💔 AFIYYA 💔
Nine (Free)
✍️ Ayshatuuu
Na Kara kallon shafcecen tsakar gidan sannan Kuma na kalli tsintsiyar hannuna, nifa bazan iya tuna last da nayi shara ba, kada ma nace ban taba ba aga kamar karya nake, nayi shiru Ina ayyana yadda zata kasance. Mino tuni ta wuce ta Kama aikin wanke wanke, ita Kuma Siyama tana hura wuta, a raina nace Allah kar kasa watarana ace Zan huta wannan itacen, inaga makancewa kawai zanyi. Ina nan tsaye rike da tsintsiyar Mino tace min
" Wai me kike jira ne"
Nayi raurau da idanuna nace
" Ban iya ba"
Tace
" Tab! Gwara ki koya Dan daga yau shi ne aikin ki, kada ma ki Bari Ummaan mu ta leko taga Baki Gama ba"
Jin haka se na duka na fara Amma yadda kukasan bayana zai balle, numfashi na har cicciko was yake, idanuna Suka kada sukai jawur, a Haka nayi tayi, dukda kawai Yi nake bawai Dan na iya ba, saa ta daya Babu datti tunda su mutane ne masu tsafta, ban taba zuwa Naga gidan su day datti ba, kullum a share yake. Nayi rabi na Kuma Bata wajen minti talatin inayi Ina dagowa Ina hutawa, naji dum! A bayana, nayi saurin sakin tsintsiyar na dago Ina rike bayan da nake lallabawa, Ummaan su ce a tsaye tana min wani mugun kallo
" Haka ake shara a gidan ku, koma baya ki fara daga farko"
Kallon da take min ma Bai Isa ya bani damar rokon ta da nake Shirin Yi ba, haka na dauki tsintsiyar Ina share hawayena na Kara tisowa daga farko, a kalla na Tisa sharar nan tafi say biyu, da kuka na karasa ta wajen karfe goma na safe kenan, Ina cikin sharar Yaya da Baba suka fito, seda ya kalleni na wasu mintuna kafin ya gyada kanshi kawai ya nufi gurin Babar shi, na aje tsintsiyar na gaishe shi ya amsa min fuskar shi a sake, Baba dama girman Kai ne dashi you can mistaken him for Dan gwamna, Yana ji da kanshi irin sosae dinnan fa, ya kalleni ya dubi Yaya dake tsaye yace
" Who's she?"
Na dago na kalleshi, haka yake ya kuma Saba min hakan, idan Ina gurin Abbu yazo zai gaida shi zaice me sunan tsofi Amma idan Ina gaban ko Hajiya indai bana tareda Abbu zaice Wai wacece wannan, idan aka fada Masa se yace Wai shi baya gane mu. Ko magana ban Masa ba seda Yaya yace na gaishe shi sannan na gaishe shi. Ina Gama sharar nayi wanka, wata Yunwa nake ji Dan hakan Ina saka Kaya nazo nace Ummaan su Yunwa nake ji, wani Koko ta Miko min a bude duk kuda sun Gama binshi se fanke a flask, naci fanken Babu laifi Amma kokon ban Sha ba, ganin hakan yasa Yaya fita, can Babu dadewa ya kwalla min Kira, Ina zuwa zaure ya bani tea me kauri yace na shanye cikin farar Leda, na karba nasha sannan na Masa smiling na godiya na koma ciki. Wajen azahar tace naje na kunna wutar girki ni da Siyama, ta nuna min yadda akeyi, gabana ya fadi ga ciwon jikin shara, ga radadin fuskar net ga wata azaba da zaayiwa idanuna. Haka mukaje muka hura wutar girki, idanuna sukai jawur, numfashi na ya cunkushe muna Gama daurawa aka bani dakan yaji, ranar haka na wuni kana kallo na kasan a gigice nake, kafin yamma wata sabuwar mura ta balle min, saboda hayaki, shara da Kuma abin borkono, ga dama nayi Rama a mutuwar Abbu yanzun ma se na fara akan ta da. Duk wannan abin da ake Banga Kawu Sa'idu ba, seda nayi sati daya, har na fara hakura da saka ran wani zaizo yaga halin da nake ciki ya tausaya min ya tafi dani, idan nayi wani tunanin se Naga waye ma zaizo, Mummy na NY, Uncle Babawo na UK, Kawu Tijjani na Kano, Nanny na maiduguri. Dama su dinne, se na hakura na fawallawa Allah na saka a raina am stuck a cikin gidannan kila sede a fitar da gawata. Wannan kwanakin bakwan na tashi tsakar dare nayi kukan da ban San sau nawa ha, nayi addua Allah yasa Nima na mutu da bakar wahalar da nake Sha, Amma kullum jiran mutuwar nake Taki zuwa. Ummaan su ta takura min kowanne aiki zaayi se Dani idan aka gwada min sw tace su tafi su barmin, abincin ba irin Wanda na Saba ci bane, kullum Mai da yaji har ciki na ya fara ciwo. Tunda nazo sau daya akai shinkafa da Miya, shima seda kowa ya samu sannan ta difana min, na rasa me na tare Mata, me nayi Mata na kasa sani. Amma ko kallon da take min na tsana ne. Da yammacin kwana na takwas Ina zaune takure a tabarma, Mino na karatu ita Kuma Siyama na tilawar karatun islamiyya. Tunda ta fara Qadsami suratul mujadala take bata, na matso inda take nace
" Na iya, na Kara karanta Miki"
Ta harareni
" Nace Miki ban iya bane ko me, ke din me Kika iya?"
