shafi na ashirin

125 7 0
                                    

*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
       _(Treasure of noor)_

*OUM MUMTAZ*

             *20*

********Wani mat'siyacin kallo mai kama da gargad'in karki sakemin kalar wannan nuraaz ya antayama janan d'in daya sata sauk'e hannunta k'asa a sukwane tana magana k'asa k'asa alamun gunguni takeyi...!
k'wafa yayi ya wuce bedroom nasa fuu kamar wani kububuwa sbd takaicin janan ma kad'ai ya isa yasa masa hawan jini yanxu gakuma nasu abba ma dayake ganin faruwar hakan da kamar wuya...!

saida taga ya shige d'akinsa ta wut'siyar ido kamin ta sauk'e nannauyar ajiyar zuciya tana safe k'irji sbd yadda k'anin nata yau ya matik'ar yi mata k'warijini...! ta wani wurin kuma taji kunya yakamata,yanxu wai ace kamar nuraaz har shine zai mata wannan kallon kamar wata sa'arsa...? lalle kuwa sai ta koya masa hankali ta yadda ko gaba idan tace masa bazai tab'a t'sallekwa ba kamar yadda suka saba rayuwarsu a baya...!(karku zagar mani janan d'ita yasin🧐)...!

mik'ewa tayi ta tinkari bedroom d'inda nuraaz ya shiga albarkatun jikinta sai faman mot'sawa sukeyi sbd kalar rigar dake jikinta...!

tura bedroom d'in tayi ta shiga batare da tayi sallama ba...! a sukwane ta juyo da niyyar ficewa sbd kallon nuraaz da tayi babu komai a jikinsa sai boxes nasa daya matik'ar d'amesa yayi daidai akan gado iskar ac na kad'asa yana kallon k'ofar d''akin nasa sbd sanin t'saurin ido kalar na janan ba barinsa zatayi ba saita biyo sa ta sake masa wani d'ibar albarkar...!

da hanzarinsa ya mik'e,taku biyu lafiyayyu ya isko inda take ya wani fisgota ta fad'o jikinsa da har kanta saida tayi yamata wani d'an banzan zafi...!

saikuwa gata nan y'ar cinkul a gaban nuraaz d'in kamar wata babyn roba sbd yanayinta na rashin girma...!

gabanta ne yafara dukan tara tara tafara k'ok'arin kwace kanta daga rik'on da yayi mata had'i da kalar kallon data ga yanabin jikinta dashi,idanunsa sun kad'a sunyi jazur...!

daburcewa tayi fa sosai tafara neman hanyar guduwa sbd t'soron abinda nuraaz d'in kan iya aikata mata...!

wani miskilin murmushi na gefen baki yasake ya d'auketa kamar y'ar t'sana ita kuma tana wut'sul wut'sil da k'afafuwa kan ya sauk'eta amma yayi biris da ita sbd yaci alwashin yau sayya koya mata hankali wallhi...!

kan gadon ya kwantar da ita ya haye kanta yamata rumfa da faffad'an k'irjinsa yanabin fuskarta zuwa k'irjinta dake cike dam dam da kallon sha'awar dayayi kwana da kwanaki yana dannewa...!

"yaya dan allah kayi hakuri...! wlhi bazan sake maka rashin kunya ba...! kabarni naje na kwanta kaji yaya nuraaz...?" janan tayi maganar muryarta na rawa cike da lallashi...!

hmmm dashike nuraaz d'in ya fita duniyanci kota kan hak'urin da take basa bayyi ba yafara aika mata da wasu zafafan wasannin da tinda suke wannan shirmen nasu bai tab'a gwada mata kalarsu ba...! sosai nuraaz yake gurzan bakin janan d'in kamar wani zakin da yayi sati yana farautar abinci bai samu ba...!

