A harabar gidan yai parking. Sannan ya kalli Zinneera ya ce
“Sis fita ki shiga Mommy tana ciki”
“Allah yasa ba wani laifi nai mata ba”
Zinneera ta fada tana yar dariya.
“Kin taba mata laifi ne?”
Ya tambaya idonsa akanta kamar zai cinyeta.
“Kamin na shiga university, idan na yi ma Umma laifi tana kira Daddy ta fada masa saboda Abbah yana min fada, shi kuma Daddy sai ya fadama Mommy sai Mommy tasa a dauko ni a kawo ni gidan ta hukunta ni, saboda Daddy ma baya iya min komai”
Sadam yai murmushin da be san ta ina ya zo masa ba, har yanzu kallonta yake ya kasa dauke idonsa akanta.
“Fada min wani irin hukunci take miki?”
“A ranar ni zan share gidan nai mopping ko ina, kuma tace ni zan girka abincin da zan ci da kaina nawa ni kadai, kuma tasan ban iya ba”
“Kamar ya baki iya ba?”
“Idan na girka chabewa yake ko kuma hannayena su lankwshe na kasa yin aikin”
Ya dan yi shiru alamar mamaki yana kallon kofar falon da aka bude.
“Kamar ya hannayenki suke lakwashewa? Umma bata saka ki girki ne?”
“Bata sani cewa take bana yin na masu hankali, imagine komai Umma cewa take na mahaukata nake, kowa haka yake ce min”
Har ya bude baki zai sake wata maganar, sai ya hango Mommy wacce ta fito sanye da doguwar rigar buba da lace mai dan karan tsada. Kallonsu take cike da burgewa, yadda Sadam ya dora hannunsa saman sitari ya karkata ya maida hankalinsa gurin Zinneera, ita kuma tana da faman murmushi mai yanayi da dariya.
“Look at them...”
Ta furta tana musu kallon burgewa. Kamin ta soma ta ko stairs din ta sauko ta nufo inda suke. Ganin hakan yasa Zinneera bude motar ta fito.
“Mommy laifi nai?”
“In ji wa?”
Mommy ya fada tana mika mata duka hannayenta biyu, ta rika na Zinneera sai ta rumgume ta, abunda bata taba mata ba. Fitowa Sadam yai a motar ya tsaya yana kallonsu, murmushi yai haka kawai sai abun ya burgeshi.
Zinneera ta dago ta kalli Mommy.“Mommy lafiya dai?”
“Lafiya kalau”
Sai rika hannunta suka nufi cikin falon. For the first time Mommy ta rika ta ta zaunar sannan ta zauna kusa da ita.
“Tausayi kike ba ni, kawon ki ya fada min aure za'a miki”
Ba laifi nan kam ta dan ji kunyar Mommy yar da sadda kai kasa.
“Eh amman Mommy kin ga ai na huta da fadan da muke da Umma”
“Amman Zinneera karatunki fa?”
“Sadiq ya taba fada min tun kamin na shiga makarantar cewar zai barni na cigaba da karatuna ba zai hanani ba, kin ga shi ya siya min form din ma”
Mommy ta kawar da fuska kamin ta sake kallo ba Zinneera.
“Amman kin tabbatar kina son Sadiq din nan ko kuwa ko dai cilasta miki akai? Dan mu dai fada mana kawai akai wai za a miki baiko washe gari aka kawo mana minti da goro wai na baikonki, waya sani ma ko cilasta miki akai?”
“Aa ni nace ina son shi”
“Kin tabbata? Amman an bincika ansan waye shi? Yana da aikin yi ma, ina kika hadu da shi?”
YOU ARE READING
ZABIN RAI
Fiksi UmumChoice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking story.