UWARGIDAN BAHAUSHEXXXV
✍️ Ayshatuuu 🤍
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Babu dadi da dadi haka abin yake, idan yau tayi maka rashin dadi shi kuwan wani dadi take Masa, bazaka Hana wani yayi farin ciki ba saboda Kai kana cikin kunci, wannan shi ne concept din rayuwa, ability mu fahimci hakan Shima tamkar saukakawa rayuwa ne. Jikin Anty Rumasa'u ya Kara tsananta Amma dukda haka tana nan kulle mental asylum din, idan jikin ya danyi sauki se a fito da ita cikin sauran patients din, idan abin ya Kara birkitowa Kuma se a maida ta seclusion kamar yadda suke Kiran gurin. Wannan yasa Ayaan ta dawo gurin Ammi gaba daya da Zama. Ko a hakan aka tsaya ya kamata Mata mu zauna muyi tunani, komai a rayuwar nan talala ake Mana, gashi dai Anty Rumasa'u na da Rai, Dan da take kulafaci Bata Haifa ba, mijin da Yar da Suka rage Mata sun koma hannun wadda tun farko ta so ganin ta rabata da nata yaran, gashi komai da take fada a Kai a karshe baa je ki Ina ba sun dawo hannunta.
Bayan anyi biki da wata daya Yaya Ismail yazo Zaria nasan ba Danni yazo ba specifically Amma Kuma ya karaso gurina, lokacin da yazo Ina cikin lecture din biochem, so seda ya jira ba fito sannan na sameshi a zaune cikin motar shi, ta bangaren shi na tsaya Ina Dan murmushi nace
" Ango, sannu da zuwa?"
Ya Harare ni, muryar shi a hankali yace
" Ki zagayo Mana"
Ya fada Yana bude min kofar gefen shi Babu musu na karasa na shiga ya rufe sannan ya tashi motar muka fita daga campus din Baki daya, ba dube shi nace
" Ina zamu je"
Ya girgiza Kai yace
" Yunwa nake ji, abinci Zaki rakani naci"
Se ban Kara magana ba har muka karasa wani classy eatery, muka Shiga aka kawo Masa menu ya zaba sannan ya maida idanun shi kaina, kallon shi nayi yadda yake kallona so intense, na Dan saki siririn tsaki nace
" Oh! Oh!! Kallon fa?"
Yayi murmushi yace
" I missed you"
Na dauke kaina tareda kokarin Ciro waya ta dake ringing daga pocket din rigar jikina. Ina fito da ita wata course mate Dita falmata tana Kirana, seda naga Kiran na tuna Ashe munyi dasu zamuyi brainstorming akan anatomy of apes, na dauka ko gaisawa bamuyi ba tace
" Sofy Gumel"
Kamar yadda suke Kirana dashi
" Nazo room dinku baki nan, karki manta fa"
Na sauke ajiyar zuciya nace
" Na Dan fita ne, Ina dawowa inshallah Zan Kira ki"
Mukai sallama na dubi Yaya Ismail dake cin abincin shi a nutse ba tare da ya kalleni ba nace
" Yaya Kai sauri I need to go back ana jirana"
Bai cemin komai ba na lura baya magana idan Yana cin abinci, seda ya gama ya nufi counter Babu jimawa ya nufo ni hannunshi rike da leda anyi packaging abincin, na dube shi muka fita seda ya tada motar sannan na shiga, ya fara driving sannan yace
" Baki tambayeni amarya ba, ko kishi kike?"
Nayi dariya Bayan na kalle shi nace
" Kishi fa? Ni zanyi kishin ka"
Se Naga ya Bata Rai saboda yadda nake dariya kamar I'm making fun of him
" Seriously kayi loosing duk wasu chances na aurena Bayan ka aura Hanifa, so ina son kayi hakuri ka manta munyi wani relationship.."
Se ya kats ni da fadin
" Relationship? It was just a sided feeling, ni kadai nake sonki ai."
