*🌸🌸NURAAZ...!🌸*
_(Treasure of noor)_*©OUM MUMTAZ*
*16*
******* "Ashe baka da hankali ban sani ba Nuraaz? Soyayyya akace maka hauka ne da zakana jijjiga mahaifiyarka har haka akan mace? A kan mace kake neman aikata babban kuskuren da har abada bazaka tab'a daina dana sani ba? A gaskiya kayi wa kanka fad'a, kasan mainene ya dace da kuma wanda bai dace kayisa ba idan baka cikin hayyacinka."
mommy ke wannan maganar cike da mad'aukacin b'acin ran shirmen da Nuraaz yake faman aikatawa mahaifiyarsa akan soyayya kaman wanda ya zaucewar k'wak'walwa. Mammi kuwa sosai take kuka sabida ganin wannan ranar da bata tab'a t'sammani ba t'sawon rayuwarta.
Gasu Hanan ma da suke kuka sosai suna k'ank'ame da junansu sabida t'sananin tashin hankalin da suka shiga akan abinda ke faruwa cikin gidan nasu. Abba tari ya sark'e masa na abinda idanuwansa suka gane masa dayakejin gara yaga ranar mutuwarsa akan bad'alar da d'ansa na cikinsa da kuma y'ar k'anwarsa suke aikatawa cikin mahallinsu da ransu da kuma lafiya wanda ba komai bane ya jawo masu hakan kuma illa *SAKACINSU* da kuma rashin wadata y'ay'an nasu da ilmin islama saina boko dik *A SABODA DUNIYA* ...!
Ihun Janan ne ya karad'e cikin parlon daya sa hankalin kowa yakoma kanta, tashin hankali kenan domin kuwa Abbi ne ya zage iya k'arfinsa yake kirb'an Janan d'in kamar yasamu kayan wanki, dukanta yakeyi kamar Allah ne ya aiko sa kuma aka rasa mutum d'ata dazai karb'eta sabida kowa ba cikin hayyacinsa yake ba.
Dukan ne ya fara yin yawa sabida abbi niyyarsa yayi ma Janan d'in babban illlah ne, da wani mugun firgici na ganin yadda idanuwan Janan yake ta faman lumshewa alamun gaf take da rasa numfashinta Mommy tayi nasarar hankad'a Abbi gefe da shima kansa kukan bakin ciki yake sabida abinda ya gane ma idanunsa.
Taga-taga yayi zai fad'i Ameen da Adnan da tin d'azu suka k'ame wuri d'aya kamar basa cikin parlon suka tarosa suka zube baki d'ayansu.
Hanan ce cike da tashin hankalin na ganin kamar Aunty Janan d'in za ta mutu ta kawo ruwa da gudu mai matik'ar sanyi tafara kela mata a fuska, banda gunjin kuka babu abinda Janan take yi sabida wallahi ba k'aramin bugu tasha a hannun abbi ba wanda takejin alamun ya karya mata wani wurin cikin gab'ob'in jikinta, a ranta kuwa ta riga da ta fahimci abinda suka gani cikin wayar ya dangance ta.
Mommy,Hanan da Mufy ne suka kamota suka fice da ita daga wannan part d'in suka wuce part nasu da ita sabida Mommyn tabata taimakon gaggawa kasancewar ta babbar likita, da k'yar Abbi ma yaja k'afafunsa tare da taimakon su Ameen suka koma part nasa inda suka kaisa har bedroom nasa kan gado suka tabbatar daya kwanta kamin suka fice xuwa d'akin Mommyn, anan suka tarda Janan na bacci tana sauk'e ajiyar zuciya a galabaice sabida allurar samun hutun da mommy tai mata.
Ga hanan da dik tabi ta t'sangwami kanta ta d'aurawa kanta alhakin ciwon Janan d'in, sai rasgar kuka take ta tasa yayar tata a gaba cike da danasanin nuna vedion da tayi, tana matik'ar son y'ar uwar tata amma kuma tana bala'in kishinta dik kuma ba akan kowa bane sai dan *NURAAZ* da ta budi ido da natsananciyar soyayyarsa.
