*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
_(Treasure of noor)_*©OUM MUMTAZ*
*5*
********Bayan wata bakwai.
Mami ta sauk'a a wayewar garin safiyar yau, inda ta haifo yaranta santala santala har gudu uku reras!Maza biyu sai kuma mace guda d'aya bayan bak'ar wahalar data sha wurin nak'udar da kwana akayi kamin aka sauk'a.
Kowa ka gani cikin wannan gidan,dama way'anda suke kewaye dasu sai farin cikin da walwala zaka hango shimfid'e bisa fiskokinsu,sabida irin kyautar da ubangiji yayi masu da basu t'sammata ba a wannan lokacin na 3ples!
Inna Zainaba ma takanas ta tare a shashin Mami a ranar data samu labarin haihuwar mamin.Su Nuraaz an bar sahun yara an koma Yaya Nuraaz yanzu, kowa yagansa a wannan gidan ansan ba k'aramin farin ciki yake ciki ba, su anty Janan ma an gagara mot'sawa ko nan da can, ana mak'ale a d'akin Mami ana kallon 3ples, hakan yasa Nuraaz ma biyo sahunta.
Haka nan y'an uwa da abokan arzik'i suka yi ta zuwan masu barka tin daga wannan ranar, Mammi ma kusan ko yaushe tana shashen Mamin idan dai ba dare bane yayi.*RANAR SUNA*
An yanka jibga-jibgan raguna da kuma shanaye anyi komai a wadace, suna an gama sa lafiya sai son barka, sunan yaran kuma:
*Muhammad Sani* baban su Mami (Ameen)
*Kamaludden* baban Abbi (Adnan)
*Zainab* mai sunar Inna Zainaba Mmn Mammi (ana kiranta da Hanan).Yara sosai suke sumun kulawa daga wurin t'sohuwa inna Zainaba babu k'ak'k'autawa, bama kamar Hanan da take ji kamar ta lasheta sabida kalar karar da Abbi yayi mata yasamata takwara.
Cikin kwana arba'in yarannan idan mutum yagansu saii yace sunyi wata biyu ne, jikinsu yayi k'wari sosai,wanda a lokuta da dama Hanan tana wajen Mammi, sabida ganin yarinyar take kamar y'arta hanan marigayiya data rasa.
Lokacin da suka cika wata biyu aka samawa nuraaz makaranta na kwana wato boarding school barewa college...!
Saida aka kai ruwa rana da Nuraaz sosai kamin ya amince da tafiyarsa makarantar, Janan ma bataso tayi nisa da k'anin nata ba,amma kuma babu yadda ta iya haka nan sunaji suna gani da kuka suka raka shi makaranta,inda yafara daga jjs 1.Watansu 3ples uku Mami tafara ciwon k'irji sosai babu k'ak'k'autawa, tin abin anayinsa na t'sait'saye har takai takawo ciwo ya kwantar da ita, wanda hakan sosai ya d'aga masu Mammi hankali bana wasa ba, babu shiri aka janye su 3ples daga shan nono aka fara basu madara,tin suna k'in karb'a harma suka zo suka saba,
renonsu gaba d'aya kuma yakoma hannun Mammi ne,ita kuma Janan na taimaka ma mahaifiyar ta.
Tasha jinya sosai ba kad'an ba na t'sawon wata biyar,wanda har Nuraaz ma yazo hutu na first term yakoma tana kwance.Ashe dai ciwon ajali ne ya kwantar da Mami, inda aka wayi gari aka tarda gawanta kwance flate akan katifa bayan dawowar Abbi daga masallaci sallar asuba😭😭.
Da asuba kamin Abbi ya fita sai da ya taimaka mata tayi alwala ya tabbatar da cewa ta tada kabbarar sallah kamin ya fito yashiga d'akin janan ma ya tasheta yasakai ya fice yanajin zuciyarsa na t'sananin bugawa sosai ba kad'an ba.Bayan Janan ta idar sallar asubahi ba tare data jira tayi addu'ointa kamar yadda tasaba ba tashiga kitchen nasu ta kunna gas, ta d'akko tukunyar da daren jiya ta riga data gama had'in komai na shayin dake had'e da kayan yaji dakuma k'amshi ta d'aurasa.
