XXI

1K 166 5
                                    

UWARGIDAN BAHAUSHE

XXI (21)

✍️ Ayshatuuu 💜

Ban taba tunanin Yana da fada ba, saboda yadda yake girman Kai ne kawai abinda zaka fara fahimta kenan. Yayi fada har muka iso gida, uffan ban ce masa ba seda yayi parking na fara kokarin dakko Kaya yace

"Keep them, zaa shigo dasu"

Bance komai ba kuwa na nufi parlor, Rayha na dariya kasakasa na Harare ta nace

" Munafuka! Kiyi dariyar ki Mana"

Tana dariyar tace

" Kece ai, kinsan abinda yake nufi Amma kikai provoking din shi"

Nayi murmushi ban Bata amsa ba saboda isowar mu parlon Ummaah, suna zaune itada Anty jidda, Bayan duk awoyinnan ko mayafinta Bata cire ba, a raina nace anata kulla sharri kenan. Zama mukai muka gaishe su, Ummaah na tambayar mu yadda fitar ta kasance muka ce Mata mun ji dadi mun gode. Har zamu koma sama nace Mata

" Ummaah gobe karfe takwas zanyi jarabawar"

Ta gyada Kai tace

" Allah ya bada saa Ismail Zak raka ki"

Ba hakan naso ba Amma hakan Zan hakura, na wuce bayan munyi sallama da Anty jidda dake Mana kashedin saura mu ki zuwa gidan ta, a raina nace se kace yayanta na zuwa namu gidan ne. Muna karsawa daki na kwanta, Rayha tace

" Ba zamu je gidanta ba wallahi, munafuka"

Nayi murmushi nace

" Rayha ki rabani da zagin da kike ma dangin Baba Babu ruwana"

Tayi tsaki bayan ta gama cire kayan ta tace

" Yunwa nake ji, Bari na sauka na kawo Mana abinci"

Na gyada Mata kai ta sauka, ni Kuma na Yi wanka sannan na fito na samu Bata dawo ba, se kawai na shirya, Ina Zama naji anyi knocking kafin nayi magana kofar an bude ta, Yaya Ismail ya shigo, na Bata fuska tareda dauke kaina na mayar kan tv dake aiki, gefe ya samu ya zauna tareda hade hannayen shi biyu yace

" I'm sorry I shouted at you"

Bance komai ba na janyo littafi Dan fara karantawa se ya taso zai dawo inda nake, abinda na fahimta dashi Bai dauki body contact matsayin wani laifi ba, ganin zai taho yasa nace

" Karka zo! Just stay inda kake"

He comply, ya koma ya zauna ya marairaice fuska yace

" I love you..."

Zai cigaba da magana na katse shi da fadin

" Karatu zanyi fa"

Yayi shiru na Yan sakanni Yana kallona kafin ya sauke ajiyar zuciya ya fara kallon TV din, shigowar Rayha da tray yasa ya Mike ya aje min wayar shi yace

" In case you need it. Zan kiraki"

Bance Masa komai ba ya fita, na dauki wayar nayi dialing contact din Ammi tana dauka muka fara waya Ina fada Mata duk abinda ya faru a ranar. Rayha ta karba tace

" Ammi kinyi suruki fa"

Saboda yadda muke da Ammi, yadda take janmu a jiki yasa bama kunyar fada Mata komai, we believe Ammi kawar mu ce, Bata da Wanda zatayi Hira dasu se mu din dai, mu ne sanyin idaniyar ta!

" Wallahi Ammi wai Yaya Ismail ke sonta, Amma kinsan ba zata taba yarda tayi camping da enemies dinki ba"

Ina kurban tea Ina murmushi, Rayha ko banyi magana ba tasan me nake nufi tasan bazan taba yarda da zancen Ismail ba Amma a kasan raina I'm using him to avenge abinda akaiwa Ammi. Bayan mun Gama da Ammi ta Kira Yaya Fahad sunata hira ni Kuma Ina karatu.

Washegari very early na Gama shiryawa, tea kadai Nasha na fita, Yaya Ismail na jirana a mota muka tafi center Dina, muna zuwa baifi 30 mins ba muka Shiga, tabbas nasan nayi karatu, tunda na durkusar da kaina Banda solving da clicking Babu abinda nake, in less than an hour na Gama, na Kara komawa na dudduba sannan nayi submit na fito, I felt relaxed se adduar nasara kawai dake bakina. Tunda ya hangoni ya fara sakar min murmushi, na danyi yake Dan nasan ba murmushi nayi ba, Ina bude gefen shi na zauna ya Miko min chilled freshyo, kamar yasan Abu me sanyi nake bukata na amsa tareda Masa godiya na fara Sha, yace min a hankali kamar yadda maganar tashi take, yafi wata macen sanyin murya

" How was the test"

" Alhamdulillah!'

