37.paradis

3.1K 368 50
                                    

*♡TUNTUBEN HARSHE🌺*
_Voyage within the hearts!_

        *WATTPAD*
  *@SURAYYAHMS*
_Brilliant writers   Association_

_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_

37 paradise

Asad yana kwance a daki kawu ya kira shi awaya ya amsa da sallama kawu yace masa "Maza ka shirya ka fito zamu tafi yola mu dauko nadra" asad rasa amsar da zai bayar yayi dan ji yayi komai ya tsaya masa, sai da kawu yace "kaji abinda nace kuwa?Da sauri yace "yes,yes..sir" a hanzarce ya mike yana tunanin anya yaji abinda yace din kuwa? Ya daiji kamar ance yola kuma ance nadra, sai ma a lokacin tunanin shi ya dawo.

Yau nadra zasu je su dauko a yola har da shi,aransa yace what? It means yau zai ganta kenan? Wani tsalle yayi ya sauko daga kan katifar sa ya fito palo yana neman azad ko dan yayi confirming, yana fitowa kuwa sai ga azad yana shigowa da sauri,azad ya kalle shi yace "a haka zaka je dauko amaryar taka"

Asad ji yayi kamar kafafuwan sa ba zasu dauke shi ba, ai da uban gudu ya koma daki sai kuma gashi ya sake fitowa da gudu yace wa Azad yau zamu dawo ko kwana zamu yi? Tsaki azad yyi ya duba agogonsa yace "sai dai mu kwana ai it is already late wallhy wajrn da nisa, dan dai baba ya matsa tafiyar nan ne amma da mun bari kawai sai da safe"wani harara asad ya watsa masa bai ma ji karashen maganar ba ya koma dakin

ba'afi minti biyar ba sai gashi ya fito a shirye da jaka a hannunsa babu azad a palon dan haka ya fita waje ya saka kayansa a motar da zata kai su airport, ji yake kamar yaje ya chichchibo duk wanda za'ayi tafiyar dasu suzo su tafi kawai,sai leke leke yake gani yake kamar duk suna sane d zakuwar sa suke masa saibi.

It seems like eternity to him kafin su mama su fito Yaji dadi da ba mota daya zasu shiga ba

shi da Azad ne mama kuma ita da kawu..Sai gab da azahar suka  iso yola aka kai su wani gida acan wani karamin kauye inda sauran yan uwan mama na suke inda na fara xuwa da kawu afarkon zuwan nu nigeria

Asad da azad suka sauka a guest house,duk shi dai kawai jira yake yi suje waje na,har sai da zasu kwanta azad yake masa bayanin fa ba'a nan nake ba yace ina can cikin asalin garin yola ne waje kawu na amma gobe muna tahowa  muna hanyan zuwa nan,Ranar Asad yadda yaga rana haka yaga dare.

wani irin farin ciki yake ji da wani irin sona a ransa sannan kuma da kakkarfar fargaba what if yanzu kuma nace bana son shi Tunda shi ya jawo min duk wannan wahalar da na sha?

yasan dai ina cewa bana son shi yau kawu zai kore  maganan auren He will then be back to square one."Allahumma ajirni fi musabati"ya furta yana me sauke ajiyan zucia

Washegari tunda yayi breakfast yake zaune kamar dondi..gabansa ne kawai yake ta faduwa sai can bayan azahar Azad ya shigo yana famar dariya,Asad yasan me zai ce masa

Azad yace ai sai ka shi.."sun zo..nasha mamaki kana nan ya baka je kayi mata oyoyo ba?
Tsaki asad yaja sai ya zauna akan kujera yana rike kansa cikin boye fargaban sa wani dariyar azad yayy yace"jarumtar kenan? Kar ka bani kunya mana ni da na saka ran zaka fita a guje kaje ka ture mama ka rungumo mana nady?"

Hararar sa kawai asad yayi dan shi kadai yasan me yake ji a ransa na tsoron hada idanun sa dani.

Azad cikin neman magana ya sake cewa"kaga ni na fita zan yi waya, in ga kama ragwantar ka fita driver zai kaika inda suke zan same ku a can" aikuwa Asad tsaban fargaba sai bai iya fitan ba har sai da kawu ya kira shi a waya yace sun kusa gama wa su zo su same su Da sauri ya dan watsa ruwa ko zaiji garau ya chanja kaya yana kallon kansa a karamin mirror maybe ma cewa zata yi bai yi mata kyau yauba ya cire hular ya ajiye sai kuma ya sake daukawa ya mayar agogon sa da takalmin sa duk ya kalla Sai kuma yaji wani haushin kansa me yasa yake jin tsoron yar wannan  yarinyar ne? Koma me zata ce ta fada din yade san yana son ta kuma hakan baze taba sauyawa ba,ahakan sai Ya fito aka kai shi can wani gidan inda su nadra suka sauka,
Sai ya fito daga car ya jingina da jikin mota yana jiran fitowar sun wayarsa ya dauko yana daddan nawa amma sam ba wai yasan abinda yake yi bane jim kadan sai ji yayi kamar ana kallon sa kuma har cikin kahon zuciar sa yasan cewa itace kuma yasan daga wanne side take..

TUNTUBEN HARSHEWhere stories live. Discover now