36

1.6K 278 32
                                    

Zinneera na karanta sakon ta dago da sauri ta kalli Suraiya hankalinta a tashe, so take ta tantace idan Suraiya taga sakon ko kuma akasin haka, sai dai yadda Suraiya ta sakar mata ido tana mata kallon tuhuma ya tabbatar mata da cewar takaranta sakon. Da sauri Zinneera ta juya rike da wayar ta nufi kitchen, sai kuma ta juyo da sauri ta nufi dakinta kamar wacce ta rikice.

_Zinneera inda har da gaske saboda yana ni kikai auren nan, to ya kamata ki kashe shi yanzu, karki tsaya neman hanyar kudi zan..._

Haka Suraiya tai ta maimaita sakon a ranta tana kokarin gano abunda Zinneera take boye, tashi tai ta nufi dakin da Zinneera ta shiga.
Safa da marwa ta samu Zinneera na yi a cikin dakin sai dai ganinta ya saka Zinneera kokarin daidaita natsuwarta. Kallon mamaki da tuhuma Suraiya take mata.

“Waya turo miki sakon nan Zinneera”

Ta tambaya kamin ta karasa kusa da ita. Sai Zinneera ta dauke kai kamar bata ji ba.

“Wa zaki kashe dan'uwana?”

Da sauri Zinneera ta kalleta fuskarta na bayyana tashin hankalin dake cikin zuciyarta, bakinta har rawa yake gurin amsa wa Suraiya.

“A'a Wallahi ba wanda za a kashe, wrong number ne”

“Babu wani wrong number ba, ai ya rubuto da sunanki, Sadam yake nufin ki kashe ko wanene”

A take idon Zinneera suka cika da kwalla, a yadda take tunanin Suraiya ta dauki abu ashe har ya wuce nan, a tunanin Suraiya zata fahimce cewar tana waya da wani namijin ne da aurenta, ashe ita wata daukar dabam take ba wacan ba.

“Na rantse da Allah ba Sadam yake nufin na kashe ba Wallahi ba Sadam yake nufi ba”

“To wa yake nufi? Waya turo miki sakon? Kamar ya akanshi kikai?”

Tuni hawaye ya wankewa Zinneera fuska kuzari da sauran karfin jikinta da take da shi yana kokarin guduwa ya barta, jin zargin da Zinneera take jifanta da shi.

“Wanene...!”

Suraiya ta daka mata tsawa har sai da ta firgita.

“Wani ya gada kai ki kashe dan'uwana ku kwashe dukiyarsa ko?”

“Aa Wallahi ba Sadam yake nufi ba, aurena yake nufin na kashe, ni ba zan iya kashe kowa ba, wai ke ba zaki gane ba ne?”

Zinneera ta fada tana kara fashewa da kuka.

“Taya za ayi na fahimta bayan abunda idanuwa suka gani? Kin bani mamaki Zinneera har wani zai hada kai da ke yace a kashe Sadam? Wane makiyinsa ne wannan? Me Sadam yai masa?”

“Sadiq ne! Amman Wallahi na rantse miki da Allah ba Sadam yake nufin mu kashe ba, aurena yake nufin na kashe”

“Sadiq...”

Suraiya ta maimaita sunan a bakinta tana kallon Zinneera wacce ke aikin kuka cike da tuhuma, kamin ta juya da sauri ta fita daga dakin ta nufo falon inda kawayenta biyu suke zaune.

“Sisters ku tashe muje Mommy ta kirani tace na dawo gida yanzu nan...”

“Lafiya...?”

Daya daga cikinsu ta tambaya.

“Ban sani ba, amman dai tace ko minti biyar karna yarda na kara na dawo gida yanzu, ko na barku a nan naje ns dawo”

Da sauri suka mike tsaye dayar tana rataya jakarta. Sai ga Zinneera ta fito da sauri tana kuka ta nufo gurin da Suraiya take tsaye tana jiran kawayen nata.

“Wallahi Suraiya ba abunda kike tunani ba ne, na ran... ”

“Karki fada min komai, babu kalmar bakinki da zan saurara, kui sauri muje”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now