https://chat.whatsapp.com/Cpp26Qt6krcEoPwkPVohE6
*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
_(Treasure of noor)_*©OUM MUMTAZ*
*8*
******** *After 10yrs*
*Barau Dikko Special Hospital*
Wata matashiyar budurwa na hango cikin wani faffad'an office mai cike da tarkacen files akan table d'in dake gabanta, farace tas mai sirkin yello wanda hakan ba k'aramin sake fito da kyawunta yayi ba, idanuwanta b'oye suke cikin wani farin glass mai k'ara kuzarin ido (medicated).
Sannan kuma tana sanye da rigar likitoci ne shima fari tas dashi da yasha guga yana shining.
A shekaru haihuwa bazata gaza shekaru 28 ba, amma kuma dik wanda baisanta ba tabbas sai yace bata wuce irin 22 d'innan ba,sbd zallar k'uriyace mararan zaka hango tattare da ita.Wasu files take cikewa,fuskarta had'e take kamar hadarin gabas,alamun ranta yakai mak'ura wajen b'aci, ji tayi ana mata knocking daga bakin office d'in nata,hakan yasa ta dakatawa daga abinda takeyi tana mai maida hankalinta zuwa bakin k'ofar domin ganin wanda ya shigo.
Wani matashin saurayi ne ya shigo,cike da ladabi bayan ta basa izinin shigowa,sanye yake cikin kayan messengers alamu dai ya nuna d'an aikene shima, "Allah ya taimakeki *Dr Juwairiyya,* Allah ya huci zuciyarki, wallahi Doctor naje na duba office nasa kwata-kwata ban samesa ba, dazu da ya shigo kuma bansan mai yake damunsa ba sabida naga alamun yau yana cikin t'sananin damuwa da ban tab'a ganin yayi hakan ba."
"Will u keep that your stupit mouth shut-up? Ina ruwana da abinda yake damunsa tambayarka nayi? Ko bashi da hankali ne? So yake a zage mu ace bama aiki yadda yakamata? Ba sau d'aya ba! Ba sau biyu ba yake tafka wannan babban kuskuren waishi baya son stress na aiki? idan yasan bazai iya ba tin farko ai baikamata yafara ba! Gashi nan,saiya zuba ruwa a k'asa yasha Allah yayima matar dayak'i t'sayawa ya dubata rasuwa, dan haka nidai babu ruwa na yaje can ya k'arata tinda ya raina mutane shima yanzu yanajin yakawo kai..."
Janan ta k'are maganar tata cike da masifa dajin haushin *NURAAZ* na wannan sakacin nasa da yake yi cikin asibitin.Shidai wannan d'an aiken banda hak'uri babu abinda yake bata itakuma tana ta kumfar baki tana tattare wasu important files na marasa lafiya, sai da ta gama had'e komai t'saf kamin ta mik'awa Isiyaku tace ya kaima Dr Aryan, ita kuma ta had'e dik wasu kwamut'santa tafito cikin kuzarinta daga office.
Dik wanda ta had'u dasu sai sun gaisheta cike da girmamawa amma ko kallonsu yau ba tayi ba kamar yadda tasaba saima wani hararar mutane da take yi kamar su suka b'ata mata rai, a 360 tayi waje da motarta k'irar ferari 2020 daga cikin asibitin aka bita da addu'ar a sauk'a lafiya, sabida wulak'anta mutane sam ba d'abi'arta bace ko kuma kyaliya,mutane da dama sun tabbatar wani abu ne ya b'atama Dr nasu rai yau, cikin k'ank'anin lokaci ta k'araso unguwar malali dake cikin garin Kaduna, k'ofar wani tangamemen gida take zuba horn babu k'ak'k'autawa, a 360 wani magidancin mutumi ya lek'o ta hujin k'ofa domin ganin wanda yake zuba uban horn haka, bai b'ata lokaci ba wajen wangale mata gate d'in gidan ta danno motartata da uban gudu kamar zata bangaje mai gadin,shi kuma ai bayyi k'asa a gwiwa ba wajen kauce mata gudun karyayiwa hurera mai d'akinsa asara.
Parking space tayi parking na motarta, babban gidane sosai mai d'auke da part manya manya guda biyar,
Guda uku na daga gefe d'aya komai kalarsu d'aya babu bambanci, sai kuma wasu guda biyu suma da suke jere wuri d'aya ,amma basukai way'ancan ukun girma ba...!Cikin sassarfa ta fara tafiwa tana dosan d'aya daga cikin part guda biyu dake jere da junansu, tin daga bakin k'ofa tafara doka sallama tana kwanama Mammi k'ira kamar ita ta rad'a mata sunan, shigowarta cikin parlon ta tadda wata dattijuwa da zatakai 45 yrs tare da wasu yara mata guda biyu, d'ayar fara ce sosai ta gaban misali kamar ka tab'ata jini ya fito shekarunta na haihuwa goma sha hud'u, d'ayar kuma black beauty ce amma kuwa kyakkyawa sosai bakad'an ba sannan shekarunta goma sha d'aya ne amma idan kaganta a haka ta kusan kamo wannan y'ar 14yrs d'in girman jiki.
