https://chat.whatsapp.com/Cpp26Qt6krcEoPwkPVohE6*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
_(Treasure of noor)_*©OUM MUMTAZ*
*7*
********Bayan Nuzaaz yayi wanka ya shirya cikin riga da wandonsa na shan iska ya fesa daddad'an turarensa da Abba ya saya masa, Dr Salame tana sallama da su Inna sai ga su Abba sun shigo da sallamarsu, har k'asa Dr ta t'sugana ta gaishe su ta kuma yi masu ta'aziyan rashin da suka yi inda har saida idanuwan Abbi ya ciko da k'walla da aka tuno masa da marigayiyar matar tasa.
Mammi ta bada chaculate dasu sweet masu yawa tace akaima mufyda t'saraba,bayan sun dawo daga rakiyar tata Janan ta zuboma nuraaz abinci tawuce d'akinsa na ganin har yanxu bai fito ba, nanma saida tamasa jan ido kamin ya yadda da cin abincin sabida har yanzu halin nasa bai canza ba na k'in cin abinci sai sangarta yake zuba mata tana riritashi.Tare suka fito inda suka tarda Inna Zainaba ,Mammi ,Abba da kuma Abbi sai 3ples da suke ta kwarafniyarsu, a gefe Hanan k'arama kuma tana baccinta ajikin Mammi wanda ba ta jima da yi ba, bayan sun zauna Nuzaaz ya gaida iyayen nasa yana cewa shi bazai koma ba.
"Mammi nikam ina mami naga kowa da kowa amma tinda nadawo banganta ba? Kuma dazan shiga part d'inta d'azu damuka shigo Lamid'o driver yacemin wai tana nan."
Nuzaaz ne yayi wannan tambayar yana maibin iyayen nasa da kallo. Kowa shuru yayi a wurin aka rasa wanda zai fad'a masa sabida gudun boren da shima zai masu amma kuma yazama dole yasan d'acin mutuwa tin a wannan shekarun nasa bawai ace sai ya girma ba sabida basu san kuma inda rayuwa za ta sake wulla su ba.Ba tare da Janan ta jira an basa ansa ba ta mik'e da gudunta har tana tuntub'e ta shige d'akinta tana sakin siririn kuka na rashin mahaifiyar tata da take iya k'ok'arinta na ganin ta danne, bin bayan janan nuraaz yayi da kallo na ganin tana kuka sai yaji hankalinsa ya tashi, ya mik'e da niyyar bin bayanta Abba ya dawo dashi ya zaunar dashi yamasa bayanin yadda k'wak'walwarsa zata iya d'auka a dai-dai wannan shekarun nasa.
Ai kuwa sunga tashin hankali sosai a wannan ranar fiye da tunanin mai karatu,k'arshe ma sai Janan d'ince ta zamana mai lallashinsa haka nan yasake dawowa so silent a gidan,sosai yakejin t'soron sake rasa waninsu cikin wannan gidan nasu hakan yasa yake sake shige masu sosai kuma shi ya tub'ure kan shi wlhi bazai koma wannan makarantar ba tinda gashi har Mami ta rasu aka rasa mai zuwa yaje ya dauko sa, babu yadda suka iya haka nan Inna Zainaba da har yanxu bata koma ba tace acanza masa makarantar sabida basusan dalilin dayace baya so ba,kuma yakamata ace idan kuka ga yaronku na k'in zuwa wani ko makaranta da makamantansu karku tak'ura masu domin kuwa ba kusan illar da hakan zai iya jawo maku ba.A lokacin da suka cik sati ukun na hutun nasu tare da taimakon Abbin aka sama masa wata private school na jeka kadawo wato day school, sosai kuwa hakan ya masa dad'i,3ples ma kuma yanzu sun k'ara wayo abinsu sunyi b'ulb'ul dasu har gwarancinsu suna kwab'awa na magana.
An d'aura auren Dr Salame da kuma Abbi, wanda kuma hakan ba aikin kowa bane saina Inna Zainaba wanda zuwa yanzu itama takoma zaria abinta.
Mufyda y'ar Dr har yanxu ba tazo wannan gidan ba sabida har yanzu tana gidan yayan babanta acan jalingo kenan wai saita gama primary school zata dawo wajen mmnta da zama.Aunty Janan ma karatu ne akeyi gadan-gadan babu kama hannun yaro,soyayyarta da kuma Ahmad sosai tayi nisa,sabida iyayennsu ma yanzu sunsan da maganar dan haka akoi alk'awarin aurensu amma sai nan da ta gama jami'arta tukunna!
Sosai fahimtar juna da kuma girmamawa ta karu cikin wannan familyn abin dai sa wanda yagani kawai.*after 10yrs*
*✅ote*
*comment*
*share*
*follow me on wattpad@Oum-Mumtaz123🚴🏻♂️🚴🏻♂️🚴🏻♂️*