shafi na d'aya

710 42 5
                                    

  *🌸🌸NURAAZ...!🌸*
       _(Treasure of noor)_

         *©OUM MUMTAZ*

        *1*

" *ANTY JANAN* dan allah karki barsu su fitamin da *ANTY HANAN* wallahi na daina mata rashin kunya, daga yanzu dik abinda tacemin nayi wlhi zanyi, *MAMI* dan Allah ki sakeni karsu tafi dan Allah!"

Wani karamin yaro ne da bazai gaza shekaru goma na haihuwa ba ke ta faman rantaba ihu da kururuwa yana naiman kufcewa d'aga rik'on da wata mata da zata bama shekaru talatin baya ta masa, itama sosai hawaye ke zuba daga cikin idanuwanta,fuskarta tayi jazur,ga dikkan alamu ya nuna ta jima tana kukan.
Mata ne zazzaune sanye suke da hijabai,wanda dayawa daga cikin way'annan matan idan kuka gansu zakusan cewa sosai suke cikin damuwa,sabida fuskokinsu ta gaza b'oye kalar tashin hankalin dasuke ciki dik da ma sunyi k'ok'ari k'warai da gaske a dai-dai wannan lokacin wajen hana hawaye malalowa daga cikin idanuwansu...!

wata mata ce da itama takan iya bama shekaru talatin baya wasu mata wajen su uku ke ta rirrik'eta sabida yadda take ta faman turjiya tana wani kuka mai matik'ar tab'a zuciyar mai sauraro tana rok'onsu saketa amma ina? Haka nan suke ta tausar zuciyarta suna nuna mata d'aukar kyakkyawar k'addara da kuma akasinta.
Sannan daga gefe d'aya na hango wata matashiyar budurwa da a k'alla zata kai shekaru sha bakwai tana zaune kanta kallon sama ta lumshe idonuwanta sosai hawaye ke ambaliya bisa ga kamilalliyar fuskarta, kallon farko idan ka mata zaka fahimci t'sant'sar kamarta da wannan matar dake rik'e da wannan yaron da har yanzu ihunsa da kururuwarsa ne yacika cikin wannan parlon.

Sosai zuciyarta ke faman lugude kamar ana buga mata ganga,gashi kuma wani juyawan da kanta ke mata yana naiman ragargaza mata k'wak'walwarta wanda babu wanda yasan kalar azababben ciwon kan dake damunta a wannan lokacin sai ita kanta dakuma ubangiji da ya jarafceta dashi a dai-dai wannan lokacin...!

Cikin zuciyarta banda k'una babu abinda yake mata, jin yadda wannan yaron keta faman ambatar sunanta yasa ta bud'e manya manyan idanuwanta ta sauk'ar dashi akansa,inda idanuwansu suka sark'e cikin na junansu, wanda hakan yasa wannan yaron dat'sa ma mami(matar data rik'esa) cizo, babu shiri ta sake sa,sabida ba k'aramin shigarta cizon yayi ba,kasancewar anyi cizon ne cikin fushi dakuma fitar hayyaci.

Da gudunsa ya k'arasa inda ta take,ya fad'a jikinta ya k'ank'ameta yana sakin sabon kuka sosai ba kad'an ba, itama k'ara rungumesa tayi sosai cike da tausayin kanta dakuma shi karan kansa wannan yaron da saura iyayen nasu dake dake cikin palon.

" *NURAAZ* kana so Anty Hanan tayi fushi dakai ko?" Girgiza kansa ya somayi a jikinta har zuwa lokacin bai yi shuru ba sai kuka yake,wanda hakan kuma ba k'aramin sake dagula mata lissafi yake ba.
"To kuwa tabbas idan baka so Anty Hanan tayi fushi damu saika daina ihun nan da kakeyi! Ka tashi muje kayi alwala kayi sallar kana naima mata rahamar ubangiji a cikin addu'oinka!! Idan kuma kace ba za kayi ba, ba Anty Hanan kad'ai ba, ni kaina ba k'aramin fushi zanyi dakai ba,kuma nima zanbi Anty Hanan ta yadda bazaka k'ara kallona ba!" Janan ta k'are maganar cikin dan daure fuska,wanda kuma k'arfin hali sosai takeyi a wannan dogon maganar da tayi sabida yanayi na rashin dadi da zuciyarta ke ciki.