Ficewa tayi zuwa d'akinta,toilet tashiga bayan ta fito ta feshe jikinta da turaruka masu k'amshi,kamin ta zura doguwar riga ta abaya ta d'aura gyalen a kanta mat'sayin d'an kwali, daga nan kuma ta koma kitchen ta juyo shayin a tea plast, kamin ta doshi d'akin mahaifiyar tata,inda ta tardata kishingid'e bakin gado bakinta na mots'i alamun addu'a takeyi daga kishingid'en.
Zama tayi daga bakin gadon ta rik'o hannun mahaifiyarta tana gaisheta had'i da tambayar jikinta.
Shayin ta zuba mata a cup tana bata daga zaunen datake,tas ta shanye harda naiman k'ari, inda ta farayi ma Janan wasu maganganu maras kan gado daba fahimta janan d'in keyi ba, kamin ta rungume y'artata a jikinta,dik kuwa da kalar ciwon da k'irjin nata yakeyi,saketa tayi ta umarceta kan taje ta wajen Mammi ta d'akko mata 3ples tana son ganinsu.
Ita kuwa janan cike da jin dad'i ta wuce part d'insu Mammin na ganin yadda lafiyar mahaifiyarta ke samuwa,b'angare d'aya kuma haka nan zuciyarta keta kai kawo...!Bayan sun gaisa da Mammi ta shaida mata sak'on Mamin,hakan ne yasa Mammin d'aukar Hanan da Ameen a hannunta,ita kuma janan ta d'auki Adnan suka wuce shashin nasu, da sallama suka shiga d'akin Mamin amma shuru bata ansa masu ba,hakan yasa Mammi tayi tunanin bacci ne ya d'auki Mamin, Janan kam tasan Mamin nata ba wani nauyin bacci bane da ita,yasa tace, "Mami ki tashi ga nan 3ples d'in mun kawo su tare da Mammi!"
Shuru sukaji bata ansa ba, hakan yasa janan mat'sowa ta wajen kan Mamin, ja da baya tayi a d'an t'sorace,na ganin yadda fuskar mamin yake a kafe kamar ma bata numfashi, mat'sowa tak'arayi dakyau tana mai nazarin fuskar mahaifiyar tata kamar mai son gano wani abu.Mammi ce ta mat'so itama tana kallon Mamin a d'an t'sorace, dikda abinda idanuwanta suke gane mata bata sare ba,hakan yasa ta ficewa daga part d'in Mamin a hargit'se ta nufi k'ofar gate,inda sukayi clashing da Abbi da kuma Abba da suma shigowarsu kenan daga masallacin,sabida sun t'saya d'aukar karatu yasa ba su dawo da wuri ba.
Ganin yadda kamar a gigice take ne yasa Abba rik'o hannunta shima a nat'se yana tamnayarta, "Lafiya!?"
Kasa magana tayi,sai nuna masu part d'in Abbin da take yi da hannu,wanda hakan yasa zuciyar y'an maza saida ta girgiza (Abbi).
Ba tare da Abbi ya jira k'arin bayani ba yawuce part nasa kamar ana hankad'a sa su Mammi suka rufa masa baya tare da Abba hankali tashe.
D'akin Mamin da yake jiyo sambatun Janan cikin muryar dakana jinta kasan a gigice take ta kut'sa kansa, a hanzarce ya k'arasa wurin ya mat'sar da Janan d'in data kanainaye mamin tana kuka yayi, "Yahanasu! Yahanasu!"Haka nan Abbi yake ta faman k'iran sunan Mamin yana girgizata a gigice amma yaji shuru bata ansa ba, hakan yasa bai jira wata wata ba ya sungumeta suka fito daga d'akin Janan nabinsu a baya tana mai sakin kuka bana wasa ba.
