38

1.2K 224 80
                                    

“Ki amsa mana ko ba magana ake miki ba? Baki da wani abu da zaki wanke kanki ko? Baki da wani abun cewa shiyasa kikai shiru kina mana kukan munafurci”

Mommy ta fada a fusace. Zinneera kam babu abunda take sai aikin hawaye, bata jin nauyin wani abu kamar yadda take jin nauyin Sadam da mahaifansa da kuma Umma a yau ba, sun cika mata ido ta ko'ina da har bata iya daga kai ta kallesu, ji take kamar ce komai a mafarki ne na gaske ba, ina ma kasa zata bude ta nutse a ciki...

“Zinneera ki ce wani abu mana...”

Sadam ya kira sunanta kamar mai koyon magana gaba daya jikinsa yai sanyi.

“Babu wata kalma da zan fada ta wanke ni a gurinka ko a gurin iyayenka Sadam, dukan abunda zai fito daga bakina ba zai yi ma kowa dadi ba, iyakar abunda zan iya fada shine ba kai yake nufin na kashe ba, aurena yake nufin na kashe”

Ta fada muryarta na gargada still kanta na kasa. Mommy ta tabe baki.

“Karya kike Allah dai ne ya tona asirinku, kuma Wallahi dana yafi karfin ku, sannan bari kiji na fada maki duk abunda ya samu dana sai na hukunta ki”

Sai a lokacin Zinneera ta dago idonta da suka kumbura sukai ja ta kalli Mommy.

“Kuna da damar ku yi duk abunda kuke so, saboda abunda na aikata nasan be kamata na aikata hakan ga danku ba, amman bana da wata mafita ne sai wannan”

“Me kike kokarin fada?”

Umma ta tari numfashinta tana zare mata ido alamar karta fada. Amman sai ta risina kasam guiyoginta tana kallon Sadam.

“Ka yafe min Sadam, ban aure kan dana kashe ba, Sadiq be turo min sako dan na kashe ba. Amman a yau ina son ka san gaskiya, ban aureka dan ina sonka ba, sai dan nemanwa Sadiq mafita... Naira miliyan ashirin ake binsa, kuma bashi da inda zai same su shiyasa na yake shawarar aurenka wata kila ta hakan na samu hanyar da zai biya kudin ba da amincewarsa na.... ”

Zinneera bata karasa ba, Mommy ta dora hannu aka tana salati Daddy kuma kai ma Zinneera kuri da ido. Sadam kan murmushi yai idonsa suka cika da kwalla, sai ya sauka daga kan gadon ya nufi kofar fita, da sauri Suraiya da Mommy suka rufa masa baya. Daddy ya kalli Umma wacce ta dora hannu a ka tana kuka ya ce.

“Kar abunda tai ya dame ki, na san ba za a hada kai da ke a cutar da Sadam ba, ba kuma zata nemi shawararki lokacin data aikata ba, Yayan zamani ne wadanda soyayya take canja musu tarbiyar iyaye zuwa nata, muje na sauke ku gida”

Kasa cewa komai Umma tai dukan kokarinta na taga ta tsagaita kukanka ne, tana gaba Zinneera na biya kowa sai kallonta yake yadda take zubarda hawaye kamar an mata mutuwa, ta kasa daga kanta har suka isa gurin motar Daddy, gidan baya Zinneera ta shiga baya. Umma tai tunanin ko gida zai wuce ya aje su tare amman sai taga Daddy ya fara isa gidan da aka kai Zinneera ya tsaya ta gate ya juyo ya kalleta.

“Fita ki shiga gidanki”

“Gidanta kuma? Ai kamata yai mu wuce gida tare da ita kawai”

Umma ta fada still tana hawaye.

“Shi zai yanke hukunci idan zata zauna a gidansa ko aa, Sadam ba karamin yaro ba ne, at least ya san cewa ita din barazana ce ga a rayuwarsa...”

Wani irin abu Zinneera taji ya ratsa mata zuciya marar dadi har sai ta lumshe ido ta bude, sannan ta fita daga motar ta tsaya bakin gate din tana kallon motar Daddy har ta daina hango shi. Samun kanta tai ta kasa shiga cikin gidan, tana jin kunyar kallon gate din gidan ma balle kuma ta shiga ciki ta zauna. A saman wani dan suminta ta zauna wanda aka zagaye fulawon kofar gidan da su, sai ta kasa kanta cikin guiyoyinta tai ta ranka kuka. After like one hour wata bakuwar mota ta doso gate din, Zinneera bata dago ba har motar tai horn aka bude mata ta wuce ciki, sai kuma ta ji an sake bude karamar kofar gate din. Kallonta bayanta kawai Sadam ke yi, zuciyarsa na sosuwa da kalamanta na dazun, wanda sanarwar mutuwa sunfi masa dadi sau dubu akan abunda ya ji, ina ma Suraiya bata binciki wayarsa ba, da duk wannan be faru ba, domin kazantar da baka gani ba tsabta ce, ko kadan hakan be taba soyayyarta a zuciyarsa ba, sai dai ya bude wani sabom shafin bakinciki da nadamar aurenta a rayuwarsa...
  Bata waigo ba, har sai da taji an rufe gate din sannan ta mike tsaye ta kama hanya ta soma tafiya ba tare da ta sa inda zata je ba, domin a yanzu tana halin rana zafi inuwa kuna, sai dai komai fushin da Umma zatai da iya bata da kamar gidan mahaifinta.
Da hawaye shakaf ta tare mai Napep a gafen titi tana rokonsa.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now