Kuka tai sosai har sai da ta ji kukan ya isheta dan kanta sannan tai shiru tana sauraren yadda zuciyarta take bugawa. Sai da Sadam ya tabbatar ta natsu sannan ya tashi ya shiga kitchen ya dibo mata ruwa mai sanyi ya dawo falon.
“Zinneera...”
A natse ya kira sunanta, sai ta dago jajayen idanuwanta da suka kumbura saboda kuka ta kalleshi. Ruwan hannunta ya mika mata, tsayawa tai kallon ruwan kamar ance mata duka mafitarta da damuwarta suna ciki.
“Sha”
A tunaninsa bata fahimci abunda yake nufi da mika mata ruwan da yai ba. Sakin Mommy tai ta mika hannunta ta karbi ruwan ta sha kadan sannan ta kalli Mommy.
“Mommy ke ba yar'uwata ba ce ko? Komai da nake tunani ba shi ba ne”
Mommy ta shafa kanta cike da tausaya.
“Har gobe mu yan'uwanki ne Zinneera, Kamar yadda Umma take uwa a gareki”
Ta soma wasa da kofin ruwan dake hannunta.
“Miyasa baku taba fada min cewar Umma ba ita ce mahaifiyata ta asali ba? Ko a fira ko a wasa wani be taba fada min ba, baku yi tunanin raina zai yi kuna kamar yanzu ba?”
“Ba mu boye miki dan mu cutar da ke ba, sai dan tunanin Karima ba zata taba dawowa ba, kuma idan har kisan gaskiyar cewar mahaifiyarki ta tafi ta barku ba zaki taba jindadi ba, dukan mu munyi hakan ne saboda farincikinki”
“Amman Abbah fa? Shi ma ba mahaifina ba ne?”
“Mahaifinki ne, Umma ma mahaifiyarki ne saboda ta shayar da ke”
“Bana son ganin kowa a yanzu”
“Yes a nan za ki zauna har zuciyarki ta huce”
“Zuciyata ba zata taba hucewa ba Mommy, har sai idan za a fada cewar wannan duk ba gaskiya ba ne”
“Gaskiya ne Zinneera komai gaskiya ne”
Sadam ya fada.
“Wani guri na ke so, wani guri inda ba zan ga kowa ba inda babu kowa sai ni kadai”
“A nan za ki zauna na wani dan lokaci, ba za ki ga Abbah ba, ba za ki ga Umma ba kuma ba zaki ga kowa ba har sai kin bukaci hakan, as long as kina nan hankalin kowa zai kwanta okay?”
Ta daga kai ta kalli Sadam.
“Okay?”
Sai ta gyada masa kai.
“Good girl, zanje anjima na dauko miki kayanki gida, daga nan zan rika kaiki scul na dauko ki”
Mommy ta dora da.
“Tashi kije ki yi wanka yanzu sai ki ci wani abu”
“Ba zan iya cin komai ba”
Ta fada cikin kukan da take jin yana son kara taso mata yanzu. Sadam ya karbi kofin ya aje
“Tashi ki wasa ruwa za ki jidadin jikinki”
Sai kuma ya kalli Mommy.
“Bari naje na dawo”
“Okay”
Sai da ya saka hannyensa aljihu sannan ya fice yana auna irin bacin rai da bakinciki da Zinneera take ji.
*** *** ***
Ko da Daddy ya shiga gidan ya tarar da Umma tana aikin kuka hankalinta duk ya tashi sai neman Zinneera take, a tunaninta ta gudu zuwa wani gurin ne. Har sai da Daddy ya fada mata cewar tana gidansa.“Wai ya akai wannan lamarin ya faru?”
Bata boye masa komai ba tun daga farkon zuwan Karima gidan har zuwa yau.
YOU ARE READING
ZABIN RAI
General FictionChoice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking story.