*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
_(Treasure of noor)_*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_'''( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)️'''_*
*wattpad:UMMIE2018*
*MALLAKAR:oum mumtaz**shafi na sha biyar*
******* abba ne yafara jawabi kamar haka bayan yayi masu sallama kamar yadda manzon allah ya koyar damu yace "wannan taron badan kowa akayishi ba sai don sbd nuraaz...!
shekaranjiya yazo ya sameni da wani batu da ni a lokacin nayi tunanin shirme ce kawai take yawo akansa ko kuma ince t'saurin ido...!
amma kuma daga baya mun zauna da shi deen dakuma mommyn ku mun yanke wani hukunci batare da sanin ita mammin naku ba dakuma ku kanku baki d'aya...!
kazo kasameni akan kana son kayi aure haka ne ko ...?" abba ya yanke maganar tasa yana mai fuskantar nuraaz d'in da kansa ke k'asa zuciyarsa sai faman dokawa yakeyi...!
dak'yar yasamu ya had'e wani yawu mai kauri dayayi masa t'saye a mak'oshi yace "hakane abba"
da mamaki mammi ke bin nuraaz d'in da kallon t'sant'sar mamaki da alajabi...! bata samu zarafin magana ba muryar abba ya k'ara karad'e cikin parlon yace " *kacemin k'anwarka hanan kake so ka aura haka ne...?*"
abba ya sakeyin maganar da sigar tambaya...! a wani mugun gigice nuraaz ya d'ago kansa ya kalli inda janan ke zaune...! karaf kuwa suka had'a idanuwa da itama take masa wani kalar kallon daya gaza gane fahimtar na minene sbd shiga rud'u...!
jikinsa na t'suma yamaida akalar kallon nasa izuwa fuskar hanan da itama take kallonsa kamar sabon halitta...!dikda kasancewarta yarinya mai k'arancin shekaru kuma marasa son hayaniya amma kuma tasan mai kalmar aure take nufi t'saf...!
wani mat'siyacin kallo ta wat'sa masa idanunta na cikowa da k'walla na bak'in cikin abinda yace wai zai aureta...! wato ma sunje sun gama abinda zasuyi da anty janan shine zai lallab'o wajen abba ya wani ce zai aureta ko...? to kuwa lallai za'ayi gagarumin yak'i idan akace za'a aura mata wannan kwarton...!🙊
kallonsa ya mayar kan fuskar mammi daya hango wani kalar tashin hankali a fuskarta da bai tab'a experiancing tare da ita ba...!
ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauk'e cikin sanyin murya yace *hakane abba*...!
murmushin manya abba yayi cikin kakkausar murya yace " *yaya mukayi dakai kuma a wannan lokacin...?*"
tiryan tiryan nuraaz ya zayyane masu dik yadda sukayi da abba a wannan ranar,yanayi yana satar kallon fuskar janan da ita kuma take kallon nuraaz d'in idanunta sun kad'a sunyi jazur dasu...!
shuru parlon ya d'auka na t'sawon lokaci,kamin abba ya nisa yace "toh yanxu hak'uri nake so na baka a mat'sayina na mahaifinka...!kayi hak'uri da zancen aurenka da ita hanan d'in har sai ta cika shekaru goma sha biyar a duniya...! kaga zuwa wannan lokacin ta k'ara wayo ta kuma san ciwon kanta yaso sai a maku auren amma a yanxu kam gaskiya bazaka samu hanan d'in ba...! kuma nayi maka alk'awari insha allah indai ina raye a doron duniya da yaddar ubangiji zan aura maka ita kaji babana...?"
abba ya k'are maganar tasa cike da tausasa murya ...! k'asa nuraaz yayi da kansa yanajin wani tuk'uk'in bak'in cikin hanasa hanan d'in da akayi a daidai lokacib dayake buk'atar ta cikin rayuwarsa...!
