37

1.7K 263 46
                                    

Zubewa tai kasa tana duba gurin da Sadiq ya samu rauni fuskarta shar da hawaye.

“Wannan be dace ba, akan me zaku masa haka sai kace wanda yai sata?”

Ta fada a tsawace tana kallon sojojin cikin bacin rai. Raliya ta dafa cike da mamaki.

“Ummi ke fa ya mara”

“Dan ya mareni sai a wulakantashi? Shi ba mutum ba ne? Baki kyauta min ba, ban jidadi ba”

Ta kara fashewa da kuka tana kallon raunukan dake jikinsa tana jin kamar a jikinta ne suke.

“Ku kaishi asibiti mana, ku dauke shi ku kai shi asibiti kar ya mutu....!”

Da su take magana amman babu wanda yace mata uffan har sai da mahaifinta ya basu umarni. Sannan duka cirashi sama da sauri suka saka shi a motar ita kuma ta nufi cikin gidan da sauri tana kuka.

“Ke ke lafiya”

Bata ko ji maganar da Ammy take mata ba ta shiga dakinta ta dauko gyalenta da jakarta tana ta kuka ta fice daga falo. Da mamaki Raliya da Daddy suka shigo falon bama kamar yadda wanda yasa aka aikata abun dole daukar mata fansa.

“Wanene wannan yaron?”

“Nima ban sanshi ba”

Raliya ta amsawa Daddy tana kokarin saman carpet yayinda shi kuma ya zauna saman kujerar dake kusa da Ammy.

“Me akai ma Ummi ta shigo tana kuka ta dauki jaka ta fita”

Raliya ce ta labartawa Ammy abunda ya faru tun daga kan hadarin da akai har zuwa abunda ya faru yanzu.

“Toh yau kuma Ummi ce a haka? To Allah ya kyauta, amman be dace ba kai kayi hukunci ita kuma ta nuna hakan be dace ba, ai ko dan ganin idonka ya kamata ta kyale... ”

Ammy bata karasa ba Daddy ya daga mata hannu.

“Maimunatu na sha fada miki cewar bana son kina fadar laifin Ummi, babu ruwanki da abunda zatai ko tai, laifin ba nata bane nawa ne, daman be kamata nai haka ba, tunda sai wanda ya isa yake iya daga hannu ya mari Ummi...”

Yana kawai nan ya tashi ya nufi wani bangare na falon. Ammy ta bashi da kallo tana tabe baki

“Muje zuwa indai Ummi ce kana nan zata saka ka kuka, ba kace baka son ganin kukan yarka ba to ita zata saka ka”


***     ***     ***

Da motarta tabi bayan sojojin asibitin da aka fito dashi aka koma wato uduth, kai tsaye emergency aka karbeshi ita tai ta zirga zirga har aka gama gyara gurin daya jimu wani gurin kuma aka saka masa bandege sannan aka kaishi wani dakin dabam na musamman kamar yadda ta bukata bayan ta biya kudin dakin wato Anas room.
   A bakin kofar dakin ta tsaya rike da kofa tana kallonsa zuciyarta cike da tausayinsa, idonsa a rufe suke yana motsa su alamar yana jin zafi sosai har yanzu.

“Sannu.... ”

Ta fada muryarta na rawa, sai ya bude Idon kadan ya kalleta ya maida ya rufe yana cizon baki sakamakon wani azababben zugi da yake ji. Hannu ta kai ta share hawayenta taja kofar ta rufe, jinginawa tai da kofar ta lumshe ido tana jin kamar wani jigo a rayuwarta akai ma haka.

“Daddy be kyauta ba, be dace yai haka ba”

Magana take da kanta zuciyarta na sosuwa da abunda mahaifin nata yai.

“Ya kamata na bawa iyeyensa hakuri, kuma na sanar da su.. Amman ina zan gansu?”

Ta tambayi kanta tana mayarda atm dinta cikin ja. Kofar fita daga ward din ta nufa zuwa parking space, tana shiga motarta ta dauki hanyar Aliyu Quarters inda ta san sun kade shi da dare lokacin da take tare da mahaifinta, a tunaninta can iyayensa suke rayuwa tare da shi, lokacin data isa unguwar tambaya ta fara yi tana kwatanta yanayinsa da sunansa tun ana kaita gurin wasu masu irin sunansa har tai dacen aka nuna mata gidan Sadiq. A bakim kofar gidan tai fakin ta fito ta soma tawaka zuciyarta cike da kwankwanton idan gidan, domin bata ga alamun dake nuna cewar mata suna rayuwa a gidan ba. Hannu ta kai ta fara knocking kofar falon tana kallon yanayin kofar gidan, shiru ba a amsa mata ba, hakan yasa ta sake yi, a karo na uku ta kai hannu ta murda kofar sai taga ta bude. Da dan tsoro ta tura kofar ta shiga tana waige idan wani ya ganta.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now