XXXVII

1K 202 13
                                    

UWARGIDAN BAHAUSHE

XXXVII (37)

✍️ Ayshatuuu🤎

Baka gane rayuwar is too short se wani bangare na jikin ka ya rabu da kai, bayan komai ya lafa se Naga dukka rayuwar is just an empty shell. Fada, masifa da tashin hankali duk na menene? Gaba daya rayuwar idan ka dunkule ta is too short wallahi.

Motar da ta buga tamu da muke ciki, irin Wanda suke hording kayan abinci ne, sun taho custom Kuma sun biyo su, suna neman tsira Dan haka kowacce mota ce a gabansu zasu iya shigar mata Dan su tsira, tana tahowa mu Kuma zamu wuce ta buga mu tareda hada mu da wata motar, Bayan furta masa wannan "Gefenka" nasan na runtse idanuna daga wannan ban Kara bude shi ba se a gadon asibiti, ko kuma nace a kwance a kasa Shima bawai na dawo consciousness Dina bane duka na dai ji hayaniya da koke koke gefena, ban Kara Kuma gane komai ba na Kara dozing a gurin. Lokacin Dana Kara dawowa hayyacina I was fully aware of inda nake, me ya faru dani da Kuma su waye a gefena. Ko Ina na jikina ciwo yake haka yayi min nauyi tamkar an daura min Abu a kirjina. Na bude idanuna Amma hasken da ya nemi lalata min pupils dina yasa cikin sauri na mayar na kulle idon, se Kuma a hankali na Shiga bude idon nawa, har nayi adjusting da hasken dakin, hannuna na hagu na daga Dan taba kaina da nake jin tamkar an daura min Abu me nauyi Amma se hakan ya gagara, Shima hannun yayi nauyi se na Kai idanuna kan shi, take na gane na karye ne saboda yadda akai casting hannun. Na runtse idanuna sannan na fara kokarin tashi, cikin saa na tashi na zauna Ina bin dakin da kallo, ni kadai ce a ciki Babu kowa se can gefe na hanga Gwoggo akan sallayya tana Jan casbaha hannunta. Na bude baki nace

" Gwoggo"

Amma ko ni kaina banji abinda na fada ba balle ita, se kawai na sakko daga kan gadon na nufeta, sede duk jikina ciwo yakeake min,na karasa gefenta na kwanta a kafadar ta, cikin hanzari ta dubeni tareda rungume ni a jikinta, fuskar ta na fitar da tsananin annuri na farin ciki, Nima nayi Mata murmushi se Kuma naga ta rike hannuna me lafiya tana sakin kuka me ban tausayi, a tuanina duk tausayin na ne.

Ammi ta shigo bayanta Baba suna rike da carton a hannun su, Ammi na ganina a tsaye ta karaso gurina ta rungume ni, tana kuka a hankali, Nima se na fara Taya ta, Baba ya karaso Yana tambayar Gwoggo yaushe na tashi, tace Masa ban Jima ba se ya juya Dan ya sanar dasu na tashi, suka karaso in a team, har lokacin Ammi na gefena tana kuka, Wanda yasa na fara jin kamar akwai wani Abin dake faruwa, idan Dan nayi accident ne to ai yanzun na tashi. Suka zo se Baba ya fita da ita Gwoggo tabi bayansu, Dr ya tambayeni ko Ina jin ciwo na Masa bayanin jikina ne ke ciwo yace buguwa ce a hanakli zai daina, zasu sallameni se muna zuwa follow up tunda gyaran yayi kyau, Bayan 3 weeks se a cire. Na musu godiya da muryata da ta fara fita a hankali. Gwoggo tasa nayi wanka, Anty Safara'u ta hada kayanmu Amma har lokacin Banga Ammi ta Kara dawowa ba. Dukkansu sunyi jugum su day suke tare dani, seda na gyara jikina sannan muka fito Dan tafiya se lokacin kwakwalwa ta ta tuna min ai ni da Likita mukai accident din, shi Yana Ina, tsayawa nayi cak Ina duban Baba dake rike da hannuna na dama nace cikin dasashiyyar murya

" Baba Likita fa?"

Yayi min shiru kamar Bai jini ba se nayi tunanin Bai ji din bane da gaske, Amma hannunsa dake cikin nawa se naji sunyi gumi sosae har seda na kalla fuskar shi, naga gaba daya ya fita hayyacin shi, fuskar shi tayi zuru zuru. A take naji gabana ya fadi. Ban Kara magana ba har muka dauka hanya seda mukaje Dayi sannan na fahimci Muna katsina, tun da muka bar Dayi nake jin wata faduwar gaba na riskata, Ammi dake gaba kusa da Baba lokaci zuwa lokaci se naga ta share hawayenta, haka Gwoggo ma se ya zamana Anty Safara'u da Baba ne kadai Wanda Basu kuka, itama Anty Safara'u rungumeni tayi jikinta nayi lamo. Daf da zamu bar funtua na kasa hakuri na dubi Anty nace

" Ummiey Ina Likita yake, tare dashi mukai accident din ko baa fada muku ba"

Ai Ammi na jin abinda na fada ta Kara fashewa da kuka, haka Gwoggo ma duk se naji hankalina ya tashi, na dubi Anty Safara'u idanunta sun kawo kwalla nace

" Ummiey ki fada min me ya same shi? Shima karyewa yayi?"

