"Akwai wani wani Sadiq a cikina, wanda ya saka ni aikata abunda ban taba tsammanin aikatawa, da ace ni Sadiq ne na ainahi a wacan lokacin da yanzu duk haka be faru ba"
Ta kalleshi da kallo irin na rashin fahimta.
"Kana da aljanune?"
Sai ya juyo ya kalleta idonsa cike da kwalla.
"Ni din dai ne, wacan mummunan hali nane, wani bangare ne na zuciyata da yake saka ni aikata abunda ban taba tunanin aikatawa ba"
"Ni duk ban gane wannan abun ba, sace ni zaka yi, kai dan fashi ne, wani Sadiq ne a cikin ka ban gane komai ba"
Juyar da fuskarsa yana fuskantar titi.
"Ina da shekara takwas mahaifina ya saka ni makarantar boko, a kaidar gidansu ko kuma na ce na kakanina ba'a saka mutum boko sai ya sauke kur'ane, saboda suna ganin kamar wacan karatun zai iya saka mutum mantawa da addininsa, mahaifina ba mai wadatar arziki ba ne, amman yana da rufin asiri saboda manomi ne, ni da shi muna noman wata gona daya gada a gurin mahaifinsa, akwai wata rana ba zan manta ba malaman gona suka zo tare da wasu yan boko yadda ake turanci ake magana sai kawai ya burge mahaifina, sanadin hakan ya saka ni makaranta a nan cikin garin sokoto, domin a wacan lokacin muna Tangaza local government ne, a gurin yayar mahaifiyata na zauna, Hajiya Samira, a lokacin ita tana babbar makaranta domin ita a birni ta tashi kuma ta auri dan boko, ba kamar mahaifiyata ba, a gurinta na zauna daga gidanta na ke takawa da kafa naje makaranta, ajinmu daya da Sadam, wannan dan'uwan na ki, muna da kyakkyawar fahimta tun muna yara, wani abu baya shiga tsakaninmu, banbanci na da shi, daya ne, shi yana dan mai kudi ni kuma ina dan talaka wani abun sai dai na ji ko na gani a agareshi, idan wani abun ya tashi na makaranta mahaifina yana aikowa da kudi ayi min komai, a haka har na gama makarantar primary, da taimakonsa da na mahaifiyata naje makarantar secondary, a lokacin aka canjawa Sadam makaranta zuwa wata dabam ni kuma nai Sultan Bello, idan na bukaci wani na karatu ko na ci, cikin kwana biyu za a aiko min shi, duk burin mahaifina nai karatu, ashe a lokacin yana fama da ciwon hawan jini ban sani ba, be yarda a fada min ba, saboda kar na saka damuwa araina, domin ya kwallafa karatuna aransa, ganin ni kadai ya haifa namiji, na gama karantar secondary da credit 9, daman can ni ba yaro ne mai sawasa ba, da wannan jajircewar na shiga Usmanu dan fodio University, a lokacin Sadam na waje yana karatu, gidan da yake ciki ya saida ya biya min duk wani abu da nake bukata na karatu shi ya kama haya, sauran kudin yasa na saka a account idan wani abun ya taso sai dai na zara kawai nai, da haka da haka har na gama university, a lokacin ciwon har ya fara cin karfin mahaifina, naje bautar kasa Anambra a can wani kauye, idan ina sallah sai a tsaya kallona irin nayi sabon abunda basu taba gani ba, a haka dai cikin takura nai na gama, dana dawo sai na tare a kauyen mu Tangaza saboda bana jin sakewa a gidan Hajiya Samira, kuma jinin mahaifina ya fara nisan da ya kamata na zauna kusa da shi, mahaifina ya yi murna da karatu, duk kuwa da kasancewar karatun lafiya mahaifina ya so nai amman rashin wadata tasa dole nai degree in business and administration.
Babu yadda zan yi ba akan mahaifina ya siyar da gonarsa ya nemi mahaifiyarsa amman yaki, wai ya gadi gonar a gurin mahaifinsa, shi ma mahaifinsa ya gada a gurin kakansa kuma nima yana son na gade ta. Yana yawan fada min, ka kula da yan'uwanka, saboda ku samu rayuwa mai kyau na tsaya kan karatunku, saboda na san kai ma wata rana za ka zama wani abu da za ka iya taimakon yan'uwanka. Hakan yasa na kara dagewa a duk inda naji ana neman aiki sai na tura takarduna, inda wasu yan'uwa na birni kuma duk na rarraba musu ko Allah zai sa a dace, a lokacin da naji ana neman aiki a CBN, mahaifina yana cikin tsantsar rashin lafiya, wanda har yasa yai fargabar tafiya na barshi a haka, da naje nai applying na dawo sai na tararda mummuna labari, ba a kai gawarsa ba, amman an masa sutura an masa sallah..."A daidai gabar yai shiru saboda kukan da ke son cin karfinsa, wasu hawaye masu zafi na ta masa zuba. Hannu Zinneera ta kai ta kama hannunsa sai ya matse hannunta sosai ya juyo ya kai hannunta a goshinsa ya rumtse ido, sai dai hakan be hana hawayensa zuba, kamar yadda na ta hawayen ke zuba.
YOU ARE READING
ZABIN RAI
General FictionChoice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking story.