Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JQwSpMa3DmBDp85itUS0TM
*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
_(Treasure of noor)_*©OUM MUMTAZ*
*3*
********Yan uwa na naisa da suka zo masu ta'aziya dik an wat'se bayan anyi sadakar bakwai,gida ya rage su su kad'ai, sosai kuma suke cike da kewar Hanan dikda kasancewarta yarinya mara surutu sai sukaji gidan is quite different...!
Nuraaz ma yanzu ya koma shuru-shurun dole na k'arfi da yaji, gashi sam yanzu baya son cin abinci sai idan Janan tasaka shi a gaba tana basa a baki cike da lallashi kamin ya sama cikinsa abinci, shi a nasa yarintan gani yake kamar Hanan d'in zata dawo,dik kuwa da a islamiya malaminsu yace masu dik wanda ya rasu bazai sake dawowa ba...!Haka nan Janan ma sosai take cike da kewar y'ar uwarta, amma dole suka ta rungumi k'addara a kullum take bin sistern ta da fatan dacewa,wanda kuma hakan shine kad'ai gatan da zata yi mata Hanan d'in duniya da lahira bawai saka damuwa a zuciya da koke-koke ba,tinda dai sunsan cewa kulli nafsin za'ikatil ma'ut ne.
Mammi ma sosai ta rungumi k'addara tana bin y'arta da addu'a wanda muke fatan muma musamu masuyi manaa addu'ar bayan mun shud'e a doron k'asa, part d'insu Nuraaz Janan ta tare sabida d'ebema Mammi da Nuraaz kewa,kuma Alhamdulillah sosai ake samun progressing...!
*Bayan wata uku da rasuwar Hanan*
Zuwa wannan lokacin rayuwar gidan yana tafiya ne cike da t'sant'sar k'aunar junansu da kuma mutuntawa hadi da fahimtar juna, wanda zuwa lokacin kuma mutuwar Hanan tariga data gama sake masu zuciyoyinsu,sai dai idan antuno ta kuma a bita da addu'a cikin kabarinta.
Sosai Nuraaz ya zama miskilin k'arfi da yaji, dama kuma shi tin asali bashi da abokanai ko a makaranta dan haka yanzun ma shi kad'ai yake rayuwarsa sai kuma Antynsa Janan da kuma iyayensa sun ishesa,wanda idan ma kajisa na dogon surutu sosai sai da Janan.
Itama kuma sosai take k'ara sangartasa kamar wani jinjiri, abinci wannan wata rana idan y'an sakarcinsa suna kusa ita zata basa a baki yana zuba mata shagwab'a itama tana biyesa, sannan kuma wata rana idan yayi wanka sai ya zauna gaban mirrow na d'akinsa yak'i saka shafaa mai ballanta kuma saka kaya wai sai Janan ce zata masa, itama kuwa cike da tausayin k'anin nata zata shafa masa mai tasa masa kaya sabida kaunar da take masa. Su Mammi sosai sukejin dad'in ganin kalar shak'uwar dake t'sakanin Janan da Nuraaz.
******** K'wab'e fuska sosai Nuraaz da kansa ke kan cinyar Janan yayi yana kallon farar fuskarta dake cike da walwala tana sakin murmushi, alamu dai wani abu mai mahimmanci da yake sata farin cikin takeyi a cikin wayarta da gaba d'aya attention nata na kan wayan...!
"Anty Janan. "
"Anty Jaanannn! !"Banza Janan ta masa kamar bata jisa ba taci gaba da chart d'inda takeyi da sabon saurayin da tayi, wanda suka had'u a wani group na whatsapp satin daya gabata, ganin tak'i kulasa yasa shi tashi zaune yanata kallon fuskarta yadda take ta faman doka murmushi kamar wacce akayiwa albishir.
Mat'sowa yayi sosai kamar zai shige cikinta ya k'ara narke mata a jikinta ya rungumeta ta gefe yana lek'a kansa domin ganin da wanda take chart ta manna masa bajin hauka har haka *My Love* shine sunan daya gani b'aro-b'aro, wani haushi ne ya kama sa sosai, wato Aunty Janan dan ta samu wani shine yana ta mata magana ko? B'ata fuska yayi sosai ya zare jikinsa daga nata yanata faman yat'sina fuska yana tunanin abinda zai mata don ya huce haushinsa. Janan kam soyayya tayi dad'i sosai da *Ahmad* dinta! bata ma san dik wainar da Nuraaz ke toya wa ba,sabida yadda gaba d'aya hankalinta ya ta'allaka akan chart d'in da take.
Mik'ewa yayi sosai ya saita hanyar d'akinsa kamin ya daddage ya fisge wayar daga hannunta ya kwaso a guje zuwa d'akinsa ya banko k'ofar ya danna key ta ciki yana ta wani cika yana bat'sewa.Janan kam tin a lokacin daya fuske wayar taa d'ago a fusace da niyar sauk'e masa kwandon bala'i amma tini ya baima wandonsa iska,sai k'urar b'acewarsa data gani, mik'ewa tayi a fusace taje k'ofar d'akinnasa ta tura taji ya rufe k'ofar, cike da masifarta data kwan biyu batayi ba tafara kiransa kan yazo ya bud'e mata k'ofa ya bata wayarta sai faman bubbuga k'ofar take kamar Allah ne ya aiko ta amma yayi biris da ita, sai ma zamansa da yayi bakin gadon ya shiga kan sunan Ahmad d'in da tayi saving da My Love ya fara karanta chart nasu yana ta wani b'ab'b'ata fuska kamar wanda aka sa dole sai ya karanta.
