shafi na hud'u

165 12 0
                                    


*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
       _(Treasure of noor)_

*©️OUM MUMTAZ*

        *4*

******** Sosai dariya ya cika cikin Mammi na ganin yadda yaro k'arami kamar Nuraaz iya wasa da hankalin Auntyn nasa Janan da rashin lafiyar k'arya sbd zillewa hukuncinta, amma ta maze dikkuwa da kallo d'aya tayima fuskar Nuraaz d'in ta fahimci rashin lafiyar k'arya ce, kallonsu tayi da kyau fuska d'aure tace, "Abinda za'ayi yanzu bara naje na k'ira Abbanku a waya sai ya turo mana Doctor Salame tazo ta maka allura ta rubuta maka magunguna sabida bana son ciwon nan naka ya kwantar dakai gwanda a tare sa tin wuri, amma abinda za'ayi ku taso idan kaci abinci tukunna ko Babana?"

Wannan karon kam kukan gaske ya fashe dashi sosai yana girgiza kai yana had'e hannunsa alamun rok'o shi baya son allura, sabida shi a rayuwarsa wallahi ya t'sani dik wani abinda yashafi magani da allura kwata-kwata. Ficewa daga dakin Mammi tayi tana gimtse dariyarta, a ranta kuwa tana mamakin wayo kalar na Nuraaz.

Kallonsa Janan tayi cike da tausayinsa tace, "Ka tashi muje kaci abinci idan yaso sai na lallab'a Mammi kar a kira Doctor, sabida kasan nima bana so ana maka wannan allurar mai shegen zafin tinda nima ba so nake ba."

Bai yi musu ba kuwa ya mik'e yana yayyat'sina fuska takamo hannunsa suka fito inda suka tarda Mammi tafara cin abincinta, bata cika son zama kan dining ba,hakan yasa suma sukafi gane zama kan kafet suci abinci dan haka ta had'a masu a wani babban plate dikkansu uku, zama suka yi suma a wajen, Janan ta fara basa  abaki,shima sai wani shawagab'e mata yake ita kuwa tana biyesa,ko kallonsu Mammi ba tayi ba sabida takaicin sangarta kalar na Nuraaz ta fara is art a,shima kuwa da kad'an-kad'an har ya fara cin dayawa ya warware daga jinyar k'aryar tasa,sai da suka gama cin abincin,Janan ta kwashe komai takai kitchen itama ta dawo parlon taje ta kwanta a jikin Mammi kamar yadda Nuraaz ma ya kwanta ta gefe d'aya suna kallon film abinsu.

A haka Abba yashigo ya iskesu dawowarsu daga wajen d'aurin auren wata y'ar abokinsu shida Abbi, da sallama ya shigo suka ansa masa fuska a sake, Nuraaz ne yaje da gudunsa ya taro abban nasa yana masa oyoyo, ficewa Janan tayi bayan tayima Abban sannu da zuwa sun gaisa zuwa shashen iyayenta,sabida yau basu had'u ba kwata-kwata...!

Da sallam ta shigo shashin nasu,bataji an amsa mata sallamar tata ba,alamu ya nuna mata cewa suna ciki, dan haka ta shiga kitchen nasu ta tarda Umaima mai wanke-wanken Mamin nata tana sauk'e sanwar abinci daga kan gas, sa'ar su janan d'ince itama,gaisawa suka sosai sabida akoi kyakkyawar fahimtar juna t'sakaninsu da masu aiki a k'ark'ashin na su,saka hannu tayi a aikin girkin sukaci gaba da aikin nasu, anan ne Janan take jin ashema yau tun safe Mamin nata bata fito ba tana d'aki bata ji dadi ba, barin aikin tayi zuwa d'akin mahaifiyar tata.

Knocking tayi daga bakin k'ofa taji Abba ya bada umarnin shigowa, da sallama ta shigo tana maibin Mamin da kallon k'urilla, gefen Mamin ta zauna dake jingine daga jikin filo fuskarta tayi fayau alamun batajin dad'i k'arara ya bayyana,kamo hannayen Mamin tayi tana tattab'a jikinta kamar mai son gano wani abu.

"Ina wuni Abbi?" Fad'ar Janan tana mai maida hankalinta kan mahaifinnata da shima yake zaune a d'ayan gefen sunsa Mami a t'sakiya.
"Lafiya kalau uwata, fatan kun tashi lafiya?"

