XV

1K 172 4
                                    


UWARGIDAN BAHAUSHE

XV

✍️ Ayshatuuu 💚

Muka jera muka nufi kofar da zata fitar damu daga sashen Gwoggo, duk yawancin aunties dinmu ko kuma Wanda Suka girme ni se na gaishe su, hannun shi yasa riko hannuna, nayi saurin kwacewa Ina zumbura baki nace

" Ni dai karka Kara taba ni"

Se yayi murmushi yace

" To ki daina gaida mutane, just focus muje gurin Ammin"

Bance Masa komai ba na hango, Yaya Nasir Yana tahowa, a cikin raina na fara adduar Allah yasa ya tsayar dashi na samu na gudu, aikuwa Allah ya karba adduata, Yana zuwa ya Mika masa hannu yace

" Man kwana da yawa"

Na gaida Yaya Nasir Yana murmushi yace

" Grandma kece Kika girma haka? Mashaaa Allah kin Zama Yan Mata"

Nayi murmushi Ina rufe fuskata saboda kunyar kallon da yake min, ganin hakan Ismail ya gyara murya yace

" Dude lower your gaze!"

Yaya Nasir ya kalleni sannan ya kalle shi yace

" Grandma should I borrow him for an hour? Na Jima ban ganshi ba"

Na gyada Kai na Ina murmushi, baban shi cousins suke da Baba, ya Jima baya Nigeria Dan ni kaina bansan yaushe ya dawo ba. Na juya Zan bar gurin naji muryar Yaya Ismail yace

" Sofiyya!"

Na juyo se yace

"Kar kiyi nisa"

Na gyada kaina na juya na tafi, ban Kai ga fita daga gidan ba muka hadu da Ammi da Yan uwanta da Suka zo daga Dan ladin gumel. Na gaishe su Ina tambayar su Baba da  Alhaji, suka amsa ni sannan Suka shiga ciki ni Kuma na nufi wajen kallon Hawa, gurin a cike yake dam da mutane daga garuruwa daban daban, Gumel is famous a wañnan aladar tasu.

A bangaren su Yaya Nasir,wani secluded spot suka samu suka zauna, Nasir yace

" Dude baka da kirki baka Neman mutane"

Ismail yayi dariya yace

" Dukkan mu zaka ce, Kai da zaka tafi Babu sallama shiyasa na yada Kai"

Suka Dan taba Hira, Nasir yace

" So Sofy fa?"

Ya Harare shi yace

" Ina sonta, Zan aureta!"

Nasir ya gyada Kai yace

" I'm happy! Amma kana ganin Ummaah zata yadda kasan basa shiri da Ammin ta"

Se ya dage kafadar shi irin ko a jikin shi yace

"Matsalar su ce wannan! Ni Bai dameni ba. What I know Ina son Sofy Zan Kuma sure ta"

Nasir yace

" Kabi a hankali dai, baa zuwa gurin mace da girman Kai"

Se yayi dariya kadan yace

" Ka dameni!"

Bamu Kara haduwa dashi ba Dan daga nan se na koma gida, ni kadai nayi zamana Ina karanta PQ na waec, nayi nisa sosae dan tunda na shiga SS2 nake Abu daya. Saboda duk hankalina ya koma kan final qualifying exam din. Se bayan Isha sannan Ammi suka dawo, Ina zaune kan sofa na baje da scientific calculator hannuna, naji sallamar su, na amsa Suka shigo Ammi ta rike baki cikeda mamaki tace

" Dama kina nan? Munata nemanki"

Nayi murmushi nace

" Tun dazun na dawo, gajiya nayi"

UWARGIDAN BAHAUSHEOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz