35

1.8K 256 98
                                    

Bayan ya hada nata tea ya dawo dakin rike da dashi ya zauna kusa da ita ya kai hannunsa daya ya taso ta. Ya soma hura tea sannan ya kai mata a baki.
  Kadan ta kurba ta kawarda kanta ta koma ta kwanta.

“Da kin yi hakuri ki dan kara sai ki sha maganin”

“Ba sai na sha ba, ni bana son magani”

Ta fada tana kara dunkulewa, murmushi kawai yai ya aje kofin ya hau saman gadon can baya ya rungume ta suka soma bachin tare. Guraren goma saura na safe Mommy ta aiko musu da abincin safe wannan karom direban kawai aka bawa ya kawo a lokacin Zinneera nata bachi Sadam ne ya karbi abinci ya jera shi a dinning, ko da ya dawo dakin Zinneera na zaune saman gadon tana karema dakin kallo. Hannnunshi ya kai zai shafa fuskarta sai tai saurin tashi tsaye ta matsa daga inda yake fuskarta a hade kamar ya mata wani abun. Matsawa yai kusa da ita.

“Minene?”
 
Kallonsa kawai tai ta dauke kai ta nufi bandaki shi kuma ya bita da kallo yana murmushi yasan wannan baya rasa nasaba da abunda ya faru jiya wata kila shiyasa take fushi da shi. Fita yai daga dakin ya shiga dayan dakin wanda aka zuba nasa duk wani abu nasa a ciki ya bude laptop dinsa yana duba wasu abubuwan, murmushi kawai yake na tsayawar Zinneera a ransa.
Bakinta ta da fuskarta ta fito daga bandakin ta nufi inda wayar Sadam take ringing, ganin number Suraiya yasa taki dagawa sai kawai ta nufi gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta. Yadda zata iya rusa farincikin Umma Mommy da kuma Daddy cikin sauki take tunani, yadda idan ta kashe auren ba zasu zargeta ba.
  Turo kofar dakin yai ya shigo ta cikin madubin yake kallonta yana mika mata kyakkyawan murmushin har ya karaso inda take tsaye ya kai hannunsa ya dafa ta ya sumbanci gefen fuskarta.

“Zo muje ki yi breakfast”

Bata ce masa komai ba. Yajata jikinsa suka nufi falo, shi ya hada musu komai sannan ya zaunar da ita zai soma bata ta kawar da fuska.

“Bana jin yunwa”

Ya aje spoon din.

“Zinneera akwai abunda yake damunki ne? Kin kasa sakewa?”

“Bana jindadin rai na ne?”

“Miyasa wani abun kike so ne? Fada min ko minene zan miki shi Zinneera, saboda ki yi farinciki na aureki”

Juyowa tai ta kalleshi.

“Kawai ina tunanin abunda zan yi na sakawa Mommy da Daddy akan abunda suka min ne?”

Hannu ya kai ya rika hannunta ya matsa kadan.

“Babu abunda zaki musu face ki zauna da dansu zama na amana na farinciki da jindadi, kuma ke ma ki saki ranki ki yi rayuwa kamar ko wace mace a gidan mijinta, wannan kadai ya isa ya saka su farinciki”

Hannun nasa ta kalla sai kuma ta maida dubanta gurin abinci ta dauki spoon ta fara ci da kanta.
  Misalin biyu da wani abu na rana ya fita daga gidan zuwa kiran da Daddy ke masa. Be yi minti talatin da fita ba Mommy ta aiko musu da abincin rana wannan karon da wasu yan uwanta aka zo suka amarya sannan direba ya karbi tulolin sa aka kawo abinci jiya da kuma na yau da safe ya koma tare da su da mutane.

***   ***   ***

Ya kasa banbance dayan biyu zuciyarsa nata raya masa Sadam ya kai ga jikin Zinneera.

“Sadam ba zai kyaleki ba, ko dai kin boye min gaskiya ko kuma kina yaudararta ne”

Ya mike tsaye daga zaune da yake ya nufi windows yana kallon waje.

“Sadam ya nema a waje ma balle a cikin gidansa, Sadam ya samu komai da yake so Zinneera you're fool, kin bashi komai a saukake...”

Saurin juyowa yai da sauri jin an taba kofar yana kallo Ummi wacce ta shigo yanzu tare da wata budurwa da ba zata wuce sa'arta ba.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now