Ta rungume ni a jikinta tana shesheka, har Raina ban kawo zai mutu ba, a kwana kusa ban taba kawo Masa mutuwa ba Ashe shi his days were only a mere count down, Ashe a karar kwana muke. Baba ne ya fada min daf da min shiga maska, a cewar shi gwara na sani ba se anje can ba. Yana fada min naji gaba daya hawayen idanuna sun kafe, na kwantar da kaina a jikin kujerar motar, tareda runtse idanuna a hankali Ina jin wani Abu na taso min tundaga cikina har zuwa makogaro na, duk wasu tunani were blocked, na kasa fahimtar abinda kaina ke ciki. Ammi ta dubi Baba a tsiarce tana fadin

" Baban Sofy kaga Bata kuka, Gwoggo kina kallonta Taki kuka"

Na bude idanuna nace

" Gwoggo Wasa Baba yake ko, Bai mutu ba ko? Ina laifin ace Shima ya karye kamar yadda nayi. How am I supposed to believe cewar Likita ya rasu"

Kowa yaji abinda na fada yasan hankalina ya fara gushewa, tundaga wannan maganar da nayi ban Kara cewa uffan ba Kuma na kasa kukan sede zuciyata kamar ana soya ta haka nake ji, tunda muka shiga nake bin kowa da idanu, Ammi ta rungume ni, ganina da plastered hand yasa suka San ni ce wadda mukai accident tare se kuka ya dawo sabo, na hango Yan uwana kacakaca a gidan saboda umarnin Gwoggo ne kowa yaje. Dakin mahaifiyar shi aka kaini, tunda na shiga gaba daya fuskokin dake ciki tamkar an cire fuskar Likita an sassaka musu a tasu, se naji labarin mutuwar shi ya dawo min, a hankali na shiga ciki, tunda taga Ammi a bayana ta saki kuka tana zaune can kuryar daki sanye da hijab. Hannunta ta Miko min tana fadin

" Alhamdulillah bamuyi gawa biyu ba, taho yata Babu rabon naga auren ku"

Na karasa inda take zaune tana rikon hannu na saki kuka kamar Zan fitar da idanuna saboda kuka, dukka 'Yan uwanshi suka dinga kuka. Na Jima Ina kuka a jikin matar har aka samu nayi shiru, anan gurin nayi sallah amma abinci duk yadda aka taru akan lallashina naki ci, da suka ishe ni se na rike hannun Mama, Maman Bature na dinga kuka se tace su barni kawai. Ban taba jin bakin ciki a iya rayuwata ba, ban taba jin zuciyata tayi kuncin da tayi ba. Da dare yayi duka aka kwanta, Mama ta matsa min akan lallae lallae naci abinci naki se Naga tana kuka kawai se na dauki cup din tea na kafa a bakina, daci naji Amma hakan na daure nasha. Can cikin dare Ina takure na lulluba da hijab din da sister din shi ta bani da zanyi sallah, tunda aka kwanta nake kwance Amma ko dison bacci Babu idanuna, maganganun mu da shi kanshi ke dawo min, na tuna Yara biyar da yace zamu Haifa, I remembered yadda yake planning rayuwa hundred years to come, shi kan shi Bai kawo wa Kansa mutuwa ba, mikewa nayi na fita daga dakin mutane nata bacci abinsu, se Naga basuda matsala kenan, can gefe na samu na rakube na dinga kuka inajin dama Ina da damar zabar rayuwa ko mutuwa Allah na tuba da Zan zaba gwara nabi Bature Nima. Dafa ni naji anyi da sauri na goge hawayena na dago idanuna, Rayha ce alama sun nuna daga toilet take, ta zauna gefena idanunta sunyi ja, tunda na dawo na ganta amma I wasn't in the mood muyi magana, duk yadda nake daukin ganinta, dawowar tata yazo min baa dadin Rai ba. Mun Jima da ita tana ta rarrashina sannan tasa nayi alwala nayi sallah amma Shima a sujaddar se na Jima Ina kuka, kafin safe na zabge ga jinya ga Kuma tashin hankali. Ashe kwana na biyu asibiti, bayan motar ta buge mu ya samu fractured rib Wanda ya Huda lungs dinsa, tun kafin akai mu asibiti ya rasu, nikam mild head injury ne saboda buguwa se karaya a hannu.  Nayi kuka nayi kukan rashin shi, na tuna dukkan wahala da sadaukar da yayi min, ya bar aikin shi Dan dakko ni ko kaini makaranta, Ashe our time is limited, na tuna fadan mu. Nayi kuka har idanuna seda suka fara ciwo, bana tunanin akwai ranar da Zan Kara irin wannan kukan a rayuwata.

Shatttzzzx

UWARGIDAN BAHAUSHEOù les histoires vivent. Découvrez maintenant