Kamar anyi ruwa an d'auke, haka nan kukan wannan yaron cak ya t'saya, hakan kuwa yasa mutane da dama jin salama cikin k'wak'walwarsu, kansa nakan k'irjinta,hannayensa kuma na zagaye da cikinta ya k'ank'ametaa sosai sai sauk'e ajiyar zuciya ya ke yi,amma har yanzu hawaye bai bar zuba daga cikin idanuwansa ba,cikin muryarsa data dishashe da kuka can k'asa-k'asa ya ce,"Aunty Janan na bar kukan, ki tashi muje to nayi alwala sai inyi ta mawa Anty Hanan addu'a idan dai baza tayi fushi dani ba,kuma kema bazakiyi fushi dani ba, ki tafi ki barni kamar yadda Anty Hanan tayi kinji...?" ya k'are maganar ya mai d'ago kansa fuskarsa a d'an shagwab'e m!
Ba tare da tace masa k'ala ba ta mik'e ta kamo hannunsa suka shige wani lungu dake manne da jikin parlon,mutane da dama suka bisu da kallon tausayawa na wannan rashin da sukayi...!

Sai da Mami taga shigewarsu janan wannan lungun data tabbatar zai sada su ne bedroom din *NURAAZ*  kamin ta sauk'e k'ak'k'arfar ajiya zuciya tana share wani siririn hawayen daya sak'k'o mata ...!
Takowa tayi cike da sanyin jiki kamar wacce k'wai ta fashewa a ciki zuwa gaban wannan matar da aketa faman bata hak'uri amma kamar k'ara zugata akeyi,dikta fice hayyacinta gwanin ban tausayi sai ambatar *Ni y'ata bata mutu ba* takeyi.
k'urama wannan matar ido Mami tayi tana kallonta cike da tausayinta...!

" *MAMMIn* yara yanzu wato kina nuna cewa kina ja da hukuncin ubangiji ne akan abinda yake da iko dashi ne ko kuwa me? Ko kina so kice min kinfi ubangiji sanin dai-dai akan Hanan d'inne da har zaki na ambatar cewa ke y'arki bata mutu ba? Ko kin manta da cewa *kulli nafsin za'ikatul maut...?*  Muma da kika ga har yanzu muna rayen bawai dan Allah yafi k'aunarmu akan Hanan d'in bane ya d'auketa a dai-dai wannan lokacin mu kuma muke rayuwa cikin duniyar? Ina iliminki? Ina saninki? Ina kuma tawakkalin dana san cewa ni y'ar uwata tana dashi? Ki duba ki gani yadda Nuraaz yake ta faman kuka,idan ke bakiyi shuru ba shin wanene zai lallashesa? Ko kuwa idan yaga ke kina kuka shin shikuma mai zayyi? Bakya tunanin wani kalar hali zamu iya shiga mu kuma idan wani abin yasameki ne? Addu'arki Hanan tafi buk'ata a dai-dai wannan gab'ar bawai kuka ba! Kinsan cewa wannan kururuwar da kikeyi kina k'arama Hanan nauyi ne? Addu'arki kuma tamkar kina yaye mata nauyine? Kiyi farin ciki yarinyarki mutuniyar kirki ce,tasamu kyakkyawan k'arshe da muma muke fatan musamu irin wannan k'arshen! Allah yajikan Hanan ,Allah yasa aljanna ce makomarta,mu kuma idan namu yazo allah yasa mu cika da imani."
Mami ta k'are maganar wasu hawaye na ci gaba da sauk'a daga cikin idanuwanta!
"Amin-amin." wannan shine ke ta faman fitowa daga bakunan mutanen dake wajen!
A hankali kukan Mammi yake t'sayawa har tasamu tayi controlling na kanta,sai dai kuma hawaye har yanzu na faman ci gaba da zubowa daga cikin idanunta,wanda kuma tana da yak'inin kota share hawayen saiya k'ara zubowa.

********

Alwala Janan tayi ma *Nuraaz* daya lanjare mata kamar zai fad'i, bayan sun fitoma basu fita can parlo ba,zama sukayi kan sallaya suna ta addu'oin nema wa Hanan gafara cikin kabarinta, a haka wani wahalallen bacci yayi gaba da *Nuraaz*, sai da Janan ta gyara masa kwanciyarsa kamin kwanta itama a gefensa tana zubar da wasu zazzafan hawayen tunanin abubuwa da dama dasuka shud'e dangane da rayuwarsu yake dawo mata daki-daki...!

*wasa farin girki🤼‍♀️*

_Wacece Anty Hanan?_
_Wacece Anty Janan?_
_Wacece Mami?_
_Wacece Mammi?_
_Wanene NURAAZ?_

Idan kukayi hak'uri kuna bibiye da alk'alamin Oum Mumtaz zan warware maku zare da abawa, sai dae kuma idan kin karanta kiyi k'ok'arin k'aramini k'arfin gwiwa ta hanyar bugamin sharhi akan dik page d'in dana turo, sannan kuma kiyi share nasa a dik novels group da kike ciki...!
y'an wattpad kuma ayi k'ok'ari a dangwalamin vote hilis😊

*✅ote*
*comment*
*share*
*follow me on wattpad@Oum-Mumtaz123 🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂️*

NURAAZ(treasure of noor)Where stories live. Discover now