Abba ne ya sake hannun Mammin shima ya k'araso yana tambayar abokin nasa ko lafiya zuciyarsa na t'sananin bugawa na ganin condition d'inda aka fitar da k'anwar tasa.Abbi bai kula Abba bama sai neman hanyar dazai fita yakeyi,hakan yasa Abba bud'e masa k'ofa shi kuma yatafi part nasa ya d'akko makullin mota a hanzarce suka shiga abban suka bata wuta zuwa asibiti mafi kusa dasu...!
Tin a yadda likitoci suka ga yadda aka kawo Mami suka fahimci tariga mu gidan gaskiya,amma sabida su k'ara tabbatarwa saida akayi gwaje-gwaje.A asibitinnan abbi ya zube sumamme aka shiga dashi emergency, Abba ma kuka sosai ya fashe dashi dik kuwa da daurewar da yake k'ok'arinyi na ganin wannan ranar daya rasa tilon k'anwarsa a duniya data rage masa...!
A k'ofar gida suka tarda Mammi da Janan tare da sauran ma'aikatan gidannasu sai sintiri sukeyi a k'ofar gida daga ganinsu kasan bana lafiya bane, ai kuwa lokacin da aka fito da gawar Mami ne yasa mutane da dama fara sallallami,maras hakalin cikinsu kuma suka fara zunduma ihu,kalar wanda ba'ason dik wani musulmin k'warai ya aikata shi😭
Janan kam jin abinda ake cewa maminta ta rasu tamkar a mafarki ne, kallon kowa take d'aya bayan d'aya tanajin wannan abinma is imporsible...!Da taimakon mammi da wasu daga cikin y'an unguwa aka suturta mami akayi mata wanka aka kint'sata, su 3ples kamar sunsan maike faruwa sai challara uban kuka sukeyi kamar ana yankan naman jikinsu,haka nan Umaima mai aikinsu keta faman rarrashinsu,itama tana alhinin rasuwar uwar d'akin nata, tana da dad'in zama sosai Mami,masifarta ma da take yi sai idan ka tab'ota kuma shima dik a barazana takeyinsa, bacin wannan Mami bata da wani aibu wanda mutane da dama sukayi mata kyakkyawan shaida.
Jana'iza k'arfe 2 na rana za'ayi,dan haka y'an uwansu abbi dasu mammi dik sun samu labari,kowa yazo shi anata koke-koke, Inna Zainaba ma sosai wannan mutuwa ya girgizata fiye da tunanin mai karatu.
Abba ne ya koma asibiti yataho da Abbi gida daya farfad'o, inda dik wanda yaga Abbi a wannan ranar ansan mutuwar matar tasa ba k'aramin dakarsa tayi ba,Abba ma dai kawai dauriya yakeyi a mat'sayinsa na namiji, amma kuwa shima da zai samu dama ba k'aramin kuka zaiyi ba, k'arfe biyu daidai na wannan ranar aka mik'a Mami gidanta na gaskiya😭😭inda dik wani musulmi saiya je ya tadda abinda ya aikata a cikin wannan waje😭😭😭
Allah kasa mucika da imani mufi k'arfin zuk'atanmu😭😭😭
Janan gaba d'aya ta zauce a wannan ranar da bata t'aba hasashen zata riske shi ba t'sawon rayuwar ta, tayi kuka, tayi kuka, tayi kuka😢 daga baya kuma ta zama kurmar dole.Mammi ce ke k'ara tausar zuciyar Janan d'in itama cikin k'arfin hali da kuma t'soron duniyar da abinda ke cikinta, haka akayi ta samun mutane masu zuwan masu ta'azziya daga wurare da dama, Abba da Abbi ke karb'an na k'ofar gida,mata kuma part d'in Mammi sabida an rufe part d'insu janan d'in sai dare Abba suke bud'ewa shida abbi idan zasu kwanta.
Bayan anyi sadakar bakwai.*✅ote*
*comment*
*share*
*follow me on wattpad@Oum-Mumtaz123🚴🏻♂️🚴🏻♂️🚴🏻♂️*