dad'i da zafi ne ya had'e ma janan lokaci d'aya...!inda dad'in datakeji ya rinjayi zafin tuni ta bada kai bori ya hau itama dashike dikkaninsu sun iya jarabar🤗

sun gurji junansu sosai saida suka samu gamsuwa batare da anyi sex ba kamin suka sarara ma junansu suna sakin numfarfashi rungume da junansu...!

saida suka gama dawowa hayyacinsu kamin wani bahagon kunya ya zurmowa janan da taji tamkar ta nit'se k'asa...! itakam tana mamakin kanta ta yadda take da k'arfin sha'awa da abu kad'an ke taso mata...!

shikuwa goga zareta yayi daga jikinsa yana shan kunu ya zaro towel ya d'aura a k'ugunsa ya fad'a bedroom batare da ya kalleta ba..!
bayan ya fito daga wankan ma bai sameta a d'akin nasa ba alamun ta gudu d'akinta...!

saida ya murza mansa a lafiyayyar skin nasa kamin ya zura kayan baccinsa riga da wando ya fito suwa d'akin janan d'in daya taddata duk'unk'une cikin bargo alamun tayi baccinta...!

bai ce k'ala ba ya had'a tea abinsa da kayan shayin daya kawo mata d'azu mai kauri ya d'auki ledar bread d'in ya fito parlo ya zauna yana shan shayinsa had'i da bread badan dad'i ba saidan sbd t'sananin yunwar dake neman kaisa barzahu...!

ya d'auki t'sawon lokaci a parlon yana kallo sai wajajen goma na dare kamin ya mik'e yakoma bedroom nasa cike da damuwa ya lat'so number mammi amma yaji ba''a d'auka ba,bai hakura ba yaci gana da k'ira,inda daga k'arshe ma yaji wayar switch off...!

wani mololon bak'in ciki ne ya masa karan t'saye a mak'ogwaro ya hau kan bed nasa ya duk'unkune jikinsa yana tunanin abubuwa da dama...!

daga k'arshe kuma moment nasu da janan na d'azu ya dawo masa daki daki,batare daya shirya ba wani k'aramin murmushi yayi masa escaping akan lips nasa idan ya tuno dacewa yau janan ta k'irasa da yaya nuraaz,da bai tab'a t'sammanin zuwar wannan ranar ba💃

a haka wani daddad'an bacci yayi gaba dashi mai cike da mafarkai barkata tai gasu nan dai...!

Mammi saida abba ya fad'a mata komai ta yadda zata fahimta akan dalilinsu na aurawa janan da nuraaz aure,itama kuwa sosai taji dad'in hukuncin dasuka yanke sbd bazasu aurama wani janan ba domin kuwa kamar sun zalinci dik wanda ya aureta ne tinda dai ba fad'a masa abinda janan d'in sukayi za'ayi ba,dan haka suda suka fara abinsu suje can su k'arata wannan shine daidai...!

d'azun ma tana kallon kiransa da gangan tak'i d'auka sbd hakan ma na d'aya daga cikin hukuncinsu...!

mommy kam acan shashenta sai faman gyra y'ar tata takeyi mufy kuwa na ta faman mita wai ita yarinya ce batakai aure ba sun tashi sun aura mata wannan mugun,idan mommy taji haka saida kawai tayi murmushinta,sbd itakam allah ya gani tin mufy da nuraaz na k'anana take fatan su zamo k'ark'ashin inuwa d'aya,gashi kuma hakan ta faru cikib ruwan sanyi batare datayi tunanin wannan burin nata zai cika ba(allah kenan ai nace)...!

*FREE PAGES NA LITTAFIN SILAR AL-MAJIRANCI YA K'ARE...! HARMA AN FARA POSTING NA PAID PAGES...! KU GARZAYO DA NAIRA 200 KACAL DOMIN SAMUN DAMAR SHIGA CIKIN PAID GROUP KO DON SBD KU NUNAMIN K'AUNA ZUWA GARENI💋💋💋*

*✅ote*
*comment*
*share*
*follow me on wattpad@ummie2018🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂️*

NURAAZ(treasure of noor)Where stories live. Discover now