Mufy ma dikda ba kasafai suke shiri da Janan d'inba amma kuwa ta matik'ar tausaya mata akan wannan bugun kayan wankin da Abbi yayi mata, dikdama dai tasan ba'a banza Abbi zai mata wannan dukan ba har sai idan yana da k'wak'k'waran dalilinsa tinda ba ta taba ganin yasa hannu ya daki daya daga cikin yaransa ba a dik tsayin zaman ta a gidan.
Ameen da Adnan suma suna kallon Janan d'in cike da tausayawa, abinka ga farar fata babu quality😝, shatin dukannan ya fito rud'u-rud'u,
hatta fuskarta akoi shatin bulala da kuma marin da abbin yayi ta wawwaska mata."Hanan mai kika nunama su abbinku?" Mommy ta tambayi hanan d'im fuska d'aure sabida ta tabbatar dik wannan abinda ya biyo baya bawai akan Mammi tace Nuraaz da ita Hanan d'in sunsha nono d'aya bane sai dan abinda hanan d'in ta nuna masu...!
cike da t'soro bakinta na rawa Hanan tace, "babu komai mommy dan allah kiyi hak'uri."
Babu yadda Mommyn ta iya tinda ba zata saka ta dole ta fad'a mata ba tace, "Maza kuyi shirin bacci kuzo ku kwanta anan tare da yayarku, kuma Adnan maza ku wuce kuje ku kwanta sabida dare yayi sosai, yanzu kusan sha biyun dare." Cike da ladabi da kuma sanyin jiki suma suka wuce nasu d'akin sunama yayar tasu fatan samun sauk'i.
D'akin Abbi ta shiga hannunta rik'e da firstaid nata inda shima ta tarda sa zazzab'i yayi masa mummunar kamu a lokaci d'aya sai rawan sanyi yake yi, taimakon gaggawa tafara basa inda shima daga k'arshe ta masa alluran bacci.
Sai da ta gyara masa kwanciyarsa sosai kamin ta sauk'e k'ak'k'arfar ajiyar zuciya ta shiga band'akin Abban ta wat'so ruwa kamin tasaka sleeping dress nata dake d'akin abban itama ta kwanta ta lula duniyar tunanim abinda ya wakana daga shekaran jiya zuwa yau d'innan.
Ita babban abinda ma yafi d'aga mata hankali yanxu shine *AUREN NURAAZ DA MUFYDA DA AKA D'AURA JIYA A CAN JALINGON BA TARE DA SANIN D'AYA DAGA CIKINSU BA, WANDA KUMA DAGA ABBA,ABBI,ITA KANTA,SAI KUMA DANGIN BABAN MUFYDAN DAKE CAN JALINGO SUKA SANI WANDA KO MAMMIN NURAAZ D'IN BATA DA LABARI🙊*Maganin ciwon kai ta wat'sa a bakinta ta kora da ruwa sabida jin yadda kanta ke bala'in sara mata akan stress da yayi mata yawa, babu jimawa bacci yayi gaba da ita.
BANGAREN SU NURAAZ KUWA...!
Durk'ushe yake a wannan wurin tinda mommy ta maresa ya gagara mat'sawa daga wurin ballantana yasan mai ke wakana cikin parlon sbd gushewar wucin gadin da kwanyarsa tayi, wai Hanan d'in daya k'wallafa rai akanta itace ake nufin ace aure t'sakaninsu ya haramta? Shin da gaske Mammi take wannan zancen nata ko kuwa dikdan sbd batason farin cikinsa ne na nan gidan dubiya yasata k'irk'iro wannan maganar? (kujimin d'an k'wal uba mai kan kwakwa😒) Shifa yanzu bawai ta abinda Hanan d'in ta nunawa su abba yake yi ba sai tunanin ta yadda za'ayi ya mallaketa a mat'sayin matarsa kota halin k'ak'a.
Da k'yar Abba yaja jikinsa yafad'a bedroom sabida idan ya mik'ema ba k'aramin jiri yake d'aukarsa ba.
Gashi ko kallon nuraaz d'in yanzu shi sam baya sonyi sabida t'sananin takaici dakuma t'sant'sar bak'in ciki. Mammi ma cike da sanyin jiki ta wuce bedroom nata batare data ce ma Nuraaz k'ala ba sbd tunanin daya k'ulle mata kwakwalwa itama.*WASHE GARI*
*✅ote*
*comment*
*share*
*follow me on wattpad@ Oum-Mumtaz123🚴🏻♂️🚴🏻♂️🚴🏻♂️*