cewar lallai kin yi dacen mijin aure... Ina kaunarki sosai Zinneera ban taba jin so wata mace a zuciyata kamar yadda nake jinki ba, ban taba son wata ya mace ba sai ke...”

Kamar wacce ta tuna wani abu sai tai hanzarin dagowa ta raba jikinta da nashi tana share hawayenta. Murmushi yai yana kallonta kamar zai hadeyeta.

“Bachi nake ji”

Ta fada ba tare data kalleshi ba sai kokarin haurawa kan gadon take. Hannu ya kai ya riko farar kafarta wacce tasha kumshi ya shafota ya daga kafar yai kissing din feet dinta.

“Alwala ya kamata mu yi a yanzu mu godewa Allah sannan ki ci abinci kamin mu kwanta”

Wani jarrr taji sai tai saurin janye kafar.

“Bana sallah kuma ban jin yunwa”

Kallonta yai da idonsa da suka soma canja kala murya can kasa kasa kamar mai rarrashi ya ce.

“Kin tabbata? Ba wani abu zan miki ba, sallah kawai zamu yi sai mu kwanta”

“Ina da alwala ta tun a gida”

“Okay amman sauko kici abinci kuma ki canja kayan jikinki lace din jikinki yana da nauyi ba zai bari kiyi bachi da dadi ba, ni kuma ba zan bar abunda zai hana ki jindadi ba, ki saka kayan bachi suna can a wardrobe ni bari nai alwala sai mu gode ubangiji”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now