Na koma gefe naja bakina nayi shiru, Bata san nayi izu talatin ba a karatun da kullum Abbu ke fadan bana maida hankali. Sallamar Kawu Sa'idu tasa na kalla kofa, ya shigo se Naga dukkan su Basu tafi sun rungume shi kamar yadda na Saba ba, kowa yace Masa sannu da zuwa, se ni ce karshe nace Masa
" Kawu Ina wuni? Sannu da zuwa"
" Uwata, sannu ya bakunta?"
Na cije lebe bance Masa komai ba, ya wuce dakin shi, Abbu ya fado min idan yayi tafiya ya Dade haka idan ya dawo na dinga bin shi kenan se ya rokeni na jira shi a parlor zaiyi wanka tukun nake hakura. Muna Gama cin abinci, Yaya ya shigo ya zauna Yana ta min Hira, na saki jikina Ina bashi labarin random abubuwa, mostly magana daya biyu zance
" Allah sarki Abbu da Yana nan, da tuni kaza ya faru, Abbu yace kaza"
Haka hirar tamu ta kaaance se yace min yaji ance mun koam makaranta, nan na tuna ai tun last week an riga an koam, yace gobe na fadawa Kawu Sa'idu. Nayi tunanin tunda ya dawo zaa rage min aiki, se Naga akasin haka, musamman ranar kowa ya tafi makaranta se ni daya na rage Dan hakan ni nayi komai a gidan, har na daina jin zafin dundun saboda yadda ake sauke min shi a bayana akai akai. Na fito daga wanka na dakko skirt Zan saka kawai na rike shi na fara kuka, I remembered lokacin da mukaje wani top boutique a Abuja muka siya da Abbu, se na fasa sawa na dakko wasu kayan na saka nasa hijab kamar yadda nakeyi kullum tunda nazo, kayana ma sun taru bansan yadda zanyi dasu ba, Dan ni ban iya wanki ba. Jin muryar Kawu Sa'idu yasa nayi saurin fitowa, Yana tsaye suna magana da Ummaan su, na gaishe shi na Kara gaishe ta, ignoring harar da take banka min.
" Kawu dama an koma makaranta tun last week"
Ya kalleni da kyau yace
" Daga yau duk abinda Zaki fada min ki fara fadawa Zinatu ita zata fada min"
Na gyada kaina, ya cigaba da fadin
" Makaranta Kuma Zan dawo dake nan Ringim tunda can Babu inda Zaki zauna"
Tamkar saukar aradu haka naji zancen makaranta, nayi sauri nace
" Kawu se na koma boarding..."
" Dallah wuce ki tafi marar kunya, Yana magana kema ki nayi"
Na juya jikina a mace na koma daki, na saki kuka gefen katifa, Ringim Zan dawo da makaranta. Na bude kayana na Ciro tab dita na kunna ta dama a boye nake amfani da ita na Kira Rooks, Babu jimawa yayi connecting, tana dauka ta fara complain ramar da nayi, ban Mata magana ba se kuka, tayi sauri ta koma dakinta tayi locking kofar ta ta fara tambayata abinda ya faru, na fada Mata tace yanzun zata fadawa Mummy, nayi saurin dakatar da ita nace
" Rooks please no! It's out little secret. Kinga abinda kike tunani zaman gidannan ya wuce haka, tun yanzun idan na fara Kai Kara zaa samu matsala, Babu komai ko Ina makaranta ce zanyi karatu, kawai na fada Miki ne saboda naji dadi. Promise me Babu Wanda zai sani?"
Haka mukai wannan alkawarin Ina jin motsi na kashe na share hawayena na boye tab din. Na leko naji tana cemin zata je makwabta na hura wuta, cikin kudin na cira nayi sauri naje na siyo kifi, shi ne karon farko Dana fita, wani irin nishadi naji da yancin wucin gadi, kamar tantabara haka naji ni Dana fita, it's been a while! shima ba sanin gurin nayi ba, Mino naji tana zancen kifin na rike a raina, Kuma ban Sha wahala ba. Da na dawo kamar mayya ko mage haka na dinga ci sannan na wullar da takardar na wanke hannuna nayi brush, Ina hada itace ta dawo ta dinga fada banyi abinda tace ba, nidai nawa shiru ne Amma shima Bata Mata Rai yake!
Afiyya is not free, pay 300 through 3091721807, Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria. Send evidence through 09063467258
Shatttzzzx