“Umma Wallahi Abbah ya ce na daina tsayawa cikin sanyi”
Ta fada tana marairaicewa kamar zata narke a gurin.
“Ai kin san da tsanyin kika shiga ruwa”
“Fitsari na je yi fa, shine aka sako da ruwa”
Umma ta dauke kaita daga barin kallonta ta maida hankali gurin carbin da take ja a hannunta. Ganin hakan yasa Zinneera komawa cikin ruwan tai ta wankanta har aka gama sannan ta sake tsayawa jikin kofar tana rokon Umma ta bata zanen daurawa, daker Umma ta kukata har ta jefo mata zanen, bandaki ta shiga ta cire tufafin jikinta ta ɗaura zane ta fito, tana dariya abunda tai ɗazun ne ya dawo mata a rai. Da ɗai ɗaya ta shiga shanya kayan tana ta ƙyalƙyatar dariya.
“Allah yasa dai ba haukace mana za ki yi ba”
Cewar Umma wacce ta fito rike da kwanonin abinci daga dakinta ta kawosu harabar da ake wanke-wanke. Zinneera ta kalleta tana cigaba da dariyar.
“Wallahi Umma yau na kusa haukata mai napep din da ya kawo ni”
“Me kika masa?”
“Kin san ko da na fita ban karya ba, da kudin dawawar na karya na shiga Napep ban bashi kudi ba ina ta fira da shi har muka kawo, sai na ce masa yayi hirar kudinsa, da ya nuna zai min tijira na fira Ya Nabeel na ce gani nan wani zai taba ni, sai ya ji tsoro ya gudu”
Umma ta tsaya kallonta tana mamkin ikon Allah.
“Zinneera anya ke kadai kike kuwa? Ki sa mutum ya kawo ki har kofa gida kuma ki ce ba za ki bashi kudi ba? Anya wannan Makaratar ta ki zata daure ma? Abu kike kamar marar hankali”
“Kin san dai Abbah ya ce a daina ce min mahaukaciya ko?”
Ta fada tana turo baki. Umma ta girgiza kai.
“Addu'a yanzu kuma ban san wacce zan miki ba, Allah ya shiryaki in kina da rabon shiryuwa amman abunda kike ba na masu hankali ba ne, Na san Sadiq da yasan yadda kike a zahiri ba zai yarda ya kawo kudin tambaya a gidanku ba, dan babu wanda zai so auren mahaukaciya”
Har cikin ranta Umma ke wannan maganar dan a ganinta Zinneera bata da cikakken hankali ko kuma tana da aljanu, sam bata mata kallon mutum kamar kowa a rabin mutum take kallonta.
“A haka yake so na ni burge shi ma na ke”
“Aa kawai dai yana fada miki haka ne saboda ba yadda zai yi kuma Allah ya dauki son ki ya saka masa a zuciya, amman mutum mai natsuwa da hankali kamar Sadiq ba zai so mace irinki ba, a gaban kowa kina iya shuka rashin mutunci, mutum ko ya haifi ubanki sai ki cire ta ido ki rakka masa rashin tarbiyarki, kowa kina iya fada da shi a gaban kowa, baki kunya kowa ga rashin kunya kamar ya kasheki, bakar magana ko kamar da ita aka haifeki, abunda kike ko Aleeya da Larai basa yinsa”
“Amman Umma kullum ni kike ganin bana da mutunci, su baki ganin abunda suke min, sai dai ni ko harar mutum nai sai ki ce na cika fitsara ko bani da hankali, Ni bari ma na shirya na wuce islamiya na huta”
Ya karasa tana nufar dakinsu.
“Da yafi miki, shi ma Mai Napep din wani abu yai miki kika zalince, Lahira kyaji da hakkinsa marar mutunci”
Tana shiga ta shirya cikin uniform dinta na islamiya purple, ta dauki jakarta ta rata ta fito tana murzawa fuskarta mai daga bakin kofa. Har ta nufi kofar fita daga gidan bata ji Umma ta ce mata Allah ya tsare ba balle dawo ki ci abincin. Sai ta juyo ta kalli Umma.
“Ba zaki ce na dawo na ci abincin ba ko?”
Ko dagowa Umma ba tai ta kalleta ba balle har ta samu damar amsa mata, ita kuma ta juya ta fita cikin fushi tana ta gunguni.
YOU ARE READING
ZABIN RAI
General FictionChoice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking story.