"Lafiya kalau Abbi! Mai yasami Mami Umaima tace min yau bata fito ba bata jin dad'i?"
Cikin fuskar damuwa ya ce,"Wallahi tin daren jiya ta kwanta da ciwon kai, so yau da safe nayi tunanin abin da d'an sauk'i amma kuma dawowarmu yanzu daga wurin d'aurin aure na tardata jikin ya mat'sa mata, ga dikkan alamu ma ko abinci bataci ba inaga.." Abbi ya k'are maganar yana mai fuskantar matar tasa cike da tausayawa.

Murmushin k'arfin hali Mami tayi tana mai shafa kan Janan d'in tace, "Kar ki damu kanki kinji mamana, jikin nawa ma ai da sauk'i yanzu, ina Mammin naku da Nuraaz? ina a fatan dik suna lafiya?"

Cikin damuwa Janan tace, "Dik lafiyansu kalau Mami, sai dai kuma Nuraaz d'inma yana d'an fama da zazzab'i yaud'in,amma kuma yaji sauk'i yanxu sabida har abinci nabasa yaci."
"Allah ya basa lafiya." Mami da Abbi suka fad'a lokaci d'aya cike da tausayin Nuraaz d'in.

Janan ce ta taimaka ma Mamin nata ta shirya cikin riga da zani na atamfa tasa mata hijjap bisa umarnin Abbi, shima yawuce d'akinsa ya wat'sa ruwa ya sako jallabiya suka fito zuwa harabar gida,Abbi yace taje ta k'ira masa Nuraaz d'inma.

A parlo ta tarda su suna kallo Nuraaz sai sangarta yake tayima abban nasu, sak'on Abbi janan ta fad'ama Nuraaz amma batace masa ga inda zasuje ba,dan haka ya tashi cike da d'auki yaje ya sako jallabiya shima kamar yadda yaga Abbin Janan nayi idan zaije wuri mara nisa.
Fatan a dawo lafiya su Mammi suka bisu dashi sannan suka fice.

Abbi ne yake driving,Mami da Janan a baya, sai Nuraaz a gefen mai zaman banza, take cikin Nuraaz ya kad'a ganin inda suka zo su ya fara mat'sar k'walla yana yarfe hannu, "Wallahi Allah na warke Abbi, ni dama lafiyata kalau wallahi, kawai inajin t'soro kar Aunty Janan ta dakeni ne yasa nace mata banda lafiya." Nuraaz yak'are maganar yana mai fashewa da kuka sosaiil na ganin sunma riga dasun shigo cikin asibitin.
sosai kuwa hakan yabama kowa dariya cikin motar,hatta ga Mami ma sai da ta d'an dara dik kuwa da yadda takeji rashin kuzarin jikinta, Janan kam itama abin yabata dariya sosai ba kad'an ba, bayan Abbi yayi parking na motar tasa a haraban asibitin *Dikko Special Hospital.*

Bayan awa daya.
Zaune Abbi da Mami suke gaban likita banda farin ciki babu abinda nake hangowa a fuskokinsu baki d'aya,sabida abinda likita ya shaida masu Mami na d'auke da juna biyu na t'sawon wata biyu,wanda hakan shine sanadiyyar wannan jinyace-jinyacen da take fama dashi.

Sosai suka yi farin ciki a wannan lokacin,sabida sufa already sun riga da sun gama cire rai da k'ara ganin k'wansu cikin duniya,saikuma gashi Allah ya nuna masu ikonsa (shiysa ake cewa mutum karya yanke k'auna da rahamar ubangiji).

Haka suka dawo masu Mammi da wannan kyakkyawar albishir d'in, kowa ka gani cikin gidan sosai yake cikin farin ciki yana fatan allah yasa a haifi mace su sami little Hanan da suka rasa babbar.
Su Nuraaz shima baki har kunne wai zai samu k'anwar da zatana k'iransa da Yaya tinda shima yana cema Janan Anty, hakan yasa sosai ake tattalin Mami kamar cikin fari,Nuraaz da Janan ma sun koma shashin mamin sun tare anbar mammi da kewa.
Inna Zainaba ma da kanta tazo gidan tanata farin cikin samun wannan k'aruwar da zasu samu cikin wannan gidan.

  Bayan wata bakwai

*✅ote*
*comment*
*share*
*follow me on wattpad@Oum-Mumtaz123🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂️*

NURAAZ(treasure of noor)Where stories live. Discover now