Dik kallon Auntyn nasu Janan suke da sai babbaka masifa takeyi tana fad'ama Mammi abinda Nuraaz yayi a wurin aiki idanuwanta har cikowa da k'walla suke yi,Mammi sai lallaab'ata takeyi tana bot'sarewa kan ita wlhi yau saita zane Nuraaz a cikin gidannan idan ba haka ba kuwa babu zaman lafiya.
D'aya daga cikin yaran ne ta kwashe da dariya sosai tana nuna Janan da hannu irin na rainin wayonnan! A fusace Janan tayi kanta da niyar maketa yarinya kuwa ta zille ta bayan Mammi tanaci gaba da dariyarta babu k'ak'k'autawa, "Yanzu ke t'sakani da Allah Aunty Janan ko bulala aka baki akace ki daki Ya Nuraaz sai ki dakesa? Bacin kinsa wallahi a yanzun loma d'aya idan yayi dake babu wanda zai k'ara jin d'uriyarki cikin gidannan? Wallahi ina mai baki shawara karma ki fara domin kuwa idan Ya Nuraaz ya tashi nuna maki kalarsa a cikin gidannan babu ruwan Mufyda." Tana gama maganarta kuwa ta kwasa da gudu zuwa d'akin Mammi tasa key ta ciki,sabida tasan ba k'aramin aikin Janan bane yanzu tazo ta mammaketa ita kuwa ba ta shirya ba...!
A can parlo kuwa sosai Janan take ta babatu kan yau wallahi kar wanda ya bata hak'uri sai tayi maganin Nuraaz da Mufyda a cikin gidannan, Mammi kam da shike bayau tasaba ganin hakan ba saita zubama sarautar Allah ido a ranta tana fadin sunfi kusa za ma su shirya!
Hanan da tin d'azu batayi ma kowa magana ba kuma an cika mata kunne da hayaniya yasa mik'ewa cikin yanayinta na sanyi ba tare da ta kalli Mammi ko Janan ba tazo wucewa ta gefen janan d'in zata shige d'akinsu,wani shegen rankwashi Janan ta sakarma Hanan a t'sakar kai na ganin yanda zata wuce ta kusa da ita ba tayi mata sannu da zuwa ba, Sosai kuwa yayima Hanan zafi amma ko a fuska bata nuna ba dikda k'arancin shekarunta ballanta ta t'saya tayi shigewarta d'akinsu dake mak'ale da parlon sabida lokacin sallar magriba ta gabato!
Harara Mammi ta wat'sama Janan wanda hakan yasa ta zumburo baki gaba ta kwashi jakarta tayi cikin d'akinta dake shashin Mammi itama domin ta rage kayan jikinta itama ta gabatar da sallah...!
8:00pm
Abbi ,Abba ,Ameen da Adnan ne suka shigo cikin gidan a lokacin dawowarsu daga masallaci na sallar isha'i, idan kukaga Ameen da Adnan ba za ku tab'a cewa sune way'annan yara y'an 11yrs ba,sabida ba k'aramin garin jiki bane da way'annan yaran kamar Nuraaz da yake k'arami haka nan suma suke hatta kamanninsa suka kwaso babu abinda suka bari, ita kuwa Hanan dama komai na babanta Abbi ta d'akko harma da yanayin sanyinsa.
Anan sukayi sallama,inda Abbi ,Ameen da Adnan suka wuce nasu part d'in,Abba ma yawuce part nasa inda ya tarda Mammi,Mufyda da kuma Hanan zaune suna kallon tarkon k'auna a tashar arewa 24 kasancewar yau monday ne, zama yayi cikinsu suka ci gaba da kallon tare bayan sun masa sannu da zuwa, Mammi ce ta kawo masa dinner d'insa a nan cikin parlon bayan Mufyda da Hanan sun basu wurin sun tafi d'akinsu.
Wajen k'arfe tara na dare kamin Mammi ta kashe kallon ta lek'a d'akunansu Mufyda ta tarda sunyi bacci, addu'a ta sake tofa masu dikda tana da yak'inin sunyi amma dai saida ta sake masu taja masu k'ofa, lek'a d'akin Janan tayi ta tardata zaune kan gadonta! idanunta sanye da gilashi tana lat'se lat'se cikin laptop dinta.
"ki tabbatar kinyi addu'a kamin ki kwanta kinji dota na...?" Mammi tace cike da kulawa."Insha Allahu Mammi zanyi saida safe."
"Allah ya tashe mu lafiya." Daga haka Mammi taja mata k'ofa tawuce turakar mai gidan nata...!
Sai da Janan ta tabbatar Mammi sun kwanta wajen goma na dare kamin ta mik'e sad'af-sad'af ta fice daga parlon tawuce d'aya daga cikin shashin dake cikin gidan.
Tura k'ofar tayi,cikin sa'a kuwa tajisa a bud'e! Shiga tayi sannan ta dannan key taciki ta doshi d'aya daga cikin bedrooms d'in dake jere a wurin bayan ta tamke fuska kamar bata tab'a dariya ba t'sawon rayuwarta...!
*Shin mai kika fahimta akan wannan littafin zuwa wannan lokacin...?*
*T'sakanin Janan ,Hanan ,da kuma Mufyda wacece tauraruwarki cikin littafinnan...?*
*✅ote*
*comment*
*share*
*follow me on wattpad@Oum-Mumtaz123🚴🏻♂️🚴🏻♂️🚴🏻♂️*