shafi na sha bakwai

107 7 0
                                    

*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
       _(Treasure of noor)_

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

*_'''( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)️'''_*

*wattpad:UMMIE2018*
*MALLAKAR:oum mumtaz*

             *shafi na sha bakwai*

*******WASHE GARI*******

Gidan sun wuni wani sukuku sam babu armashi kamar baya...!ga jikin janan da yayi t'sanani,gakuma nuraaz dashima ya kwanta zazzab'i sosai jikinsa sai karkarwa yake sbd tension da yayi masa yawa...!

tin wajen k'arfe goma ma safe abba da abbi suka fice daga gidan batare da sunce masu ga inda zasu ba...!wanda hakan sosai yake sake dagulama nuraaz lissafi sbd ganin zayyi biyu babu...! babu janan d'in dayake sha'awarta kuma babu hanan d'in dayake k'auna...!

mammi ma a part na mommy ta wuni wurin jinyar ita janan d'in dake matik'ar jin jiki,babu zancen fita wurin aiki ballanta kuma zuwa makarantar su adnan d'in dik a gida suka wuni in banda suwa masallacin dasukeyi...!

sai yamma lilis kamin su abba suka dawo gida inda suka taho tare da inna zainaba da itama t'sufa yakamata sosai...!

a part d'in mammi ta sauk'a sai harara take aikama nuraaz dashima ke kwance kan d'aya daga cikin kujerun parlon ya dafe kansa dake barazanar  t'sagewa...! shikam baima san tanayi ba sbd abin dake gabansa yanxu ya wuce misali...!

abba ma ko kallon nuraaz beyi ba ballantana yaji tausayinsa na hukuncin dasuka yanke a yau d'in...!

wajen k'arfe tara da daren wannan ranar aka sake had'a meeting na cikin babban parlon part nasu abban nuraaz d'in...!mommy da mammi ne suka d'auko janan d'in bisa ga umarnin abba sbd itama ta halarci taron tinda sak'on dasuke son isarwa ya shafeta...!

inna zainaba ma na zaune kan kujera sai faman karkad'a k'afa take taci fuskar serious...!
mufy dasu ameen ma baki d'ayansu suna zaune bisa ga kan capet suna jiran sammaci...!

abbi ne ya bud'e taro da addu'a kamin abba yabud'e bakinsa cikin tamkewa yasha mur...!

"mufyda tashi kizo nan...!" yafad'a yana nuna mata gefensa wajen k'afafunsa...! aikuwa take zuciyarta yafara lugude sbd t'sananin razanar datayi na gudun mai zaije yadawo itakuma da aka ambaci sunanta a cikin abinda babu ruwanta...? cike da sanyin jiki ta rarrafo zuwa wurin da abba ya nuna mata ...!

wanda hakan yasa kowa dake cikin parlon baza kunnuwansa domin jin abinda abban yazo dashi...!

"SHIN KINA SON MUHAMMAD...? KUMA ZAKI IYA RAYUWAR AURE DASHI...?" abba ya tambayi mufy dake ta faman rarraba idanuwa a k'asa...!

bama mufy kad'ai ba...! hatta su adnan,hanan,janan dakuma su mammi saida sukaji zuciyarsu ta bada sautin ras...! sbd jin wannan tambayar da abban ya malmalo...!

a razane mufy ta d'ago kanta tana zazzare ido,a kuma lokaci d'aya tana girgiza kai har hawaye sun fara sauk'a bisa ga k'uncinta...!

cikin kwantar da murya abbi yace "ba girgiza kai zakiyi ba doter,ki bamu ansa shin kina sonsa kuma zaki iya rayuwar aure dashi...?

"NIKAM ABBI WALLAHI BAZAN IYA BA...! SBD YA NURAAZ MUGU NE...! BAYA K'AUNA TA KUMA HAR DUKANA YAKEYI KOBAN MASA KOMAI BA...!" mufy ta bada ansa jikinta na rawa,sbd itakam allah yana gani dik rashin kunyar datake ma nuraaz kawai k'arfin hali ne...!domin kuwa sosai take t'soronsa cikin zuciyarta ...!

cike da b'acin rai mommy tace "amma sai yau na tabbatar baki da k'unya wallahi mu......" abbi bai bari ta k'arasa ba ya d'aga mata hannu alamun baison jin komai daga gareta...!

NURAAZ(treasure of noor)Where stories live. Discover now