SADAM POV.
Baya baya ya zauna saman cushion yana maida numfashi.
“Ba wani abun damuwa ba ne Sadam calm down, ba yau aka fara ba, kuma ba kanka farau ba, kaje kana son yarinya kuma wani ya rigaka har an mata baiwa, thats fine... Ka kwantar da hankalinka wannan ba wani abun ba ne...”
Shi da kanshi yake magana da kanshi yana kokarin karfafa ma kansa guiwa da kalmomin da shi kanshi yasan yaudarar zuciyarsa ne kawai yake. A iya kokarin sa yake na ganin ya daidai numfashinsa ne ta yadda zai samu zafin jikinsa ya sauka wai ko hankalinsa zai kwanta. Amman ina kwanciyar hankalin da natsuwa sune abubuwan da suka masa kaura a yanzu. Mikewa yai tsaye ya nufi windows falonsa dake saiti da tsakar gidansu Zinneera ya daga labulayen yana hangen muradin ransa, hasken dake tsakar gidan be wadacin gidan gaba daya ba,amman hakan be hana Sadam hango fararen hakoran Zinneera ba, da alama wani labarin ake daya bata dariya sai wasar hakora take tana jinginawa da jikin Aleeya...
Wani yawu ya hade da karfi ya kai dayan hannunsa yana balle maballan rigarsa zafin dake jikinsa sai karuwa yake...“That's fine too, kana son ta wani ya rigaka, Allah ka bani wacce ta fita...”
Ya furta yana hade wani abu da ya tsaya masa a wuya da karfi. Sannan ya bar jikin windows din ya nufi bedroom dinsa, saman bed dinsa ya zauna ya dafe kanshi, yana sauraren wani yanayi da be taba tsintar kansa a ciki ba. Ganin zaman ba zai masa ba yasa ya kwanta yana matse each and every fingers of his. Tashi yai zaune ya yana busar iskan dake bakinsa, daga bisani kuma ya mike tsaye yana lalaben aljihunsa, sai yanzu ya tuna da ya bar motarsa a family house, domin data Daddy suka zo nan. Wani bangare na dakin ya nufa sai gashi cikin wani madaidacin daki mai cike da kayan kawa, wani madaidacin glass ya bude ya dauki keys din mota ya fito da sauri kamar an korashi. He needs to see his mom hi need to talk to her yasan kalmominta ne kawai zasu kwantar masa da hankali ko da ba zasu sama masa abunda yake so ba. Gurin da jeren motoci uku suke ya nufa ya bude wace keys dinta ke hannunsa ya shiga, har ya tashi motar sai kuma ya fito yaje ya bude gate ya fita da motar ya sake dawowa ya rufe sannan ya koma cikin motar ya kama titin gawon nama. Gaba ya sauke gilasan motar iska na shigarsa ta ko'ina amman haka be saka jikinsa ya daina zafin ba, kamar yadda yake jin zafin har cikin zuciyarsa.
Ya danna horn sau biyar zuwa shida kamin abu masa gate din gidan, a daf da kofar shiga falon yai parking ya fito ya nufi cikin falon jikinsa har rawa yake ya kai hannunsa ya bude kofar falon, sai Siyama ya bude masa tun kamin ya karaso. Shiga yai falon ya zauna saman kujera ya dafe kansa, kana ganinsa kasan ba kalau ba. Rufe kofar Siyama tai ta nufi upstairs da sauri. Yadda ta bango kofar dakin Mommy ta shigo yasa ta aje sarkar gold din dake hannunta ta kalleta.“Ke lafiya...?”
“Mommy Favorite your Favorite, ya shigo cikin damuwa sosai ko a parking dinsa ma bana mutane masu hankali yai ba...”
Ta fada cikin rada tana ware hannayenta.
“What happened to him?”
Mommy ta tambaya tana kokarin mikewa tsaye.
“I don't know”
Siyama Said.. Kofar fita Mommy ta nufa Siyama na bayanta, a tare suka sauko kasa.
“Favorite...”
A hankali ta kira sunanshi tana zama kusa sa shi, sai ya dago kansa ya kalleta yana share gummin daya tarar masa a gaban goshi. Hannu Mommy ta kai ta taba jikinsa, sai taji zafi sosai, ether one or two things, ko dai ciwon cikinsa ya motsa ko kuma wani abun tsoro da bacin rai ya sameshi a lokaci daya, tafi ta'alaka abun da bacin rai domin be taba mata complain din ciwon ciki ba, sai dai idan an kaishi asibiti likitoci su tabbatar da haka, shi ma kuma in few years back ne domin tun da ya bar kasar bata sake jin makamancin hakan ya same shi ba.
YOU ARE READING
ZABIN RAI
General FictionChoice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking story.