Na bashi amsa Ina aje bottle din hannuna,se mukai shiru se can yace

" Me kike planning bayan secondary?"

Na Dan kalleshi nace

" Nothing special! Karatu zanyi"

Ya Dan langwabar da kan shi yace

" Ki Bari muyi aure I promise you Zan kaiki duk inda kike..."

Nayi saurin katse shi nace

" No! Baba ma bazai yimin aure yanzun ba, karatu zanyi gaskiya. Beside ni bana sonka"

Seda na fada sannan naji maganar ta yimin nauyi a harshe na, you can't take back the word that's already out! Dan haka na Bata Rai na dauke kaina, ya Jima in shock din me na fada kafin yace

" Sofy just give me chance I'll prove myself!"

Daga haka bamu Kara magana ba har muka karaso gida, Muna shiga nayi breakfast Dan shi daki ya wuce, Nima na Gama na wuce daki bayan munyi Hira da Rayha na fara baccin gajiya. Tunda ya Shiga daki Bai fito ba se Bayan azahar, Ummaah na ganin shi tace

" Me ya sameka haka?"

Ya zauna gefenta Yana Dan tura baki yace

" Tace Bata Sona fa!"

Ummaah tayi dariya tace

" Shi ne abin tashin hankalin, rabu da ita itama yarinta me damun ta, ka Bata lokaci"

Lokaci zai fada idan yarinta ce ke damuna ko kuma akan Hanya nake. Kwana biyu muka Kara Rayha tayi tata sannan Ismail ya maida mu, shopping din da mukai na bashi books nace ya aika min su Gumel. Na bude kofar Zan fita yasa hannunshi ya riko nawa, na saurin juyawa nace

" Ka manta?"

Ya sakeni Yana murmushi yace

" Mantawa nayi. Tafiya zakiyi ba Zaki yadda ba?"

Na girgiza Kai nace

" Spare me! Allah ya kiyaye Hanya mun gode sosae"

Na zura kafata kasa na fita ko juyawa banyi ba saboda na fara jin zuciyata kamar zata ji tausayin shi, idan na Bari ta yimin hakan to tayi betraying dina. A hostel muka aje Kaya , bamu Kara kwana biyu ba JAMB ta sake results Kuma munci Rayha nada 220 ni Kuma 260 haka mukai. Ranaku na tafiya muka fara waec na rage bacci se karatu Yan class dinmu suyi ta tsokana ta Amma Ina ruwana ni karatuna nake. A hakan muka gama, bamuje gida ba se visiting Ammi ta zo Mana itada Baba, ba wani magana suke ba Amma Ina hango canji a tattare da ita, ta Kara Zama babbar mace ko daga maganar ta na fahimci nutsuwar da take dashi.

Mun fara neco Babu jimawa itama mukai muka Gama, Ina kan paper karshe TD teacher yace idan na Gama na sameshi, Muna fitowa se murna muke Muna exchanging contact mun Gama secondary School, na samu na wuce office din shi kafin Baba yazo Dan jiya munyi waya dashi yace zaizo ya dauke mu. Na gaishe shi ya min murna dukda banyi TD ba Amma malamai da yawa sun sani matsayin Senior prefect sannan yawancin haduwata da mutane karatu nake. Na mishi godiya sannan ya bude locker dake kusurwan office din shi ya ciro katuwar paper bag ya Mika min yace

" Idan kin samu time se ki duba, I wish you all the best"

Na mishi godiya na fito, Ina tunanin me ya hadani dashi da zai min kyauta har haka, na cigaba da tafiya Ina jin nauyin jakar tareda tunani kalakala. Can na wuce inda wasu har sun fara tafiya, motar yaya Ismail na fara hangowa sannan se ta Dr Bature, daga gefe na hango Na'ila da Rayha tsaye jikin motar yaya Fahad, nayi murmushi Ina ayyana waye zai dauke mu?

Shatttzzzx

UWARGIDAN BAHAUSHEWhere stories live. Discover now