Tana shiga cikin falon Hajiya Karima ta durkushe a gurin ta fara kuka saboda bacin rai, da sauri Hajiya Karima ta yo kanta a firgice tana neman ba'asi.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”
Mai aikinta ta fada. Hajiya Karima kuma ta rika Zinneera tana kokarin tashinta amman kafafunta sun lauye guri daya tana ta dalalar da yawu a bakinta kamar wata musaka.
“Zinneera Innalillahi”
Hajiya Karima ta fada tana kiran sunanta.
“Ba Zinneera ba ce”
Zinneera ta fada cikin muryar maza, ba shiri Hajiya Karima ta sake ta ta tsallek can gurin kofa ta tsaya tana lekanta.
“To su wanene?”
Mai aikin Hajiya Karima ce ta tambaya tana busa mata iska a goshi.
“Mu ne mu ne Maryama da Duna”
“Me akai muku? Lafiya?”
Shiru ba su sake cewa komai ba, Hajiya Karima ta fita da sauri zuwa kiran mai gadinta, abun ka da ustazu ana fada masa ya dauko qur'anensa ya nufo cikin falon, a nan ya hau yi mata karatu tun tana lankwashe yatsun hannunta har ta saki ta tashi zaune.
“Su waye ku?”
“Duna ne”
Dayan mai muryar maza ya amsa.
“Miyasa kuka shiga jikinta?”
“Son ta muke?”
“Ya akai kuka shiga jikinta?”
“Tun tana karama mike cikin jikinta, a lokacin da aka aje ta bakin kofa mu kuma munje wuce sai muka shiga jikinta”
“Ku musulmai ne?”
“Aa amman yar'uwata Maryama musulma ce ni arne ne”
“Me da me kuke saka ta?”
“Bama saka yin komai sai dai kullum muna tare da ita musmman a lokacin da take al'ada domin bata tsare addu'a a lokacin”
“Me ya kawo ku yanzu?”
“Saboda ranta ya 6ace ne, bama son ranta na 6aci bama son ana taba nana goďiyarmu, shiyasa muke cutar da duk wanda ya taba ta”
“Wa da wa kuke cutar?”
“Mutane da yawa, kuma duk abunda take mu muke saka ta, mu kuma dauki layinta mukai siffar Sadam muka bata, mu muka kawo mata wayarta da Umma ta karbe, mu muka yi mata siffar mahaukaci muka bita har cikin gida komai da take gani muke mu muke mata mu muke sakata”
“To yanzu me kuke so?”
“Bama son komai amman duk wanda ya bata mata rai sai mun taba shi”
“To yanzu ku fita ku bar jikinta kun san dai Allah yai mu dabam yai ku dabam ko?”
“Za mu fita amman zamu rika zuwa ziyararta lokaci lokaci”
“To kufi ta bakinta dan kar ku cutar da ita”
Attishawa tai tayi sosai sannan ta daw hayyacinta har tana kallon mutane da idonta a kumbure.
“Sannu”
Hajiya Karima ta fada tana kallonta cike da tsoro da kuma tausaya. Kai kawai ta iya gyadawa sai mai gadin ya ce a bata ruwa mai sanyi ta sha kuma tai wanka, laraba mai aikin ce taje ta debo ruwan ta bata ta sha mai yawa sannan Hajiya Karima ta rika ta suka shiga dakinta, sai da ta huta sannan ta shiga bathroom tai wanka ta canja wasu tufafi ta kwanta saman gado tana hutawa, wani irin ciwon jikine ta ji ya baibaiye gaba daya jikinta yana ta ciwo kamar wacce aka yiwa duka.
Misalin biyu na rana ta shiga bandaki tai alwala tai sallah azahar tana zaune saman carpet Alhaji Musa ya shigo wato mahaifin Nooriyyah kuma mijin Hajiya Karima a yanzu. Zinneera na ganinsa tai saurin gaishe shi ya amsa mata cike da far'a da kuma kulawa.
YOU ARE READING
ZABIN RAI
General FictionChoice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking story.