UWARGIDAN BAHAUSHEXL (40)
✍️ Ayshatuuu 💙
Bayan na kashe wayar na aje a gefena, se naji hawaye ya fara dripping mini kan farar fuskata, mutuwa me tonon asiri, na tuna ni na Kira Usman nace Yana Sona ko ya daina? Duk shunning dinsa da nayi, duk kin amincewa dashi da nayi, duk ikirarin da nayi bazan aura me Mata ba, bazan ma kula Wanda yake da Mata ba, Amma Wai yau nice na kirashi da hannuna har nake kamar rokon shi ya aureni , na sauke duk wani pride Dina nace ya tura. Na kwanta a hankali Ina sakin kuka me karamin sauti, wani irin kunci nake ji cikin Raina, ji nake kamar na fito da zuciyata na dauraye ta a cikin ruwan sanyi ko zanji dadi. Na Dan Jima inayi sannan na Mike Ina ganin to meye tunda shi bai ma Gama saurarata ba ya kashe saboda tsabar farin cikin da yake ciki. Wannan yanayin da naji shi a ciki ya kwantar min da hankali, wasu lokutan na kanyi tunanin Anya idan ban aura Ismail ba , banyi failing ba kuwa? Anya ban rasa babban masoyi ba? Sede ko Babu komai Hanifa Yar uwata ce, auren Yaya Ismail kamar I'm ripping the family apart, tamkar na Kara hada wasu yakin ne, shi Kam Junaid bansan shi ba, ban taba ganin shi ba Amma kawai naji bazan iya ma magana dashi ba, Usman din ne dai kadai right choice Dina, kullum Ina adduar Allah ya zaba min mafi alkhairi Dan haka na dauka cewar auren Usman shi ne zabi mafi alkhairi.
Bai Kara Kirana ba har dare yayi na Gama Shirin baccina Amma haushin rashin Kiran na nan dankare a cikin Raina duk da kokarin kawadda abin nake a raina. Wayata na janyo na Shiga Wattpad a kokarin ganin bacci ya zo min sannan Kuma na fitar da rashin Kiran da baimin ba daga Raina. Amma ooops bana fahimtar komai hakan yasa na shiga kokarin yin kallo, Wanda ni kaina seda nayi dariya Dan ni bana kallo, it takes ages kafin ka ganni Wai Ina kallo, so film ne Rayha ta tura min ban masan wanne kasar bane nadai karba Amma har yau na gagara Gama single episode. Na aje wayar tareda juyawa na kulle idanuna se naji vib dinta, da sauri na juyo and I found him calling, murmushi na saki w hankali, se Kuma na Bata Rai lokacin da nake Kara wayar a kunnena
" I'm sorry ban Kira ki ba se yanzun, I was very busy Amma kinsan ko sau daya Baki taba barin Raina ba, in fact tun ranar Dana ganki wajen quiz dinnan zuciyata se yau taji sanyi"
Se nayi murmushi Wanda nasan yaji saboda sautin da ya fita,
" Dariya na baki ko? You've no idea yadda kikai torturing dina. Duk haduwar mu se kice Wai ke Baki yadda ba saboda wani so called reason dinki"
Na Dan harara wayar kace da gaske zaiga hararar, Nima maganganun da yake se Suka saka ni cikin nishadi.
" So called reason? Haka kake gani"..
Yayi Yar dariya yace
" So tell me what happened you decided to just give me a chance out of nowhere"
Na danyi Shiru shima se yayi shiru alamar Yana saurara ta, nasan Zan Yi hurting dinsa idan nace saboda Ina tsoron auren wasu, Dan haka nace
" Kawai ji nayi na gwada ka"
" Amma kinsan inada Mata ko? Kin hakura kenan"
Na danyi Murmushin takaici nace
" Ko daya, akwai lokutan da kake hakura da wants dinka saboda circumstances. Abu daya Zan fada maka Kuma Zan cigaba da maimaita maka, I'm peaceful person bana son tashin hankali sede cikin zuciyata na yiwa kishiya babban tanadi, inada kullinta a raina"
Se naji alamar canjawar yanayin shi daga tone din muryar shi
" Why did you have so much hatred akan kishiya? Is not good kwata kwata"
Na danyi dariya nace
" Ba zaka gane ba, Ina fata zaka fahimta a hankali and mind you bawai tsanar ta nayi ba kawai dai I need peace"