Cancellation

1.8K 275 69
                                    

Tun daga lokacin da abun ya faru yau kusan kwana biyu kenan Sadiq baya iya cin wani abun kirki sai ruwa, da zarar ya dawo daga office yana cikin gida shi kadai. Baya aikin komai sai tunani da neman mafita, duk inda zai waiga ya waigo baya ganin mafita har sai idan legal abu zai aikata wanda baya fatar hakan, and Zinneera taki ta sauko idan yaje zai yi ta tsayi har ya gaji ba zata fito ba, idan kuma ya kira wayar da ta aiko masa sako da ita sai taki karba, duniyar ta masa zafi ya rasa inda zai saka kansa.

Har yanzu ya kasa yarda cewa Zinneera saboda shi za tai, indai saboda shine ya kamata ta saurareshi kuma ya kamata ace tana daukar kiransa ko ta fita idan yaje kofar gidansu, amman bata masa ko daya, babban abunda yake sa ya kara yarda da hakan ganin yadda Umma bata cewa komai idan ta ki fitowa, abun har mamaki yake bashi, ko da wasa be tsammaci haka daga Zinneera ba.
A iya abunda yake tunani kuma abunda zuciyarsa ke raya masa, Zinneera tana son auren Sadam ne kawai ba dan ta taimaki shi ba. Ya mirgina daga kwance da yake yana ta tunanin abunda ya aikatawa Zinneera ta canja masa lokaci daya, sai kokarin gano abunda Sadam ya fishi dashi yake wai ko samu dalilin da yasa Zinneera ta bar shi ta koma gurin Sadam.

“Miyasa na fada mata gaskiya from first place why?”

Ya furta yana kaiwa gadon naushi, a tunaninsa da be fada mata gaskiyar ana binsa wadannan kudin ba, ai bata da wata mafita da zai saka ta kishi, wata karya ya kamata ya yai mata ba wai ya fada mata gaskiya ba.

“Kina damar zabawa yayanki uba na gari Zinneera, na san ban dace da ke ba i know, I'm bad person i kill my own friend, i save my mother da kudin haram...”

Magana yake da kansa idonsa cike da kwalla, yana jin kansa wani guilty, ya matsa hannunsa.

“Amman ko yanzu baki zabi miji na gari ba, indai har kika auri Sadam, na san ya fini kudi, amman zan iya baki dukan farincikin da zaki samu a gidansa wanda kudi da soyayya zai samar miki, matan waje ba zasu barshi ya iya kula da ke ba Zinneera, you're fool”

Ya mirgina a karo na biyu yana fuskantar wani gefe na dakin.

“Zan miki yadda kike so, Zinneera indai har hakan ita kadai ce hanyar da zan nuna miki kaunar da na ke miki i will”

Sauka yai a kan gadon ya nufi bandaki yana jin jikinsa kamar marar lafiya.

SADAM POV.

Hankalinsa ya kasa kwanciya, yana jin nauyin kuma rashin kyautawa idan har ya auri Zinneera bayan an bashi Aleeya, budurwar abokinsa bayan kuma be san me ya raba tsakaninsu ba.   Mikewa tai tsaye rike da mug din dake hannunsa ya nufo falo, ji yai baya bukatar tsayawa a ko'ina sai inda zai hango Zinneera wato jikin windows din da yake hango tsakar gidansu. Hannu ya kai ya yaye labulen windows cikin sa'a kuwa ya hango Zinneera tsaye tana kokarin saka hijabinta fuskarta kalar tausayi.
  Be san yadda akai ya samu kansa cikin murmushi ba, wani farinciki da shauki ya lullube masa zuciya, baya iya misalta yadda yake ji idan idanuwansa sukai arba da Zinneera. Jinginawa yai da windo yana kurba tea. He was just imagine yadda zai yi rayuwa da ita idan ya aureta, ranar da ya aureta ace ta zama halalinsa, sai ya manta da komai a lokacin.

“Zan baki kyakkyawar kulawa Zinneera, zan miki gata zan gusarda duk wani bakinciki da damuwa da ke zuciyarki....”

Shi yake magana da kansa amman idanuwansa suna kanta. Ita kuma kamar ance ta daga ta kalli gurin sai ta zuba wa window ido kamar ta san da mutum a gurin, ba dan tana ganin kowa ba, sai dan tasan Sadam na cikin gidan a halin yanzu...
   Ayyana yadda zasu zauna da juna take, yadda za tai rayuwa da wani namijin da ba Sadiq ba. Kwana biyu nan duk ta lalace ta rame sosai kamar mai ciwo, bata wani cin abincin kirki sai yawan tunani da damuwa. Yau ma bata jin zata iya cin komai da safen nan, dan haka tana gama saka hijabinta ta nufi dakin Umma.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now