*ABBA NIKAM WALLAHI BANA SONSA KUMA BAZAN AURE SA BA...!* hanan ce tayi wannan maganar cike k'araji da kuma muryar kuka...! da wani mad'aukacin mamaki kowa ke kallon hanan d'in a cikin parlon sbd jin kalaman da tayi...!
wani mari mai rai da lafiya abbi da tin d'azu bayyi magana ba ya d'auke fiskar hanan d'in da saida taga wani haske ya gilma mata...! take jinta da ganinta ya d'auke na wucin gadi sbd yadda wannan marin ya ziyarci kwanyarta...!
abbi na da niyyar sake d'aura mata wani marin abba yayi gaggawar tare hannunsa yajasa gefe cike da masifa yake cewa "mai yasa zaka sa hannu ka daketa...? ai ba itace abin duka ba sbd bakasan dalilinta na cewa bazata aure sa ba...! waya sani ma ko wani aiki mara kyau yake aikatawa a b'oye ba tare da saninmh ba amma ita tasani...? kaima kuma shaida ne akan halin wannan yarinyar a cikin gidannan bata da hayaniya ko kad'an...! dan haka kabi komai a hankali saimu warware zare da abawa ba wai da zafin zuciya ba..."abba ya k'are maganar yana sauk'e numfarfashi...! zama abbi yayi bayan ya zame hannunsa daga na abba ya dafe kansa dake barazanar sara masa sbd b'acin ran abinda hanan d'in tayi yau,dikdama baisan dalilinta nayin hakan ba amma ko mutuwa najin kunyar idon uwa ballanta kuma d'an adam...!
nuraaz kam sosai yaji wani mugun tashin hankali sbd jin furucin hanan nacewa bazata aure sa ba kuma bata sonsa...!
mufy kam tin d'azu tana zaune kallon kowa kawai takeyi d'aya bayan d'aya batare da tace k'ala ba,saida taga marin da abbi ya sauk'ema hanan d'in ta mik'e a gigice ta yi wajen ta d'agota dak'yar itama hawaye na zuba a idanuwanta...!
saida kowa yasake samun natsuwa kamin abba ya dubi da hanan d'in fuskar shi sake cike da lallama yace "mamana fad'amin idan akoi abinda yayan naki yakeyi daya sa bakya son aurensa kuma bakya son sa...?" faskareriyar wayar dake kan cinyar mufyda ta d'auka tayi unlocking na passward d'in wayar tashiga app na valt da ita kad'ai tasan pin na wajen,ko mufy da wayar mallakinta ne bata sani ba...!
wajen vedio ta shiga batare da tayi ma kowa magana ba haka nan babu wanda yace mata k'ala sai kallonta da ido kawai da takeyi...!
mik'ama abba wayar tayi...! takumayi k'asa da kanta fuskarta tayi rud'u rud'u sbd marin da abba yayi mata...!
a wani mugun gigice abba ya mik'e t'saye jikinsa har kyarma yakeyi sbd abinda idanuwansa ke gane masa...! dab'as ya koma ya zube a k'asa wayar ma kad'an ya rage bai fad'i ba abbi yayi nasarar cafke wayar a hannunsa...! abinda idanunsa ke gane masa ya zarce tunaninsa kwarai da gaske...! wani kalar cilli yayi da wayar ta bugi jikin gini take kuwa wayar tayi kwat'sa kwat'sa da ita acikin wannan parlon...!
idan kuka ga abba da abbi saiku rasa wanene yafi wani shiga rud'u da tashin hankali t'sakaninsu...!
janan ma mik'ewa tayi ta doshi inda nuraaz keta faman ware idanuwa cike da rashin gaskiya tafara wawwanka nasa mari mai raida lafiya tana cewa allah ya isanta ya cuceta...! hanan da mufy kuwa suna jikin mommy dake ta faman lallashinsu sbd kukan da sukeyi...!
*BAZAI YUBA A HAD'A AUREN NURAAZ DA KUMA HANAN D'IN DA KUKE SO...! SBD SUN SHA NONO D'AYA*
sukaji muryar mammi ya karad'e cikin parlon da wani kalar sauti mai nuni da tashin hankali...! cilli nuraaz yayi da janan d'in gefe a wani mugun firgice ya k'arasa ga mahaifiyar tasa ya fara jijjiga yana kuka sosai "dan allah kicemin kunne na ne ke jiyemin wannan maganar a mafarki bawai da gaske ba mammi...!idan ban auri hanan ba zan mutu...!" haka nuraaz keta faman jijjiga mammi cikin fitar hayyaci itama tana kuka sosai...!
mommy ce ta shiga t'sakanin mammi da nuraaz d'in ta janyesa da k'arfin gaske ta sauk'e masa lafiyayyen mari mai rai da lafiya...!
*✅ote*
*comment*
*share*
*follow me on wattpad@ummie2018🚴🏻♂️🚴🏻♂️🚴🏻♂️*