*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
_(Treasure of noor)_*23*
******** "Janan ne tayi accident tin da wajen k'arfe tara na dare akan hanyarta na zuwa asibiti ashe!? kuma anyi ta neman wayarta ba'a samu bai sai yanxu da suka sake bincika cikin motarta sosai kamin suka gano wayar a yanzu haka suna asibiti inda suke aiki ita da N..!"
Ai kamin ma Abba ya gama rufe bakinsa Nuraaz yayi cikin part nasa da gudu cike da t'sananin tashin hankali ya d'akko key na motarsa da ko takalmi babu a k'afarsa ya dannan uban horn da mugun k'arfi su Abbi suna masa magana kar ya tuk'a motar yabari suyi amma sam baiji su ba,sai ma cinna kai motarsa da yayi bisa ga babbar kwaltar da zata sada shi da asibitin da suke aiki da wani uban gudu na sai da rai!
Tashin hankali kenan, Mammi kam kuka ta fashe dashi sosai su Ameen na taya ta, Abba yace su zauna a gida amma Mammi tace ita kam ba za ta zauna ba,ba tare da taje taga halin da yaranta suke ciki ba, Mommy ce ta rik'e Abbi dake k'ok'arin zubewa a k'asa saboda t'sananin yadda yaji kansa ya bala'in sara masa. Abba ne shima ya k'wala ma mai gadi k'ira tare da taimakonsa suka kai Abbi mota, Mommy da Mammi suka fito suma suka shiga Abba yace ma mai gadi ya kular masu da gidan kar abarsu Ameen su fita daga yanzu har zuwa lokacin da zasu dawo ya rufe k'ofar.
Su Adnan kam na kuka jin halin da y'ar uwarsu ke ciki ga kuma yanayin yadda sukaga Nuraaz ma ya figi mota,kuma an hanasu zuwa asibitin kawai suka fara kuka sosai,dakyar mai gadi ya lallab'a su suka koma ciki,Hanan da Mufy kam basu san ma halin da ake ciki ba saboda baccinsu da suka jima suna yi.Gudu sosai Nuraaz yake ta faman shararawa akan kwaltar dazai sada shi da asibitin yana ta sambatu yana t'siyayar hawaye kaman bana miji ba,idanuwansa har wani lullumshewa suke yi saboda yadda kansa ke barazanar t'sage masa na t'sananin ciwon kan da ya ziyarcesa.
Ba tare da ya ankare da yadda jama'a keta faman d'aga masa hannu ba ana cewa ya kauce ma wata babbar mota da ta yanko da gudu sai kawai ji yayi an taga-taga dashi daga nan bai sake sanin abinda ke faruwa ba,mutane anyi tururuwa a wurin ana ta k'ok'ari fiddo da Nuraaz daga cikin motar da gaba d'aya motar ta lot'se k'arfen moton ya bubbula masa jikinsa sai uban jini ne yake t'siyayowa kowa sai salati yake ta famanyi,jahilan cikinsu kuwa har an ciro waya anatata faman vedio dazasuyi posting a social media. (Wanda kuma yanzu muna fama da kalar wannan rashin lissafin,kai da abu makamancin haka ya faru a wurin da kake a maimakon ka fara k'ok'arin taimakon mutum saidai kawai ayi vedio dikdan kawai duniya ta gani a nayi maka tambayoyi kai kuwa jikinka na mazari kana sake gaya masu yadda akayi kamar fad'ama mutane da kakeyi kud'i ake ba ka ko kuma lada zaka samu, Allah yasa mu dace Ameen)Abba ma sosai yake gudu akan kwalta har suka zo daidai inda Nuraaz yayi accident da gaba d'aya kan kwaltar cike take taf da jama'a amma an rasa mai d'aukarsa ayi asibiti dashi saboda wauta, Abba ne ya sauk'o tare da Abba da yaji sauk'in hajijiyar da yake ji suka rat'sa cikin jama'ar saboda son ganin abinda ke faruwa aka cike hanya haka.
Abbi ne ya fara hango motar da Nuraaz ya fice da ita a lollot'se,zuciyarsa ce ta fara bugawa fat fat ya rik'o hannun Abba tamau jikinsa na d'aukar rawa bakinsa ya gaza furta ko da kalma d'aya saboda hango Nuraaz da yayi cikin jini sosai ba kad'an ba.
Kamin ya samu zarafin magana sun k'araso wurin Abba ma ya ganema idanuwansa wanda ke kwance cikin jini bana wasa ba,sosai yaji zuciyarsa ta t'sinke da wannan lamarin.Sai da mutane suka taimaka aka kai Abbi motar da ya sume a wurin saboda yadda yaji kansa ya sara masa wurin,inda Abba yasa wani matashi yaja su Mammi kan ya karasar dasu zuwa asibitin.
Mammi ma sosai take ta faman kuka saboda Abba ya hana ta fitowa daga cikin motar sanin da yayi cewa idan taga Nuraaz cikin wannan yanayin komai zai iya faruwa da lafiyarta.Wani mutumi ne ya k'ira asibiti da kuma location d'in da suke babu jimawa motar emergency ta k'araso wurin aka saka Nuraaz a ciki da babu alamun rai tattare dashi.
Abba kuma wannan mutumin ne ya d'aukesa a mota suka bi bayansu.Banda salati da addu'oi babu abinda Abba yake yi cikin zuciyarsa a wannan lokacin,shima da da hali kukan zai yi ko zaiji sauk'in abinda yake ji cikin zuciyarsa amma kuma wai akace kukama rahma ce ga d'an Adam, wanda shi kuma kukan ne ma yak'i zuwar masa sai t'sinkewar zuciya..
Ya riga da ya sadak'ar cewa kwana Nuraaz ya k'are a duniya saboda ko kai idan kagansa zaka san cewa abin dai toh babu dad'in gani😭*✅ote*
*comment*
*share*
*follow me on wattpad@ Oum Mumtaz123🚴🏻♂️🚴🏻♂️🚴🏻♂️*