XXIX

997 190 10
                                    


UWARGIDAN BAHAUSHE

XXIX (29)

✍️ Ayshatuuu 🤎




Babu Wanda yasan abinda Anty jidda ke shiryawa cikin ranta, sede itama tana ganin lokaci ne da zata dauki fansar bauta da tayi shekara da shekaru tana yiwa Ummaah, ta bude wuta ta fara shirye shirye Babu Kama hannun yaro, kullum tana hanyar kasuwa ko kuma tace tayi order. A bangaren Ismail Ummaah ta tabbatar jikin shi yayi sauki sannan ta same shi da batun auren, yayi shiru yana kallonta kafin yace

" Ummaah kenan na hakura da Sofy?"

Ta girgiza Kai tace

" Ina son na maka aure kafin ita ta gama  makaranta, idan ta gama se ka aureta"

Se ya gyada kanshi saboda shi mutum ne me tsananin biyayya, suna Gama maganar ta Kira Anty jidda ta sanar Mata akwai progress, Dan haka Anty jidda tace wani satin zata shigo su Gama Shirin.


A hankali na fara karatu, bana bukatar wani yace min wai nayi karatu Dan hakan Bata baki ne, ko a fada ko baa fada ba ansan zanyi karatu, in fact se ma cemin ake in daure Ina hutawa. First two weeks ban Saba da kowa ba hatta room mates dina sede na gaishe su kawai na fita, Yar final year din ce ma Anty yusra ke komawa ta kaina, ita ce take Dan tambayata idan taga na Jima ban dawo ba, har ta karba contact dina. Tun ranar da na fara ganinta, she looks familiar, tana min Kama da wata Amma na kasa tuna a Ina ma nasan me Kama da fuskar ta,kawai zuciyata ta kwanta da ita, for unknown reason Ina sonta.

  A class dama kullum Ina gaba, zaiyi wahala a tsare front seat ban zo ba, tunda naje bana taba yin  girki ranar da nake da lecture, sede na siya kawai. So ranar Saturday ce da ya Kai wajen wata na guda kenan, na fita nayo cefane na zauna na gyara komai sannan naje inda ya kamata nayi girki na daura abinci, Ina zaune da wani novel hannuna har na Gama, na juye sannan na dawo daki na aje na koma nayi wanke wanke na dawo. Anty yusra da fitowar ta kenan a wanka tana zaune tana shafa Mai, se dayar Hussaina Hussy ita Kuma ta fita, dake mutum ce me kawayen so bata fiye Zama ba. bansan Ina taje ba. Abincin na zuba a Dan deep plate na kaiwa Anty yusra, ta kalleni sannan tayi murmushi tace

" A'a yau girki Kika Yi kenan?"

Nayi murmushi nace

" Na gaji da cin na waje"

Ta gyada Kai tareda cemin ai dama tana ganin kokarina, se Bata ci abincin ba wai ta koshi, ban damu ba na zauna na cinye abinci na sannan na dauka wayata na kunna data na fara chatting. Tunda Naga Rayha online se kawai na zauna muka ta fira har bansan lokaci ya tafi sosae ba. Na aje wayar kenan Sega Kiran Ismail ya shigo kamar bazan dauka ba, se Kuma na dauka, da wannan muryar tashi me sanyi yace min

" Darling ya kike?"

Nayi dariya kamar yadda nake Yi duk lokacin da ya kirani da wani sweet name, seda muka gaisa sannan yace

" Ummaah zatayi min aure.."

Cikin farin ciki nace

" Da gaske? Oh Allah ya Sanya alkhairi"

Ya Dan Bata Rai kafin yace

" To are you happy zanyi aure, kiranki nayi na baki hakuri don't feel humiliated kinji, Zan aureki inshallah kinji?"

Na girgiza Kai nace

" Ina maka fatan alkhairi,Amma ka manta aurena kawai. Focus on the marriage you're about to hold."

" Shikenan rabuwa zakiyi dani? Kenan?"

Bance Masa komai ba Amma naji tausayin shi sosae cikin Raina, ba Kuma hakan ke nufin Zan karbe shi ba, uwarshi na ganin tayi amfani da hakan wajen Bata min Rai a yadda Ismail ya fahimta kenan, Bai San koami na gaba ba. Ya Jima Yana ta yimin complain akan baisan motive din Ummaah ba, Bai San me yasa take son Masa aure ba. Nidai sede na bishi da cewar yayi addua kawai.

UWARGIDAN BAHAUSHEWhere stories live. Discover now