Na gyada kaina nace
" Dan Allah kayi focussing akan aurenka ka manta Dani,kayi hakuri it's hard Amma just give it a try ka tuna nace maka bazan aureka ba nasan wannan zai baka karfin gwaiwar embracing matar ka"
Ya gyada Kai Yana murmushi yace
" I never thought Zan karba Hanifa, bayan ta tare na fahimci da gaske Sona take Kuma kokarin kyautata min take, se Naga gwara na barki haka na karba abinda Allah ya bani"
Nayi Murmushin Jim dadi nace
" Allah ya zaba mafi alkhairi"
Har muka karasa school hirar gidan shi kawai uake min, Hanifa tayi kaza Hanifa tace kaza, hakan ya tabbatar min zaman lafiya suke kenan baa nan gizo ke saka ba. Bamuyi da Likita zai zo gurina ba, Dan tunda na tashi ko waya bamuyi ba, Dan haka ban kawo a kaina zai zo din ba. Bayan ya dawo Dani makaranta mun Jima cikin motar muna Hira seda naga lokaci na tafiya Kuma a ranar zai koma Kano yasa mukai sallama Bayan ya bani abincin da yayi min takeaway, Ina zuro kafata idanuna ya sauka akan fuskar da bata taba zuwa gareni tana fushi ba, fuskar da kullum murmushi ne yalwatacce akanta mussaman idan Ina gurin. Yana tsaye sanye da kayan kullum wato kaftan, shidai nan duniya Yana son kaftan Kuma shadda precisely, yauma yayi kyau cikin wata shadda coffee, kanshi sanye da hula da akai Mata dinki da milk din zare yafi yawa, idanun shi da glasses sede fuskar Babu annuri abinka da fari fushin ko kadan Bai boyi ba, wayata na duba inajin yadda gabana yake faduwa, a wayata calls dinsa har uku da ban dauka ba, na dake na juya nayiwa Yaya Ismail bye bye sannan ya tafi ba karasa inda Bature ke tsaye nasan ran shi yau ya Gama baci, Amma dake ni ce Ina karasawa inda yake tsaye nayi Masa murmushi nace
" Baka cemin zaka zo ba"
Ya kalleni yadda idanun shi ke hayaki seda na Dan janye nawa kadan
" Da ban fada Miki ba gashi nazo na sameki da wani"
Anzo gurin na fada Ina gyara tsayuwaa ta nace
" Haba Likita Yaya Ismail ne fa ba wani ba"
" Shi din! Idan kina son shi ne ki fada min, ni I can't take wannan haukan..."
" Hauka!"
Na maimaita Ina kallon shi, Shima kallona yake tunda banji tsoro ba Shima daidai yake dani, na nuna Masa kaina da middle finger nace
" Ni nake haukan?"
Ya kalleni straight idanuna yace
" Duk yadda Kika dauka hakan nake nufi, idan ni Zaki aura Babu yadda zaayi ki dinga biyewa mutanen da Basu San darajar ki ba, mutanen da suka wulakanta ki Suka cuzguna Miki, idan Zaki tsaya kaina to, idan Kuma bazaki tsaya ba se na kyaleki ki koma gurin shi"
Tabbas ya Gama sanin duk wani sirrin gidan mu, kafin meye Raina ya baci na juya a hankali na nufi hostel, Ina ayyana wannan shi ne karon farko da muka taba samin sabani dashi to Amma me yasa zai dauki zafi haka. Na wuce hostel na samu su falmata na jirana mukai karatu abinmu muka Gama. Da daddare nazo bacci ma duba wayata Babu call dinsa, Babu text haka ma a WhatsApp. Se nayi laakari da ni na Masa lafi ya kamata na fara Kira, Koda na Kira na farko Bai dauka ba na biyu Kuma se aka katse.
Wasawasa magana se ta Zama babba, har muka Shure sati daya Bai Kara nemana ba Nima Kuma na dage akan ai na kirashi yayi rejecting call din. Anan na tabbatar da cewar Ina son Bature da gaske,satin farko I was feeling very proud cewar dhi yayi min laifi, abin yakan dameni Amma nayi kokarin sharewa, a sati na biyu ne Kuma zuciyata ta fara gazawa na fara tunanin me yake nufi dani da zai shafe kwanaki Bai Kira ni ba, sede duk lokacin da nayi niyyar kiranshi pride da ego se su Hana ni, ranar da muka cika sati biyu na dawo a gajiye daki, ga Yunwa ga kuncin zuciyata ga naki fitowa na fadawa kowa halin da nake ciki dukda Widad na yawan tambaya ta abinda yake damunta sede nace babu, na kwanta akan gadon se naji vib din wayata da sauri na juya tunani na shi ne Amma se Naga Ammi haka muka danyi magana sama sama tana fada min naje na Kara duba Anty Rumasa'u nace Tom, tana kashe wayar se na saki kukan da nake ta rikewa, na janyo wayar Ina Kara jin audio notes din da mukai exchanging ta WhatsApp da Kuma daddar hirar mu, I felt heartbroken! Nayi kuka ranar har fuskata ta kumbura, Bayan na Gama na wanke fuskata na kwanta tareda wiping duka chat din mu na goge contact din shi daga wayata! Tirkashi fadan masoya ai hutu ne!
Shatttzzzx