UWARGIDAN BAHAUSHEXLVIII (48)
✍️ Ayshatuuu 💛
Nayi tunanin an gama case din shara, unknown to me Ashe ana ta piling min shara ta baya inda Nima ba gani zanyi ba Dan ban fiya bude kofar kitchen Dita ta baya, ranar Saturday ce Kuma tun safe ya fita, sun tafi bauchi shi da Baffa, yace min sunje nadin sarauta ne. Tunda ya barni a kwance se wajen Sha daya sannan na fito parlor na gyara abinda Zan gyara sannan na wuce kitchen, Zama nayi a bakin kofar Ina tunanin abinda Zan ci, to Kuma yunwar ma ba jinta nake ba, se kawai na Kara komawa daki na kwanta, ban fito ba seda nayi sallar azahar har lokacin banyi wanka ba Dan wata irin kiwar wankan nake gaba daya, kitchen na shiga Bayan na Kira Albi
" Se yanzun Kika tashi?"
Ya tambaya lokacin da ya dauki wayar, agogo na kalla naga biyu ta gota nace
" A'a tun dazun na tashi, karfe nawa zaku dawo?"
" Da an idar da laasar zamu dakko Hanya, have you eaten?"
Seda nace a'a sannan na tuna abinda na fada,
" Bakici abinci ba har past two? Me Kika dinga yi? My God!"
Tunda ya fara maganan nake murmushi, se daya gama yaji sautin murmushi na yace
" Dariya kike ko? Kin Raina ni ko?"
Na danyi dariya Ina rufe bakina nace
" Kai Hamma ya zanyi na rainaka, na tashi bana jin yunwa yanzun Kuma Abu nake son naci Kuma Babu a gidan"
" What's that?"
Nace
" Kifi!"
Na tabbatar seda yayi raising brows dinsa, saboda yasan ba fan din kifi bace ni,
" Yau Kuma? To Zan saka a Aiko Miki da Kifin Amma kinsan bashi kadai Zaki ci ba ko?"
Wani karfi naji ya zo min nace
" Bashi kadai ba, Zan dafa wani abun"
Daga haka yayimin sallama akan idan zasu taho zai kirani, abinci na daura inata tunanin me zanyi da Kifin idan an kawo, grilling zanyi ko farfesu zanyi, baa Jima ba aka kawo, danyen catfish, na saka cikin bowl na bude kofar baya Dan na wanke kada na Bata kitchen Dina da karni, banma lura ba da gurin har na Gama wankewa na saka cikin colander Dan ya tsane, na juyo na hanga shara an tare ta a gurin, na tsaya hannuna rike da venigar, na Jima a tsaye Ina ayyana yaushe aka Tara sharar nan ne, ni dai nasan watana kusn biyu Amma taba fitowa gurin ba, na gyada Kiana na cigaba da aikina Amma ban kwashe ba, se wajen hudu na Gama aikin sannan nayi wanka na gyaran gidan, na shigo kitchen naji ana shara, nayi saurin aje plate din hannuna na leka ta window, fadila ke sharar tana ta bulo ta inda ta Saba, seda na Bari ta Gama ta juya zata tafi sannan na bude kofar na fito nace
" Fadila!"
Ta kuwa tsaya cak, sannan ta juyo ranta a bace, nima tawa fuskar Babu alamar Wasa nace Mata
" Nan ake Tara shara dama? Ki dakko Abu ki tattara Kika kwashe"
Ta min wani kallo daya Kara kullar dani, tace cikeda rashin kunya
" Me zakiyi idan naki kwashewa"
Nayi murmushi Ina kokarin danne fushina nace
" Ai fada kikai, ki gwada kiga abinda Zan Miki"
Ta juya zata tafi nace
" Kinsan Allah idan Kika tafi Baki kwashe sharar nan ba se na baki mamaki"
Ta Kara juyowa tace
" Lallai Kam mamaki! Ke wacece da Zaki saka ni nayi abinda banyi niyya ba..."