*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
_(Treasure of noor)_*wattpad:UMMIE2018*
*MALLAKAR:oum mumtaz**shafi na sha tara*
******** Nuraaz sai bayan sallar isha'i kamin ya shigo gida,kuma sun had'u dasu abba a lokacin shigowarsa da niyyar wucewa wurin mamminsa,amma haka abba ya rufe idanuwa yamasa tas ya fatattake sa kan karya kuskura yasake shigo masu cikin gida harsai sun nemesu,idan kuma sukak'i tabbas kuwa zasu k'ara masu t'sat'st'sauran punishment...!
da b'acin ran abinda yafaru ya shigo part d'in nasa fuskarsa kamar hadarin gabas...!
zaune ya tadda janan na kallo ga dikkan alamu taji k'arfin jikin nata...!tana sanye da wani b'ingilar rigarta ta shan iska sbd yadda takejin gumi na fitowa a jikinta sbd sauk'ar zazzab'in nata...! ganin yadda ya shigo fuska a d'aure yasa itama d'aure tata fuskar tamau kamar hadarin gabas cikin t'sare gida da nuna itace babba tace "Kai yaronnan zonan...!" tayi maganar tana mai sakarma nuraaz idanuwa daya ci burki babu shiri sbd jin kalar k'iran rainin wayon janan d'in tamasa...!
juyowa yayi a harzuk'e yadawo kuwa kamar yadda ta buk'ata ya t'sareta da idanuwansa daya sa tafara shiga setti sbd cika mata ido da nuraaz d'in yayi a daidai wannan lokacin...!
take ta arowa kanta juriya ta yafa tasake shan kunu batare data kalli cikin idanuwansa ba tace "kai dama wannan itace tarbiyyar dana baka tin yarinta nuraaz...? ban koya maka yadda ake sallama ba idan za'a shiga wuri...!? ban kuma ce maka kana gaida dik wanda ya girme maka ba da har zaka sa k'afa ka shigo batare da kayi sallama ba sannan baka gaishe ni ba a mat'sayina na yayarka sbd t'snanin rainin dake neman shiga t'sakanina dakai ba...? toh wlhi ka kiyaye ni...! idan kuma kace ba tabbas ranka idan yayi million saina b'ata shi in gaya maka...! sbd kafi kowa sanin halina bade a baka labari ba saidai kai ka bama wasu...! oyo ka juya ka fice daga parlon nan kuma kamin sallama idan zaka shigo...!"
janan ta k'are maganar cike da kumfar baki tana nuna ma nuraaz k'ofar parlon da hannu batare data kalli cikin idanunsa ba...!
*yasin na gaji🙄🙄*
*✅ote*
*comment*
*share*
*follow me on wattpad@ummie2018🚴🏻♂️🚴🏻♂️🚴🏻♂️*
