https://chat.whatsapp.com/Ki13Qiqky2fDiLssIjEjC7
*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
_(Treasure of noor)_*©OUM MUMTAZ*
*2*
*Asalinsu*
Mallam Muhammad Sani,babban Malami ne dake koyarwa a jami'ar *Ahmadu Bello University Zaria(ABU),* d'an asalin Nasarawa State ne cikin k'auyen y'ar kad'd'e, yana da matar aure d'aya tare da yaransu su guda biyu mace da namiji *Abubukar* da *Yahanasu*.
Abubakar ne babba, sai kuma k'anwarsa Yananasu, sun taso ne cikin rufin asirin Allah wanda sukan samun komai a wadace daga mahaifinsu, har yasamu gurbin lecturer a fannin islamic a wancan lokacin a can Zaria, hakan yasa suka tarkata kwamut'sansu suka bar garin Nasarawa zuwa cikin garin Zaria da zama, inda yasamu mahalli a d'aya daga cikin gidajen gomnati dake cikin makarantar.
Anan aka saka Yahanasu da Abubukar makaranta, shi ya fara daga ss2 ita kuma jjs 1, inda ta had'u da wata yarinya a makarantar mai suna *Hindatu*, tasu tazo d'aya sosai dikdama halin nasu ba d'aya bane, kasancewar ita Yahanasu tana da fad'a sosai bata ganin abu ta k'yale koda ba'a sakata ciki ba ballantana kuma an cillota cikin zance,wanda hakan yasa babu mai kawo mata wargi daga maza har matan da suke rayuwa dasu cikin makarantar tasu. Hindatu kuma ta kasance yarinya ce shuru-shuru, koda kuwa zaka kwana kana dungure mata kai ba lallai ne ta d'aga ido ta kalle ka ba,ballantana kuma ta tanka maka, hakan yasa sosai wasu daga cikin k'awayennasu sukafi mata iya shege sai dai kuma muddin Yahanasu na guri babu wanda ya isa ya taka mata k'awa ta k'yale sai ta dauki mataki.
Abubakar kuma shima ba k'aramin masifaffe bane na bugawa a jarida dakuma t'sant'sar son a girmamasa akan komai, shi a rayuwarsa kawai idan yace maka A karkace masa B,idan kuwa ba haka ba dik yadda kuke dashi bazai hana ya wanke ka ras soso da sabulu ba, hakan yasa shi sam bashi da abokanai sai mutum d'aya dayake shanye halin abokin nasa dashima a makarantar tasu suka had'u shima d'an asalin cikin garin zaria ne mai suna *Zahradden*
..*Bayan wani lokaci*
Sosai zumunci mai k'arfi ya shiga t'sakanin iyayen su Yahanasu ,Hindatu da kuma shi Zahradeen babu kama hannun yaro dik a sanadiyyar abotan y'ay'ansu. A lokacin kuma sosai t'safta tacciyar soyayya ta wanzu t'sakanin Yahanasu da kuma Zahradden, sai kuma Abubakar da Hindatu, wanda hakan sosai yayima iyayensu dad'i sosai ba kad'an ba.
Iya secondry school Hindatu da Yahanasu suka t'saya, su kuwa su Deen har degree na farko dana biyu saida sukayi shi,kuma Alhamdulillah sun samu aiki a hannunsu can jami'ar Kaduna b'angaren Business Administration. Hakan yasa bayan an gama shagulgulan biki suka tarkata matansu zuwa can garin Kaduna wanda acan suka dank'ara masu yalwataccen gininsu dai-dai gwargwadon iyawarsu.
Gidan ma idan zaka shigesa gate d'in guda d'aya ne,sai yazama kawai shashin nasu suka raba kowa danasa a unguwar *Kabala doki.*Sun fara yin lecturing nasu cikin kwanciyar hankali da kuma samun nasarori sosai, ba tare da sanin kowa ba suka fara bud'e wani madaidaicin shago a can garin kano cikin kasuwar wambai suna sarin takalmi dasu belt suka saka wani amintaccen abokinsu yake kula masu dashi sabida shi acan yake tare da iyayensu.
K'aramar kasuwanci ta zama babba, a cikin shekara biyu da auren nasu sosai suka tara kud'i bana wasa ba,sabida har girman shagon nasu saida suka k'ara bunk'asa shi, sai a wannan lokacin suka sanar ma da iyayen nasu akayi ta k'ara k'arfafa masu gwiwar naiman na kansu, rashin haihuwar da matansu basuyi ba abin na damunsu sosai, amma kuma ko a fuska basu nuna hakan ba sukaci gaba da mik'a kukansu zuwa ga Allah mai kowa mai komai da ya basu y'ay'a masu albarka dazasu zama wani abu kan addinin Allah, wanda har umra suka biyama su baki d'ayansu hud'u suka tafi sukayi ta rok'on Allah.