Komawa Daddy yai ya zauna yana kallon Umma da mamaki, Sadam kuma ya tashi tsaye yana cizon bakinsa ya nufi dinning.
Mommy kamar zata ce wani sai kuma tai shiru domim tasan halin Daddy baya son tana saka baki idan yana magana da yan'uwansa. Daddy yai dan murmushi yana kallon Umma a natse.“Na san abunda kike ji a yanzu Safiya, kamar ace Suraiya ta aikata makamancin hakan ne ga wani wanda na zaba mata, bacin rai da kokarin gyara zai iya sakawa na bashi Siyama, amman ba a wannan lokacin ba, kwana hudu zuwa biyar aka daura auren nan, cikin kwanakin nan abubuwan nan suka faru, shi kansa Sadam yana ciki damuwa da dimauta a yanzu, ina ganin be kamata muyi masa wannan maganar ba, kuma be kamata mui saurin yanke hukunci ba, har yanzu zuciyata bata natsu da abunda nan ba, ko da kuwa da gaske to dole ya zama cilasta mata akai yi, ba ni na haifi Zinneera ba, amman akwai kyakkyawar alaka da fahimtar juna tsakanina da ita, wacce nake ganin ko tsakaninta da mahaifinta babu ita, tana yawan fada min duk abunda akai mata daga kanki har mahaifinta, na bata shawara na bata na fada kuma sai na nuna mata a hankalce, a gurina har yanzu har gobe Zinneera yarinya ce Suraiya ma mai shekara ashirin da shida yarinya nake daukarta balle Zinneera”
Cikin kuka Umma ta ce
“Duk abunda ta aikata da gangan ta aikata saboda ba ni na haife ta ba, kurciya a ba hauka ba ce, Aleeya kanwarta ce amman nasan ba zata aikata abunda Zinneera ta aikata ba”
“Duk yaushe ne Zinneera tasan cewa ke ba mahaifiyarta ba ce? Bayan kuma kin riketa kamar mahaifiyarta, ba ki yi tunanin saka miki ya kamata tai yi ba, sai kuma hakan ya biyo baya? Ya kamata ku bincike yarinyar nan”
Sam Umma bata yarda cewar Zinneera ta aikata hakan dan an cilasta ba ne, ta fi yarda da cewar ta aikata hakan ne saboda tasan Umma ba mahaifiyarta ba ce dan haka zumuncin da zai lalace ba zai dame ta ba.
“Ni na so ka amince Wallahi ko dan na wanke wa Sadam zuciyarsa daga bacin ran da wannan yar ta saka mana”
“Kawai muyi addu'a Allah yasa hakan ne mafi alheri, amman zancen auren Aleeya ki aje shi gefe, be kamata ma a kawo wannan maganar ba, kada ki biyewa zuciya ki yi mata abunda baki mata a baya ba, kar shaidan ya zugaki ki goge ladarki , kuma ina son zuciyarki ta daina raya miki cewar saboda baki haifi Zinneera ba ne tai aikata miki hakan ki dauka ita da Aleeya duk daya ne”
“Har a bada naka naka ne, wanda ba naka ba kuma ba zai taba zama naka ba, ba zan taba ganin Zinneera da gashi ba...”
Ta fada tana mikewa tsaye. Mommy na kallonta ta ce
“Gaskiya kam Zinneera tai ba zata, ba ke kadai ba mu kanmu ba mu tsammaci haka daga gareta ba sam”
“Ai wannan abun ni taiwa ba kowa ba, ba dan Allah yasa ma Suraiya ta gani ba da sai ta aikata kamin asirinta ya tono”
Duk abunda ake har aka ci aka sude Sadam dake dinning be ce uffan ba, sai juya tea dake cikin cup yake. Bayan Umma ta wuce ne ya taso ya nufo inda suke ya zauna a kasa cikin ladabin daya hana shi dago kai ya kallesu.
“Daddy Mommy wata alfarma nake nema, dan Allah ku taimaka ku bar maganar nan a tsakanin mu, bana son sai Sadiq ya shigo ciki maganar nan, ya riga yasan abunda ya aikata kuma zai ji kunyar sake aikata wani abu gobe ba”
“Amman wannan maganar ba abar kyalewa ba ce Sadam, ya kamata a dauki mataki, waya sani ko yana can yana shirya wani abun dabam”
Mommy ta fada.
“Gaskiya kam, nima abunda nai tunani kenan shiyasa nake son ayi tsakani duk abunda ya same ka shi za a zarga”
Sai a lokacin ya dago ya kalli Daddy.
“Ni ba yaro ba ne Daddy, ni kaina ba wai haka zan barshi ba, nasan matakin da zan dauka, amman dan Allah ab zai munje gurin police ba anyi wannan statement din”
YOU ARE READING
ZABIN RAI
General FictionChoice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking story.