Kalamai ne sosai na soyayya da dik macen da namiji yayi mata hakan sai ta dinga jin kanta huruwa a cikin gajimare,ballantana kuma kalarsu Janan da dama neman masu girmamasu suke ruwa a jallo kuma sai suka samu cikin ruwan sanyi, ba komai ne k'wak'walwar Nuraaz ke fahimta ba, amma haka nan yakejin mugun haushin Ahmad ya samu mat'suguni cikin zuciyarsa.Mammi ce ta fito daga can d'akinta sabida jin kalar bugun k'ofar da janan take yi alamun ba lafiya ba, "Janan lafiya kuwa kike ta faman buga k'ofa haka nan? "
Mat'sar k'walla Janan tafara kamar wata k'aramar yarinya,aikuwa sosai ta fashema mammi da kuka kamar wacce akayiwa wani abu, cike da damuwa Mammi ta kamo hannunta tana lallashinta itakuma sai k'ara bot'sarewa take a jikin Mammi kan abinda Nuraaz ya mata wai yafara rainata dayawa!
Murmushi kawai Mammi tayi tana mamakin son girma kalar na Janan, ga ta dai a haka idan aka ganta sai ayi tunanin kalar y'ar 15yrs d'innan ne, wanda kuma da za'a bama Nuraaz good five years a gaba tabbas shine zai k'wace wannan girman,kasancewarsa kamar kazan agric haka nan Nuraaz yake kumbure.
Mammi ce tafara k'iran Nuraaz kan ya bud'e k'ofar, amman bai kulasu ba sai da ya gama karance-karancensa t'saf kamin ya mik'e yaje ya bud'e k'ofar. Wanda kuma zuwa lokacin Janan ta jima da shiga kitchen tare da Mammi suna hiransu gwanin sha'awa.
Sanin da yayi cewa Janan a cike take da shi yasa shi komawa cikin bargo bayan kashe ac,dik kuwa da kalar zafin da akeyi.Sosai ya lanjare kamar mara lafiyan gaske sai wani fidda numfarfashi yakeyi yana mak'yark'yata...!
Bayan Janan sun gama girkinsu,sun tattara komai sun barma mai aikin kayan wanke-wanke Mammi ta wuce d'akinta, itama Janan ta wuce d'akinta daya kasance d'akinsu ita da marigayiya a baya, da yake suna da d'aki anan sannan suna dashi a can,dik inda suke so nan suke kwana, wanka ta fara yi kamin tayi sallar azahar sabida jin an k'ira salla, doguwar riga ce a jikinta mai gajeren hannu kalar ja da rat'sin bak'i a jiki na roba, sosai yabi lafiyayyar farar fatarta sai wani glowing takeyi dik da ma dai batayi wata kwalliya idan aka dauke man da ta shafa, hula tasaka akanta kamin ta d'aure fuska tamau kamar bata tab'a dariya ba ta fice ta doshi d'akin Nuraaz ta kuma samu k'ofar a bud'e, tana shiga wayarta dake ta faman haske alamun k'ira na shigowa tafara gani, cikin hanzari ta k'arasa wajen wayar taga my love ne ke k'ira, ba tayi k'asa a gwiwa ba wajen yin recieving. Ajiyar zuciya mai k'arfi suka sauk'e kusan lokaci daya d'aga daga ita har ahmed d'in.
Ga dikkan alamu dai hak'uri ake bama masoyi sabida naga yadda take ta faman b'ata fuska tana murmur da baki, minti takwas ta d'auke su suka gama wayar,bayan ta kashe wayar ta juyo a harzuk'e da niyyar ta fara sauk'e masa kwandon bala'i...!Zaro ido tayi na ganin yadda fuskar Nuraaz d'in keta faman t'sat'safo gumi kamar an t'samosa daga ruwan zafi, idanuwansa sai wani luluuu sukeyi kalar na masu rashin lafiya dasuke jin jiki, a kid'ime tayi wurgi da wayar tata ta haye kan gadon ta yaye babban bargo daya lullub'e daga wuyansa har zuwa k'afafuwa, kansa ne kawai a waje, jikinta ne kata faman rawa ta gagara magana ma ta d'agosa,aikuwa take ya k'ara sake jikinsa kamar wanda ake control da remote ya zube jikinta,ya k'ank'ameta sai faman mazari jikinsa yake wai ala dole sanyi yakeji.
"Nuraaz ma...mmai... yasame……ka...ne?" Janan tayi maganar cike sark'ewar harshe, k'ara k'ank'ameta yayi da kyau cikin yaudararriyar murya ya ce, "An……t…y Jannnann kaina..." Yayi maganar yana k'ara tusa kanshi ajikinta,ga dariya dake neman fito masa amma dole ya t'sare sabida yasan idan ba haka ya mata ba duka yau kamar ya gama sha ne.
"Wayyo Allah na, am sorry kaji k'anina...? Bari naje wajen Mammi na kawo maka magani..." D'an duniya,gudun karta kawo masa magani sabida yasan kalau yake ya k'ara kwab'e fuska yana mat'sar k'walla wai karta tafi tabarsa.
Haka nan Janan ta biyesa sosai a wannan lokacin,tuni na ta manta da wani Ahmad ballanta kuma laifin da Nuraaz d'in yamata sai lallab'asa takeyi.
Bayan Mammi ta idar sallah ta fito parlo da niyyar suyi lunch sai tabaga Janan ba,hakan yasa ta wuce d'akinta nanma bata nan, dan haka sai ta wuce d'akin Nuraaz sabida tana kyautata zaton tana can.*✅ote*
*comment*
*share*
*follow me on wattpad OUM-Mumtaz123🚴🏻♂️🚴🏻♂️🚴🏻♂️*